Sanata Ndume Ya Fadi Dalilinsa na Nadamar Shiga Harkokin Siyasar Najeriya

Sanata Ndume Ya Fadi Dalilinsa na Nadamar Shiga Harkokin Siyasar Najeriya

  • Sanata Ali Ndume ya ce da ya san yadda siyasar Najeriya za ta kasance, da bai taɓa shiga cikinta ba
  • Ɗan majalisar ya amince cewa shi ma yana cikin waɗanda suka gaza wajen tafiyar da siyasar ƙasar
  • Ndume ya yi gargaɗin cewa rashin aikin yi da rashin haƙuri da juna na iya ƙara ruruta rikicin siyasa gabanin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja — Sanata Ali Ndume mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya bayyana nadamarsa kan shiga siyasar Najeriya.

Ndume ya bayyana cewa da ya san yadda tsarin siyasar zai kasance, da bai shiga cikinta ba.

Ndume ya yi nadamar shiga siyasa
Sanata Mohammed Ali Ndume daga jihar Borno. Hoto: Mohammed Ali Ndume.
Source: Facebook

Gargadin da Ndume ya yi a siyasa

Ndume, wanda ɗan jam’iyyar APC ne, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na ARISE NEWS ranar Laraba.

Kara karanta wannan

'Zan ba kowace mazaba N40m': Ɗan takarar shugaban ƙasa ya ɗauki alƙawari

Sanatan ya kuma yi gargaɗin cewa rashin haƙuri da juna a siyasa, rashin aikin yi da rashin hukunta masu laifi na iya kawo cikas ga sahihancin zaɓen 2027.

Da aka tambaye shi ko yana ɗora wa kansa laifin gazawar tsarin siyasar ƙasar a matsayinsa na ɗaya daga cikin ’yan siyasa, sai ya amsa da cewa:

“Eh. Ni ma ina cikin waɗanda suka gaza. Ba zan iya musanta hakan ba, da a ce na san cewa siyasar za ta koma haka, da ban shiga cikinta ba.”

Ndume ya damu da rikici a siyasa

Sanatan ya bayyana damuwarsa kan yadda ake samun hare-hare kan shugabannin siyasa da magoya bayansu gabanin zaɓen 2027.

Ndume, wanda ya mara wa kudirin Sanata Abdul Ningi baya na neman gudanar da bincike da gurfanar da waɗanda ke da hannu a tashin hankalin zaɓe, ya ce Majalisar Dattawa na damuwa kan rahotannin hare-hare da suka shafi ayarin motocin Shugaba Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a 2023, Peter Obi, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

"Akwai damuwa game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya gabanin zaben 2027"

Ya yi gargaɗin cewa idan hukumomi suka ƙi ɗaukar mataki kan lamarin tun kafin zaɓen 2027, tashin hankalin zai iya ƙara kamari.

Ya ce ya kamata a magance matsalar tun tana ƙarama kafin ta zama babbar matsala.

Sanatan ya kwatanta rikicin da wuta, yana mai cewa idan ta kama ta bazu, zai yi wuya a iya kashe ta.

Ndume ya yi gargadi kan siyasa
Sanata daga jihar Borno, Ali Ndume. Hoto: Mohammed Ali Ndume.
Source: Facebook

Ya nemi hukunta masu ɗaukar nauyin rikice-rikice

Ndume ya yi kira ga hukumomin tsaro da na shari’a da su gurfanar da mutanen da ke ɗaukar nauyin tashin hankalin siyasa, yana mai cewa bai kamata waɗanda ke ɗaukar nauyin kai hare-hare su kuɓuta daga hukunci ba.

Ya kuma ba da shawarar kafa kotuna na musamman domin sauraron shari’o’in tashin hankalin zaɓe, yana mai cewa jinkirin shari’a na raunana ƙoƙarin hukunta masu laifi.

Haka kuma, ya buƙaci a ɗauki mataki kan amfani da abubuwa masu haɗari kamar wuƙaƙe da sanduna yayin yaƙin neman zaɓe.

Dangane da rahoton harin da aka kai kan ayarin motocin Tinubu, Ndume ya yaba wa jami’an tsaro, amma ya ce bai kamata a kwatanta irin kariyar da shugaban ƙasa ke samu da matsalolin tsaron da talakawan Najeriya ke fuskanta ba.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Abin da ya fi burge Atiku idan aka taɓa Tinubu yayin amfen

Ndume ya musanta sasanta yan bindiga

An ji cewa Sanata Ali Ndume ya fusata bayan an danganta shi da shiga tsakani tare da karban kudin fansa domin bai wa yan ta'addan da su ka yi garkuwa da mutane.

Ya bayyana cewa abin da ya yi shi ne sanar da DSS, NSA da sauran hukumomin tsaro bayan samun rahoton sace mutanen Ngoshe.

Sanata Ali Ndume ya bukaci jami'an tsaro su gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da aka yi masa, domin a wanke sunansa daga zargin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.