Bola Tinubu Ya Kara Jihohin da zai Je Kamfen Din 2027
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya faɗaɗa jadawalin yaƙin neman zaɓensa na zaɓen shugaban ƙasa na 2027 daga jihohi 12 zuwa 19
- Sabon jadawalin ya nuna cewa Tinubu zai halarci tarukan yaƙin neman zaɓe guda 20 na APC tsakanin 24 ga Oktoba, 2026 zuwa 13 ga Janairu, 2027
- Jihohin da aka ƙara sun haɗa da Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara, yayin da aka kuma saka Akwa Ibom, Jigawa da Kebbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙara yawan jihohin da zai ziyarta domin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027 daga 12 zuwa 19, tare da saka Babban Birnin Tarayya, Abuja, cikin jadawalin.
Sabon jadawalin ya nuna cewa Tinubu zai halarci tarukan yaƙin neman zaɓe guda 20 da jam’iyyar APC ta shirya a faɗin ƙasar tsakanin 24 ga Oktoba, 2026 da 13 ga Janairu, 2027.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa a ranar 14 ga Oktoba, lokacin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Tinubu ya bayyana cewa ba zai iya halartar dukkan tarukan yaƙin neman zaɓen da aka shirya ba.
Jihohin da aka ƙara a jadawalin
Sabon jadawalin ya ƙara jihohin Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara, tare da Akwa Ibom, Jigawa da Kebbi, waɗanda Tinubu ya riga ya kai ziyara domin yaƙin neman zaɓe.
Ya zuwa yanzu, shugaban ƙasar ya halarci tarukan yaƙin neman zaɓe a Uyo, jihar Akwa Ibom, ranar 6 ga Nuwamba; Fatakwal, jihar Rivers, ranar 7 ga Nuwamba; Dutse, jihar Jigawa, ranar 10 ga Nuwamba; da Birnin Kebbi, jihar Kebbi, ranar 17 ga Nuwamba.
Jihohin da Tinubu zai ziyarta a Disamba
Bisa sabon jadawalin, ana sa ran Tinubu zai kai ziyara Katsina ranar 2 ga Disamba, Kano ranar 17 ga Disamba, Jalingo a jihar Taraba ranar 19 ga Disamba, sannan Abuja ranar 21 ga Disamba.
Haka kuma, zai halarci tarukan yaƙin neman zaɓe a Gusau, jihar Zamfara, ranar 28 ga Disamba, da Owerri, jihar Imo, ranar 30 ga Disamba.
Jadawalin yaƙin neman zaɓe a 2027
Bayan shiga sabuwar shekara, Tinubu zai ci gaba da yaƙin neman zaɓensa a Yola, jihar Adamawa, ranar 4 ga Janairu, Sokoto ranar 5 ga Janairu, da Ilorin, jihar Kwara, ranar 8 ga Janairu.
Daga nan zai wuce Asaba, jihar Delta, ranar 11 ga Janairu, kafin ya kammala yaƙin neman zaɓensa da babban taro a Legas ranar 13 ga Janairu.
Sabon jadawalin ya kuma sauya wasu ranakun da aka tsara tun farko, inda aka ɗage taron yaƙin neman zaɓen Sokoto daga 5 ga Disamba zuwa 5 ga Janairu, yayin da aka sauya ranar kammala yaƙin neman zaɓen Legas daga 9 ga Janairu zuwa 13 ga Janairu.

Source: Twitter
Arewa maso Yamma ce kan gaba
Jadawalin ya nuna cewa yankin Arewa maso Yamma ne zai fi samun ziyara daga Tinubu, inda zai kai jihohi bakwai, wato Kaduna, Jigawa, Kebbi, Katsina, Kano, Zamfara da Sokoto.
Yankunan Arewa maso Gabas da Kudu maso Kudu kowannensu na da jihohi uku a jadawalin, yayin da Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas kowannensu ke da jihohi biyu.

Kara karanta wannan
Shugaban APC ya ware gwamnonin Arewa 7, ya ba su shawara kan goyon bayan Tinubu a 2027
An farmaki 'yan APC a Borno
A wani labarin, mun rahoto cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ko na ƙungiyar ISWAP ne sun kai hari kan taron yaƙin neman zaɓen APC a ƙaramar hukumar Kukawa da ke jihar Borno.
Rahotanni sun ce maharan sun harba bama-bamai guda uku kan ƙauyen, inda suka nufi tawagar Mohammed Monguno, shugaban masu tsawatarwa na Majalisar Dattawa ta 10.
Sai dai dakarun Operation Hadin Kai sun fatattaki maharan, lamarin da ya ba sanatan da tawagarsa damar tserewa ba tare da samun rauni ba.
Asali: Legit.ng

