Tinubu Ya Kafa Tarihi a Najeriya, Ya Kafa Jami'a Irinta Ta Farko a Duniya

Tinubu Ya Kafa Tarihi a Najeriya, Ya Kafa Jami'a Irinta Ta Farko a Duniya

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa Jami’ar Hulɗa da Jama’a da Jagoranci ta farko a duniya domin horar da ƙwararru a fannin sadarwa da jagoranci
  • Tinubu ya bayyana cewa kafa jami’ar na daga cikin matakan da Najeriya ke ɗauka domin samar da ƙwararrun ma’aikata a fannin hulɗa da jama’a
  • Shugaban ya ce bai kamata a riƙa kallon Najeriya ta fuskar damfara ta intanet kawai ba, domin ƙasar ta fi abin da ake kira 419 girma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa jami’ar hulɗa da jama’a da jagoranci ta farko a duniya.

Tinubu ya amince da hakan ne domin inganta ilimi, bincike da horar da ƙwararru a fannin sadarwa.

Tinubu ya kafa jami'a ta farko a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taron majalisar zartarwa. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Tinubu ya amince da kafa sabuwar jami'a

Kara karanta wannan

An ba 'yar Amurka Dala miliyan 4.5 bayan ta yi hira da Shugaba Tinubu? Gaskiya ta bayyana

Tinubu ya bayyana hakan ne cikin jawabin da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya gabatar a madadinsa yayin taron ƙasa da ƙasa na 13 kan hulɗa da jama’a na duniya, cewar Vanguard.

Shugaban ya ce ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da Najeriya za ta samu daga karɓar baƙuncin taron shi ne kafa wata cibiya mai ɗorewa da za ta inganta harkar hulɗa da jama’a.

Ya ce:

“Dangane da haka, ina farin cikin sanar da amincewa da goyon bayana ga kafa Jami’ar Hulɗa da Jama’a da Jagoranci, wadda za ta kasance irin ta farko, domin bunƙasa ilimi na musamman, bincike, haɓaka ƙwarewa da horar da shugabanni a fannin hulɗa da jama’a, dabarun sadarwa da sauran fannoni masu alaƙa.”

Tinubu ya bayyana jami’ar a matsayin babban jari da za a zuba wajen bunƙasa ƙwarewar al’umma da makomar harkar sadarwa.

Ya ce jami’ar za ta samar da dama ga matasa da sauran masu sha’awar fannin domin zama ƙwararrun shugabannin sadarwa da za su iya fuskantar sauye-sauyen da ke faruwa a duniya.

Ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki su haɗa kai domin tabbatar da cewa jami’ar ta zama cibiyar ƙwarewa a duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gano dabarun 'yan kasuwa, za a kawo karshen kauce wa biyan haraji

Tinubu ya amince da kafa jami'ar hulda da jama'a
Bola Tinubu da Kashim Shettima da ya wakilce shi wurin amincewa da jami'ar hulda da jama'a a Abuja. Hoto: Khalid Ahmed/FMINO.
Source: Facebook

Tinubu ya magantu kan ƙalubalen fasahar zamani

Shugaban ya bayyana cewa Najeriya na godiya ga Ƙungiyar Hulɗa da Jama’a da Gudanar da Sadarwa ta Duniya da sauran ƙwararru bisa amincewa da aka yi wa ƙasar domin karɓar baƙuncin taron.

Da yake magana kan sauye-sauyen da ke faruwa a fannin sadarwa, shugaban ya ce fasahar zamani da basirar wucin gadi (AI) sun sauya yadda ake ƙirƙira, yaɗawa da kuma karɓar bayanai.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa waɗannan sauye-sauye sun haifar da wasu ƙalubale da suka haɗa da yaɗa labaran ƙarya, bayanan da aka ƙirƙira domin yaudarar jama'a, kalaman ƙiyayya da raguwar amincewar jama'a ga hukumomi.

Ya ce:

“A irin wannan yanayi, alhakin ƙwararrun hulɗa da jama’a da sadarwa ya wuce kula da martabar mutane da hukumomi kawai.”

Tinubu ya kara yawan jihohin da zai je

Mun ba ku labarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya faɗaɗa jadawalin yaƙin neman zaɓensa na zaɓen shugaban ƙasa na 2027 daga jihohi 12 zuwa 19.

Kara karanta wannan

Shettima ya sanar da shirin raba miliyoyin buhunan taki ga masu noman rani

Sabon jadawalin ya nuna cewa Tinubu zai halarci tarukan yaƙin neman zaɓe guda 20 na APC tsakanin 24 ga Oktoba, 2026 zuwa 13 ga Janairu, 2027.

Jihohin da aka ƙara sun haɗa da Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara, yayin da aka kuma saka Akwa Ibom, Jigawa da Kebbi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.