Sheikh Jalo Jalingo Ya Gamu da Raddin Almajirin Albani kan Sukar Sarkin Katsina
- Sheikh Dawud Az-Zahiri ya kare Sarkin Katsina daga sukar da ya samu wajen shugaban majalisar malaman kungiyar Izala
- Da Sarki Abdulmumin Kabir Usman ya yi kira ga APC su gyara matslolin da ake samu, Ibrahim Jalo Jalingo ya dura kan shi
- Malamin addinin ya ci gyaran Sheikh Jalingo, ya ce abin da Mai martaba Abdulmumin Kabir Usman ya fada ba tawaye ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Sheikh Dawud Az-Zahiri ya maida wa Ibrahim Jalo Jalingo martani a dangane da matsayarsa a kan wasu maganganun Sarkin Katsina.
Da aka kai masa ziyara, Abdulmumin Kabir Usman ya yi kira ga shugabannin APC da su yi gyara a tafiyarsu, Jalo Jalingo yana ganin hakan ba daidai ba ne.

Source: Facebook
A wani karatu da muka samu a shafin Annasiha a Facebook, an ji Dawud Az-Zahiri yana cewa babu wani kuskure a cikin kalaman Mai martaba.
Malamin yana ganin Sheikh Jalo Jalingo ya yi kuskure da ya jefi Sarki Abdulmumin Kabir Usman da neman yin fito-na-fito da masu mulkin Najeriya.
Dawud Az-Zahiri ya soki Gwamnatin Bola Tinubu
Sheikh Dawud Az-Zahiri ya ce fada wa shugabannin damukaradiyya magana irin haka ba laifi ba ne, asali ma yana ganin tsarin mulkin bai toshe kofa ba.
Da yake karatun hadisi a littafin Sahih Muslim a Zariya, an ji Az-Zahiri ya yi tsokaci game da mulkin Bola Tinubu, yana kuka da wahalar da jama’a suke sha.
Babban malamin ya nakalto maganar Olusegun Obasanjo da ya zargi gwamnatin Tinubu da kara jefa ‘yan Najeriya cikin talauci sakamakon tsare-tsarenta.
Ya ce:
An san gwamnatin nan ba ta taimaki mutanen kasar ba. Wadannan tsare-tsaren duk da yake yi, Obasanjo ne ya fito yana cewa tsare-tsaren Tinubu duk sun maida ‘yan Najeriya sun zama talakawa.
"Ji wata maganar banza da ake yi, wai abubuwan da aka yi a shekarun baya ne suka jefa mutane a wannan halin da ake ciki. Wani irin rainin hankali ne wannan malam? Meyasa a shekarun bayan ba a fada irin wannan matsalar ba?
Malamin ya kuma ce babu wata nasara da aka gani a sakamakon tsare-tsaren da Tinubu ya kawo illa nutsa wa cikin wahala da ake ta kara yi a halin yanzu.
Inda malamin ya ci gyaran Jalo Jalingo
“Amma wai Jalo Jalingo ya ce wannan khuruji ne
Ina maganar khuruji a nan, gwamnatin nan ta damukaradiyya ta kafirci ita za a yi wa khuruji? To ai khujurin ya zama dole ne a yi idan ma za a iya.”
- Sheikh Dawud Az-Zahiri
Haka zalika malamin na makarantar Darul Hadith Salafiyyah ya ce kalaman Sarkin Katsina ba su da bambanci da irin na shugabannin kungiyar Izala.
Lokacin da Abdulaziz Yari suka ziyarci manyan Izala a Abuja, an ji Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi makamancin wannan kira ga shugaban kamfen din.
Dawud Az-Zahiri ya cigaba:
“Kamata ya yi ka fara fada wa Bala Lau da Kabiru Gombe sun yi khuruji idan gaskiya ka ke yi domin su ma da Abdulaziz Yari ya je wurinsu, sun ce ba za su goyi baya ba – ga matsaloli a gyara. Irinsu ne fa Sarkin Katsina ya fada.”
Az-Zahiri ya yabi Jalingo duk da haka
Duk da ya yi masa raddi, malamin ya bayyana cewa yana matukar kaunar Sheikh Jalo Jalingo.
Az-Zahiri yake cewa yana son shugaban majalisar malamin Izalan ne saboda karatu da hidimarsa a addini, ya ce malaminsu, Auwal Albani yana yawan yabonsa.
“Kai, Allah ya ceto Jalo Jaligo.”
Ni ina son wannan mutumin ne malam saboda ilminsa da hidimominsa da na san ya yi wa addini. A bakin Malam Albani mu ke jin yabon da yake yi masa.
- In ji Dawud Az-Zahiri
A karshe shehin malamin ya zargi Dr. Jalingo da kokarin kare barnar da wannan gwamnati ta ke yi, ya ce ana neman a yi wa lamarin kwalliya alhali talakawa na wayyo.
Yake cewa duk da suna tare da malamin, wannan ba zai hana su fadi abin da suke ganin shi ne gaskiya ba.
Kiran Sarkin Katsina ga 'yan kwamitin zaben APC
An ji labari Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya gargadi tawagar yakin zaben Shugaba Bola Tinubu su fifita tsaro da tattalin arziki.

Kara karanta wannan
Da gaske shugaban INEC ya yi amfani da shafinsa na X wajen tallata Tinubu? Gaskiya ta bayyana
Mai martaban ya bayyana cewa matsalar tsaro ta hana manoma zuwa gonaki a ƙananan hukumomi 12 tare da rufe wasu makarantu a jihar Katsina.
Abdulmumin Kabir Usman ya kuma soki halin ’yan siyasar da ya jawo baraka musamman a yankin Arewa, wannan ya sa wasu talakawa sun yabe shi.
Asali: Legit.ng


