Tinubu: Nasir El Rufai Ya Daura Bidiyon Abin da Sarkin Katsina Ya Fada wa Abdulaziz Yari
- Sarkin Katsina bai jin dadin irin muguwar siyasar da ake yi yau da kuma halin da ake ciki a yankinsa na Arewa
- Abdulmumin Kabir Usman ya kalli idanun Sanata Abdulaziz Yari ya yi masa wa’azi da suka ziyarci fadar shi
- Mai martaban ya ce ya zama dole a fada wa ‘yan siyasa gaskiya domin Allah Madaukaki SWT zai tambaye su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Nasir El-Rufai yana tsare kusan tun farkon shekarar nan da ya mika kan shi ga hukuma ta bincike shi.
Har yanzu da aka soma yakin neman zabe, Nasir El-Rufai yana garkame saboda tsattsauran sharadin beli.

Source: Facebook
Masu tallar Bola Tinubu sun je Katsina
Duk da yana hannu, ya daura bidiyon wani jawabin Sarkin Katsina a shafukan tsohon gwamnan na sada zumunta.
Da tawagar yakin neman zaben Bola Ahmed Tinubu ta je Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ya yi maganganu.
Mai martaban ya koka game da yadda abubuwa su ke tafiya a karkashin gwamnatin APC, ya bukaci a gyara.
Abdulaziz Yari ya jagoranci ‘yan kwamitin kamfen APC kamar yadda ya saba domin neman albarkar Sarkin Katsina.
Abin da Sarkin Katsina ya fada wa 'yan APC
A bangaren bidiyon da El-Rufai ya daura a kan Facebook, an ji Abdulmumin Kabir Usman ya ce:
"...A amshe arzikin wane…a yi wa wane sharri? Ina amfanin duka wannan?
"Darekta janar kana ciki yanzu. Ba wai a nan Katsina ba, duka kasar. Kuma mu iyaye ne, dole mu gaya maka gaskiya.
"A fada duk inda za a fada, sai kun so mutum sannan ku ke fada masa gaskiya, sannan Allah zai so ku, ya yi tare da ku…
"Ko wane ne kai, idan da zai ka yi wulakanci ga mutum, sai ka ga abin da ba ka so. Siyasa ai ba hauka ba ce,.
- Sarki Abdulmumin Kabir Usman
Sarki ya bada shawarar a guji rabuwar kai
Sarkin ya ce dole ya fadi gaskiya, tuna wa ‘yan tawagar yakin neman zaben cewa Allah SWT zai tambaye su a kiyama.
Bayan haka, Abdulmumin Kabir Usman ya shawarci Yari da ‘yan tawagarsa su hada-kai, su guji rabuwar kai a tsakaninsu.
Ya ce:
“Sai bango ya tsage….yanzu ba kadangare yake shiga ba, rakumi yake shiga. Bangonmu ya tsage.
"Arewa maso yamma ina mu ke?"
Kiran ceto yankin Arewa maso yamma
Watakila kasancewar Yari daga Arewa maso yamma, shiyasa Mai martaban ya fada masu maganganun masu jan hankali.
Sarkin Katsina ya bada misali da yadda aka gagara noma a yankin sannan ana fama da rashin aikin yi bayan da can ana da kamfanoni
Yake cewa kamfanonin da aka sani a jihar Kaduna duk babu su a yau, amma kuma an yi gum kamar babu manya a yankin su na Arewa.
El-Rufai bai samu yada ya so a kotu ba
Rahoto ya ce wata Kotun tarayya ta amince da bukatar ICPC na nuna faifan CCTV a shari’ar N10bn da Nasir El-Rufai ya shigar.
Tsohon gwamnan ya nemi diyya saboda zargin hana shi ganawa da matarsa da ɗansa da yake tsare saboda zargin aikata laifuffuka.
Bayan lauyoyi sun buga a kotu, Alƙali Chigozie Onah ɗage sauraron ƙarar El-Rufai da hukumar ICPC zuwa 3 ga Nuwamba, 2026.
Asali: Legit.ng

