Peter Obi Ya Shirya Share Hawayen 'Yan Arewa, Ya Gano Hanyar Magance Matsalar Yankin
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, ya yi magana kan irin damarmakin da jihar Kamo take da su a fannin masana'antu
- Peter Obi ya kuma yi magana kan hanyar da za a bi wajen sake farfado da tattalin arzikin yankin Arewacin Najeriya
- Tsohon gwamnan ya yi kira ga gwamnati ta ƙarfafa ƙanana da matsakaitan sana’o’i ta hanyar samar musu da yanayin da zai ba su damar bunƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya ce farfaɗo da masana’antun Kano da suka durƙushe na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin tattalin arzikin Arewacin Najeriya.
Obi ya bayyana Kano a matsayin ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci da masana’antu a ƙasar, yana mai cewa sake buɗe masana’antun da suka daina aiki zai taimaka wajen samar da ayyukan yi.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamban 2026 a Kano, yayin bikin yaye ɗalibai karo na biyar na jami’ar Skyline University Nigeria, cewar rahoton jaridar The Punch.
A wajen taron, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya nuna damuwa kan yadda ɓangaren masana’antu a Kano ya samu koma baya, inda ya yi kira da a ɗauki matakan gaggawa domin farfaɗo da shi.
Kano ta taɓa zama babbar cibiyar masana’antu
Obi ya ce Kano ta daɗe tana taka muhimmiyar rawa a harkokin kasuwanci, cinikayya da samar da kayayyaki a Najeriya.
Sai dai ya nuna takaicinsa kan yadda masana’antu da dama da suka kasance ginshiƙin ci gaban tattalin arzikin jihar a baya suka daina aiki.
A kalamansa, ya ce:
“Yayin da nake zuwa Kano da safiyar yau, na haɗu da mutane da dama, kuma na gaya musu cewa Kano na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a Najeriya.
“Wannan birni yana wakiltar ƙarfin ƙasar nan a fannin cinikayya, kasuwanci da masana’antu. A da, Kano ta kasance babbar cibiyar masana’antu, inda masana’antu da dama ke gudanar da aiki. Amma a yau, yawancinsu sun daina aiki.
“Dole ne mu sake farfaɗo da su, mu dawo da harkokin samar da kayayyaki da kuma samar da ayyukan yi ga al’ummarmu.”
Obi ya yi misali da ƙasar Vietnam
Tsohon gwamnan ya ce sake buɗe masana’antun da suka durƙushe da ƙarfafa harkokin sarrafa kayayyaki zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, rage talauci da inganta tattalin arzikin ƙasa.
Ya yi amfani da ƙasar Vietnam a matsayin misali, inda ya bayyana cewa ƙasar ta samu gagarumin ci gaba ta hanyar bunƙasa masana’antu.
Obi ya ce Najeriya na buƙatar ƙara ƙarfin samar da kayayyaki a cikin gida, maimakon dogaro da fitar da albarkatun ƙasa zuwa ƙasashen waje.
“Ƙasashe irin su Vietnam sun samu gagarumin ci gaba ta hanyar masana’antu, inda suke samun kuɗaɗe masu yawa daga kayayyakin da suka sarrafa fiye da abin da Najeriya ke samu.” In ji shi.
Ya yi kira ga gwamnati kan ƙananan sana’o’i
Obi ya kuma jaddada muhimmancin ƙananan da matsakaitan sana’o’i wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
Ya bukaci gwamnati ta samar da yanayin da zai bai wa ’yan kasuwa damar faɗaɗa harkokinsu, bunƙasa sana’o’insu da ɗaukar ƙarin ma’aikata.
Obi ya yi nuni da ƙasar Indonesia, inda ya ce ƙananan da matsakaitan sana’o’i na samar da kaso mai yawa na ayyukan yi.
A cewarsa, Najeriya na buƙatar samar da irin wannan yanayi domin ƙananan sana’o’i su bunƙasa, su faɗaɗa ayyukansu, su kuma taimaka wajen rage rashin aikin yi.

Source: Facebook
Kwankwaso ya yabi Peter Obi
A wani labarin kuma, kun ji cewa madugun Kwankwasiyya sanata Rabiu Kwankwaso, ya yi magana kan halin Peter Obi yayin da ake tunkarar zaben 2027.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar NDC, a matsayin mutum mai gaskiya da ba ya karɓar cin hanci.
Asali: Legit.ng


