Yadda Rikici Ya Kaure tsakanin na Hannun Daman Tinubu da Gwamnan APC

Yadda Rikici Ya Kaure tsakanin na Hannun Daman Tinubu da Gwamnan APC

  • Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari, ya bayyana yadda saɓanin siyasa tsakaninsa da Gwamna Dikko Umaru Radda ya fara
  • Masari ya zargi wasu makusantan gwamnan da haddasa rikicin siyasar, musamman kan lalata allunan tallata Shugaba Tinubu a jihar
  • Ya ce bai taɓa yin wa Radda komai ba sai alheri, kuma bai da hannu wajen cire ko sauya wasu muƙamai a gwamnatin jihar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin siyasa da sauran lamura, Ibrahim Kabir Masari, ya yi karin haske kan saɓanin siyasa da ake zargin ya shiga tsakaninsa da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda.

Masari ya yi wannan bayani ne a wata hira, inda ya musanta cewa akwai wata matsala tsakaninsa da gwamnan, duk da rahotannin da ke nuna cewa manyan jiga-jigan siyasar jihar sun samu saɓani.

Kara karanta wannan

"Alamu da lissafin siyasa sun nuna wanda zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027"

Ibrahim Kabir Masari da bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Ibrahim Masari. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Masari ya kare kan shi

A hira da BBC Hausa, Masari ya musanta zargin cewa yana amfani da kusancinsa da fadar shugaban ƙasa wajen tsoma baki a harkokin siyasar Katsina ko neman a cire wasu jami’an gwamnati.

Ya ce bai taɓa neman a cire wani minista ko a maye gurbinsa da wani ba, yana mai cewa zargin da ake yi masa ba adalci ba ne.

A kalamansa:

“Da farko, wannan ba gaskiya ba ne. Ban nemi a cire wani minista ko a maye gurbinsa da wani ba.
“Alhamdulillah, Allah shaida ne a kaina, haka nan Shugaban ƙasa. Ba adalci ba ne a zarge ni da alhakin cire mutum ɗaya da maye gurbinsa da wani.”

Da aka tambaye shi ko yana jin daɗin salon mulkin Gwamna Radda, Masari ya amince cewa jihar ta samu wasu sauye-sauye a ƙarƙashin gwamnatinsa.

Ya ce ko waɗanda ba sa son gwamnan sun san ya yi ayyuka masu kyau a Katsina, yana mai cewa bai taɓa yin nadamar goyon bayansa har ya zama gwamna ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi karyar da ta ce an shirya kan kai wa Kwankwaso hari

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rikicin ya zo ne a lokacin da wasu jami’an siyasa a gwamnatin Katsina suka fara ajiye muƙamansu.

Yadda rikicinsu ya fara

Masari ya ce rikicin ya fara ne lokacin da wasu mutane da ke aiki tare da gwamnan suka fara kafa allunan tallata hoton Radda ba tare da saka hoton Shugaba Tinubu ba.

Ya bayyana cewa shi da Minista Jabiru Tsauri da sauran waɗanda shugaban ƙasa ya naɗa sun haɗa kuɗaɗe domin samar da alluna da fastoci da ke ɗauke da hotunan manyan shugabannin siyasa.

A cewarsa, allunan sun ƙunshi hotunan Shugaba Tinubu, mataimakinsa, Gwamna Radda, tsofaffin gwamnoni Aminu Masari da Shehu Shema, da kuma Ibrahim Masari, Muttaka Rabe da Jabiru Tsauri.

Gwamna Dikko Umaru Radda
Gwamnan Katsina, Dikko Radda. Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Ya yi zargin cewa wasu jami’an tsaron gwamnan sun jagoranci ’yan daba wajen lalata allunan da aka kafa domin tallata shugaban ƙasa.

Radda ya karrama sarakuna

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya umarci a biya duk kuɗin da sarakunan gargajiya ke bin gwamnatin jihar ba tare da ƙarin jinkiri ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yaye jami’an tsaron daji 1008 a Katsina, ya fadi aikin da za su yi

Gwamnan ya buƙaci sarakunan da ke fuskantar matsalar jinkirin biyan haƙƙoƙinsu da su kai ƙorafinsu kai tsaye ofishinsa domin a ɗauki matakin da ya dace.

Radda ya kuma yi alƙawarin tallafa wa aikin gyaran wani masallaci da ba a kammala ginawa ba, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da sarakunan gargajiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng