APC Ta Sake Babban Rashi, Hatsari Ya Rutsa da Daraktan Kudi na Kamfen Dinta

APC Ta Sake Babban Rashi, Hatsari Ya Rutsa da Daraktan Kudi na Kamfen Dinta

  • Gwamnan Enugu, Peter Mbah, ya bayyana rasuwar fitaccen ɗan kasuwa, Cif Festus Oshaba-Onuh, a matsayin babban rashi ga jihar
  • Marigayin, wanda aka fi sani da Ferotex, ya rasu ne sakamakon mummunan hatsarin mota a kan hanyar Enugu zuwa Fatakwal
  • Oshaba-Onuh shi ne daraktan kuɗi na kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a Enugu kafin rasuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Enugu — Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya shiga jimami bayan rasuwar wani fitaccen ɗan kasuwa a fannin gine-gine, Chief Festus Oshaba-Onuh, wanda ya rasu sakamakon hatsarin mota.

Marigayin, wanda aka fi sani da Ferotex, ya gamu da ajalinsa ne a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kan babbar hanyar Enugu zuwa Fatakwal.

An yi rashin jigon APC a Enugu
Gwamna Peter Mbah da marigayi Festus Oshaba-Onuh. Hoto: @PNMbah.
Source: Twitter

An yi rashin jigon APC a Enugu

Gwamna Mbah ne ya sanar da rasuwar a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamba, ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan zargin rikici tsakanin Shugaba Tinubu da gwamna a Najeriya

Gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jihar Enugu, yana mai cewa marigayin mutum ne da ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jihar.

Gwamna ya yi alhinin rasuwar Oshaba-Onuh

Gwamna Mbah na jihar Enugu ya bayyana alhininsa bayan rashin jajirtaccen dan APC wanda ya ba da gudunmawa sosai a jihar.

A cikin saƙon da ya wallafa, Mbah ya ce:

"Babban rashi ne ga daukacin jihar, domin shi ɗa ne nagari wanda muke alfahari da shi matuƙa."

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai taimakon al'umma, kishin ƙasa da kuma goyon bayan manufofin gwamnatinsa na gina sabuwar Enugu mai wadata.

Gudunmawar marigayin ga harkokin kasuwanci da siyasa

Oshaba-Onuh ya kasance fitaccen mutum a masana'antar gine-gine ta Najeriya, inda ya yi fice wajen harkokin kasuwanci da ayyukan ci gaban al'umma.

Baya ga nasarorin da ya samu a harkokin kasuwanci, an san shi da sauƙin kai da kuma taimakon jama'a.

Kara karanta wannan

Yadda mai babur ya jawo hatsarin mota, ya rutsa da shugaban APC, daraktan kamfen

A lokacin rasuwarsa, yana riƙe da muƙamin daraktan kuɗi na kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a jihar Enugu.

Gwamna Mbah ya ce marigayin ya kasance mai cikakken goyon bayan shirye-shiryen gwamnatinsa na bunƙasa ababen more rayuwa, kuma ya gudanar da aikinsa cikin kwarewa.

Gwamnan ya miƙa ta'aziyya ga iyalansa

Gwamna Mbah ya miƙa ta'aziyyarsa a madadin gwamnatin Enugu da al'ummar jihar ga iyalan marigayin.

Haka kuma, ya jajanta wa al'ummar Enugu Ezike da ƙaramar hukumar Igboeze ta Arewa, inda marigayin ya fito.

Ya roƙi Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya kuma ba shi rahama da hutu na har abada.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.