Sojojin Najeriya Sun Yi Bajinta, Sun Sha Yabo na Musamman daga Amurka
- Amurka ta yaba wa rundunar sojin Najeriya bisa nasarar ceto mutane 125 da aka yi garkuwa da su a yayin hare-hare
- Sojojin sun kashe ’yan ta’adda takwas, sun cafke mutum 10 da ake zargi da taimaka musu, tare da lalata sansanonin ’yan ta’adda
- Rundunar ta kuma kwato makamai, ta lalata bama-bamai, yayin da mayakan ta’addanci 12 da iyalansu suka miƙa wuya ga jami’an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja — Gwamnatin Amurka ta yaba wa rundunar sojin Najeriya bisa nasarar da ta samu na ceto mutane 125.
Sojojin sun kwato wasu da aka yi garkuwa da su, tare da lalata sansanonin ’yan ta’adda a wasu sassan ƙasar.

Source: Twitter
Hukumar kula da harkokin Afirka ta ma’aikatar harkokin wajen Amurka ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba.

Kara karanta wannan
Mazan fama: Amurka ta yabawa sojojin Najeriya bayan gudanar da wani gagarumin aiki
Amurka ta yaba wa sojojin Najeriya
Amurka ta kuma yaba wa sojojin bisa kwato makamai da kuma gano tare da lalata bama-bamai da aka binne domin cutar da jama’a.
A cikin sanarwar, hukumar ta ce:
“Amurka na yaba wa ayyukan sojojin Najeriya da aka gudanar a wannan wata, waɗanda suka kai ga ceto mutane 125 da aka yi garkuwa da su, da kuma lalata sansanonin ’yan ta’addan Islama, kwato makamai da kuma kawar da bama-bamai.”
Hukumar ta ƙara da cewa Amurka na goyon bayan duk wani ƙoƙari da gwamnatin Najeriya ke yi na dakile sace mutane da kuma hukunta waɗanda ke da hannu a aikata irin waɗannan laifuffuka.

Source: Twitter
Yadda sojoji suka ceto mutane 125
Yabon da Amurka ta yi wa sojojin ya biyo bayan wasu hare-haren da rundunar ta gudanar tsakanin ranar 6 zuwa 12 ga watan Nuwamban 2026.
A cewar hedikwatar tsaro ta ƙasa, yayin ayyukan, sojojin sun ceto mutane 125, sun kashe ’yan ta’adda takwas, tare da cafke mutum 10 da ake zargi da haɗin gwiwa da masu tayar da ƙayar baya da kuma samar musu da kayan aiki.
Haka kuma, mayakan ta’addanci 12 da wasu ’yan uwansu sun miƙa wuya ga jami’an tsaro.
Mafi yawan mutanen da aka ceto sun haɗa da matafiya 119 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar 6 ga watan Nuwamba a kan hanyar Dutsen Kura zuwa Bulazarma zuwa Kamuya, a yankin ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno.
Sojojin sun bi sawun maharan, lamarin da ya tilasta musu barin mutanen da suka yi garkuwa da su, cikin mutanen da aka ceto akwai maza 69, mata 35 da yara 15.
An ceto wasu mutane biyar a Zamfara
Baya ga ceto mutanen a Borno, sojojin sun kuma ceto wasu mutane biyar da aka yi garkuwa da su a wasu ayyukan daban-daban a jihar Zamfara.
A yayin ayyukan, rundunar ta kuma kwato makamai da alburusai, ta lalata sansanonin ’yan ta’adda tare da gano da kuma lalata bama-bamai da aka ƙera da kayan fashewa.
Yadda Amurka ke sa wa Najeriya ido
An ji cewa sojojin Najeriya na samun bayanan sirri da hotunan tauraron dan adam daga Amurka domin kai hare-hare kan shugabannin ’yan ta’adda.
Ministan Tsaro ya ce sojoji sun kashe wasu shugabannin ’yan bindiga da ’yan ta’adda a hare-hare da suka kai a yankunan Arewa.
Gwamnati na kuma amfani da bayanan sirri wajen karfafa tsaro gabanin zaben shugaban kasa na watan Janairun 2027.
Asali: Legit.ng

