Matsalar Aure: Abba Ya Tashi Tawaga zuwa Gidan Kwankwaso domin a Sasanta

Matsalar Aure: Abba Ya Tashi Tawaga zuwa Gidan Kwankwaso domin a Sasanta

  • Gwamnan jihar Kano ya kama hanyar shawo kan matar shi ta biyu da aka ce ta nemi a raba aurensu a gaban kotu
  • Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kafa tawaga ta musamman da za ta je gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a Abuja
  • Ana jita-jita cewa Zainab Musa Kwankwasso wanda diya ce wurin tsohon gwamnan jihar Kano ta gaji da zaman aure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Ana rade-radin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara kokarin shawo kan mai dakin shi da ake zargin ta bar gidan sa.

Hajiya Zainab Musa Kwankwaso ta yi kara a gaban kotu, tana neman alkali ya karbi sadakin da aka biya domin raba auren ta.

Kara karanta wannan

Yadda rikici ya kaure tsakanin na hannun daman Tinubu da gwamnan APC

Abba.
Abba Kabir Yusuf a masallaci da Abdullahi Ganduje wajen taro Hoto: @AsadMukty @AbbaM_Abiyos
Source: Twitter

Wani labari da muka samu daga gidan rediyon Express a shafin Facebook yau ya ce an fara ganin yadda za a shawo kan matsalar.

Mai girma Abba Kabir Yusuf zai ga yadda zai yi domin ceto aurensu da ya shekaru har 20 kuma ana cewa an samu ‘ya ‘ya shida.

Abba Kabir ya tura jama'a gidan Rabiu Kwankwaso

Idan labarin ya tabbata, Gwamnan jihar Kano ya zabi wasu manyan mutane su je gidan Rabiu Musa Kwankwaso a yi sulhu.

An ce tawagar da ta kunshi fitattun ‘yan siyasa, malaman Muuslunci tana karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ne.

A cikin ‘yan tawagar sulhun kawai dattawa da wasu manya da ake jin maganarsu a jihar Kano.

Abdullahi Ganduje zai jagoranci sasanta Abba da matarsa

Abdullahi Ganduje wanda aka fi sani da Khadimul Islam zai ja mutane zuwa gidan Rabiu Musa Kwankwaso da ke birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi karyar da ta ce an shirya kan kai wa Kwankwaso hari

Ana sa ran tsohon gwamnan zai magance sabanin da ya shiga tsakanin Zainab Musa Kwankwaso da Abba wanda yake kan mulki.

Rahoton da tashar rediyon ya fitar ya bayyana cewa wata majiya ta shaida tsohon shugaban na APC ne jagoran tafiyar bikon da za a yi.

Haka zalika an samu wannan labari daga shafin tashar Rahma a dandalin X ba tare da an yi wa jama'a wani cikakken bayani ba.

Majiyar da ta bukaci a sakaya sunanta, ba ta yi wani karin bayani ba, don haka ba ta iya bayyana sunayen sauran ‘yan cikin tawagar ba.

Wasu sun ce Zainab Musa Kwankwaso ta tashi a hannun tsohon gwamnan ne kuma shi ya aurar da ita ga Abba lokacin yana hadiminsa.

Kwankwaso suruki ne ga gwamnan Kano wato Abba Kabir Yusuf da kuma maitaimakinsa domin yana auren 'yaruwar Murtala Garo.

Abba.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf dauke da casbaha Hoto: @Arafatrogo
Source: Twitter

Matar Gwamnan Kano ta nemi saki a kotu

Ana da labari Zainab Musa Kwankwaso, matar Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ta biyu, ta shigar da karar neman kashe aurensu a Kotun Shari’a a Abuja.

Kara karanta wannan

Lamari ya yi tsanani har kotu tana yi wa ministan Tinubu barazana da dauri a kurkuku

Uwar yaran gwamnan ta bayyana cewa soyayya da kulawa sun kare a tsakaninsu bayan duk kokarin sasanta su ya ci tura, don haka take neman a raba su.

Kafin shigar da karar, Zainab ta bar gidan gwamnatin Kano zuwa gidan uba a wurinta, sannan ta wuce Abuja ba tare da rakiyar jami'an tsaron gidan gwamnati ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng