Tsohon Hadimin Ganduje Ya Nuna yadda Sabanin Abba da Matarsa Ya Samo Asali
- Salihu Tanko Yakasai ya ce matsalolin auren Gwamnan Kano da Hajiya Zainab sun fara tsananta ne bayan rantsar da shi
- Ya soki yadda Abba Kabir Yusuf ya bayyana rabuwar aurensa a bainar jama'a, yana mai cewa bai girmama 'ya'yansu ba
- Da yake tir da abin da ya faru a gaban manya, ‘dan siyasar ya yi kira da a dawo da darajar iyali kuma a mutunta aure
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Salihu Tanko Yakasai ya tofa albarkacin bakinsa game da abin da ya faru tsakanin Hajiya Zainab Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano.
Malam Salihu Yakasai wanda ya yi takarar gwamna a jihar Kano a zaben 2023 ya yi tir da lamarin, yana cewa sam bai ji dadin halin da aka shiga ba.

Source: Twitter
dogon rubutun da ya yi a dandalin X a ranar Talata, Salihu Yakasai ya ce tun ba yau ba Gwamna Abba Kabir yake samun sabani da matarsa ta biyu.
Duk da ya ce ba zai shiga bayanin dalla-dallar abin da ya faru ba, ‘dan siyasar ya ce tun da aka rantsar da Abba aka fara samun matsala a gidansa.
Sabanin Abba Kabir da Zainab Kwankwaso ya dade
Yakasai wanda aka fi sani da Dawisu ya ce ba sai bayan rabuwar Abba Kabir da Rabiu Kwankwaso a siyasance ne matsalar gidan auren ta bijiro ba.
Yake cewa ba Kwankwaso ba ne ya sa ta rabu da gidan aurenta domin har akwai lokacin da shi tsohon gwamnan ya yi kokarin sasanta bangarorin.
A cewarsa, Mai girma gwamna ya yi alkawarin zai magance matsalolin, amma bai yi ba. A karshe dai lamarin ya kara kamari lokacin da ya fice daga NNPP.
Malam Yakasai ya ce sai da ta kai Zainab Kwankwaso tana neman yadda za ta bar gidan aurenta, amma Mai girma gwamna ya ki sakinta, ya yi rike ta.
Ko da ta tafi kotu neman a raba su, Yakasai ya ce ba daga cikin danginta aka samu labarin ba, don haka ya ce ba daidai ba ne a ce an fallasa gwamna.
Tsokacin Salihu Tanko Yakasai
'Dan siyasar ya rubuta:
"Akwai lokacin da tun kafin sabanin Kwankwaso da Abba, Kwankwaso da kansa ya shiga tsakani, inda ya kira Gwamna Abba domin sasanta su. Abba ya yi alkawarin zai magance matsalolin, amma maimakon haka, sai abubuwan suka kara lalacewa, musamman bayan sabanin siyasa da ya shiga tsakaninsu.
Hajiya Zainab ta kai wani mataki da take matukar son fita daga auren. Abba kuma ba ya son ya sake ta. Daga karshe, ta tafi Abuja domin neman raba auren ta hanyar kotu bisa tanade-tanaden Shari'ar Musulunci.
'Gwamna bai duba kimar yaran da aka haifa ba'
Tsohon hadimin na Abdullahi Ganduje ya ce babu abin da ya fi ba shi haushi kamar yadda gwamnan ya ki la’akari da tarin ‘ya ‘yan da suke tsakaninsu.
A rubutun na shi, ya ba bayyana cewa yaransu ba za su taba manta wa da cewa a mimbarin siyasa gwamna ya sanar da duniya ya rabu da mahaifiyarsu ba.

Kara karanta wannan
Kano ta ɗauki zafi, Gwamna Abba ya yi kalaman da ake zargin ya nuna ya saki matarsa
Ya ce ko da abin da ya fada ba gaskiya ba ne, duk da haka akwai takaici game da abin da ya faru.
Mu dauka ma cewa duk abin da na faɗa a sama ba gaskiya ba ne, kuma mu dora mata laifin lalacewar auren gaba daya. Shin bayyana rabuwar aurensa da mahaifiyar ’ya’yansa a bainar jama'a, a kan dandali, tare da yadda ya yi hakan har jama'a na ta tafi da murna, shi ne mafi dacewa ga uba nagari wajen tafiyar da irin wannan lamari mai matuƙar muhimmanci da sirrin iyali?
Haba, don Allah!
Haka kuma, abin da ya kara tayar da hankali shi ne yadda wannan lamari ya faru a gaban Mai Martaba Sarkin Kano da Kwamandan Hisbah
- Salihu Tanko Yakasai
Yakasai ya cigaba da yin Allah-wadai da yadda ba a samu wani da ya iya nusar da Mai girma gwamna ba.
"Amma babu wanda ya nuna alamun damuwa ko ya ga dacewar jan hankalin Gwamnan, ko tunasar da shi mutunci da kamun kai da ake buƙata daga wanda ke riƙe da irin wannan mukami.
"Da alama faɗin gaskiya ga masu mulki ya zama abin so ne kawai idan wanda ake magana a kansa shi ne Ganduje."
Ya kare da cewa al’umma ta shiga wani mummunan yanayi, yana mai kira da a mutunta sha’anin iyali.
Salihu Tanko Yakasai:
"Iyali ne tushen da al'umma ke samun nasara ko kuma ta gaza. Idan muka rasa martabar iyali, to mun rasa ginshiƙin da aka gina al'umma ta gari a kansa."
Abubuwa dangane da shari'ar auren Gwamnan Kano
Labarin nan ya yi bayani abubuwa game da shari'ar neman raba auren Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da matarsa Zainab Kwankwaso
Ya bayyana kotun da ke sauraron karar, tarihin dangin ma'auratan, alkalin shari'ar da lauyan da ke wakiltar Zainab, tare da bayanin wakilin gwamna.
An kuma bayyana cewa kotu ta dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga Disamba, 2026, yayin da ake samun rahotannin har saki ya auku tuni.
Asali: Legit.ng


