Da Gaske Shugaban INEC Ya Yi Amfani da Shafinsa na X wajen Tallata Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

Da Gaske Shugaban INEC Ya Yi Amfani da Shafinsa na X wajen Tallata Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

  • Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya musanta mallakar shafi a dandalin X da ake zargin ya yi amfani da shi wajen tallata Shugaba Bola Tinubu da APC
  • Ya ce an kai ƙarar lamarin ga DSS da ofishin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, kuma an samu rahoto daga wani bincike mai zaman kansa
  • Amupitan ya ce wasu zarge-zargen da aka yi masa a baya, ciki har da cewa ya kasance cikin tawagar lauyoyin Tinubu, ba gaskiya ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya musanta mallakar wani asusun sada zumunta na X da ake zargin an yi amfani da shi wajen tallata Shugaba Bola Tinubu da APC a babban zaɓen 2023.

Amupitan ya kuma bayyana cewa an kai batun ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ofishin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, sannan an samu rahoto daga wani bincike mai zaman kansa kan takaddamar.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC ya magantu kan karɓar muƙami bayan barin hukumar

Amupitan.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Punch ta ruwaito cewa ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron tattaunawa a Chatham House da ke Landan, wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar Kimpact Development Initiative.

Amupitan ya musanta amfani da shafin X

Da yake amsa tambaya kan ko da gake bincike mai zaman kansa ya tabbatar da cewa ba shi ne ke amfani da shafin ba, shugaban INEC ya ce an samu rahoto kan lamarin, kuma an kai batun ga DSS da Sufeto-Janar na ’Yan Sanda.

“Mun samu rahoto daga wani bincike mai zaman kansa, sannan an kai batun gaban DSS da kuma Sufeto-Janar na ’Yan Sanda,” in ji shi.

Ya dage cewa bai taɓa mallakar shafi a dandalin X ba, inda ya bayyana cewa ƙoƙarin da ya yi na tuntuɓar kamfanin X domin warware zargin bai yi nasara ba saboda shi ba mai amfani da dandalin ba ne.

“Ban taɓa mallakar shafin X ba. Na yi ƙoƙarin tuntuɓar X, amma ba zai yiwu ba idan ba ka da shafi a dandalin. Ina da adireshin imel na Yahoo, ina duba imel ɗina anma wannan asusun ba nawa ba ne. Kuma wannan shi ne gaskiya,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC ya tafi ƙasar waje, ya faɗa wa duniya matakin da za su ɗauka kan takarar Atiku a 2027

Amupitan ya tabo lokacin zargin

Amupitan ya ce takaddamar ta kunno kai ne a daidai lokacin da aka samu hukuncin kotu kan jam’iyyar ADC da kuma fassarar umarnin kotu na mayar da al’amura yadda suke kafin rikici (status quo ante bellum).

“Ku tuna da abin da ya faru a baya. Batun ya taso ne lokacin da kotu ta yanke hukunci cewa ADC na da matsala, da kuma batun ma’anar status quo ante bellum. Ba na son komawa kan wannan batu. Amma dai abin ya faru ne a kusan wannan lokacin,” in ji shi.

Ya nuna cewa lokacin da zargin ya fito na iya kasancewa wani ɓangare na ƙoƙarin ɓata masa suna da kuma raunana hukumar zaɓe.

Shugaban INEC ya kuma yi watsi da wasu zarge-zargen da aka taɓa yi masa a baya, ciki har da ikirarin cewa ya kasance cikin tawagar lauyoyin Tinubu da kuma cewa ya yi ƙarya kan tarihin karatunsa.

Kara karanta wannan

Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta

An tare motar shugaban INEC a Landan

Kun ji cewa masu zanga-zanga sun kewaye motar shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, iyayin ziyararsa a Landan ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026.

Mutanen, wadanda ake kyautata zaton yan Najeriya ne mazuana Birtaniya sun nuna bacin ransu kan wasu abubuwa da INEC ta yi, sun nemi Amupitan ya yi murabus.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262