Shugaban Jam’iyyar APC da Aka Yi Garkuwa da Shi a Kano Ya Tsira bayan Kwanaki 68

Shugaban Jam’iyyar APC da Aka Yi Garkuwa da Shi a Kano Ya Tsira bayan Kwanaki 68

  • Shugaban APC na karamar hukumar Rogo a Kano, Abdullahi Alasan Beli, ya samu 'yanci bayan kwanaki 68 a tsare
  • ‘Dan siyasar ya ce masu garkuwa da mutanen sun rika kai shi wurare daban-daban a jihohin Kaduna da Zamfara
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yaba wa 'yan sanda tare da bada umarnin a dauki nauyin jinyar Hon. Abdullahi Beli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Shugaban jam'iyyar APC na reshen karamar hukumar Rogo a jihar Kano, Hon. Abdullahi Alasan Beli ya kubuta daga hannun ‘yan bindiga.

Hon. Abdullahi Alasan Beli wanda aka fi sani da Abdullahi Fanka, ya samu 'yanci bayan shafe kwanaki 68 a hannun masu garkuwa da mutane.

Abba.
Gwamna da kwamishinan 'yan sandan Kano bayan ceto shugaban APC Hoto: Salisu Muhammad Kosawa
Source: Facebook

Sanarwar kubutar da shugaban APC a Rogo

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ce ta samu nasarar ceto shi daga hannun masu garkuwar kamar yadda Salisu Kosawa ya sanar a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Malamin da aka cire a limanci saboda goyon bayan Tinubu ya lashe amansa

Kosawa ya dauko bayanin ne daga ofishin Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gidan Kano.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa kwamishinan 'yan sanda, CP Adamu Bakori, da sauran jami'an rundunar bisa kokarin da suka yi.

Shugaban APC ya yi watanni 2 a hannun 'yan bindiga

Jami’an tsaro sun yi kokari wajen ganin an kuɓutar da shugaban jam'iyyar da aka sace kwanaki.

An bayyana cewa an sace Abdullahi Beli ne daga gidansa da ke garin Beli, a karamar hukumar Rogo tun a cikin a farkon watan Satumban 2026.

Lamarin ya jefa iyalansa, magoya bayan jam’iyyar APC, abokan siyasa da sauran al'ummar yankin cikin damuwa na tsawon fiye da watanni biyu.

Bayan samun 'yancinsa, Beli ya bayyana cewa masu garkuwar sun rika kai shi wurare daban-daban, ciki har da Danja, Ikara da Giwa a jihar Kaduna.

‘Dan siyasar ya ce daga bisani ‘yan bindigan da suka dauke shi, sun wuce da shi jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Abba ya shiga ya fita a canza kwamishina da wasu jami‘an ‘yan sanda kafin zabe a Kano

'Yan sandan Kano sun ceto shugaban jam'iyyar APC

An bayyana nasarar ceto shi ne lokacin da kwamishinan 'yan sanda, CP Adamu Bakori, ya kai wa Gwamna Abba Yusuf rahoto a gidan gwamnatin Kano.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce jami'an tsaro sun gudanar da aikin ne ta hanyar amfani da dabaru na musamman da suka kai ga kuɓutar da ‘dan siyasar.

Mai girma Abba Yusuf ya kuma yaba wa jami'an rundunar, musamman shugaban sashen yaki da garkuwa da mutane, CSP Aliyu Muhammad Auwal.

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce gwamnan ya kuma yaba wa CSP Ado Muhammad Audi da kakakin 'yan sandan Kano, CSP Abdullahi Kiyawa.

Umarnin da Gwamna Abba Kabir ya bada

Gwamnan ya umarci kwamishinan lafiya ya tabbatar an ba Abdullahi Beli cikakkiyar kulawa.

Akwai bukatar a nema masa taimakon kwararru wajen dawo da lafiyar kwakwalwarsa bayan halin da ya shiga a tsawon lokacin da ya yi a hannun miyagun.

Abba ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa da gaske ta ke yi wajen ganin ba jami'an tsaro gudumuwa domin su kare rayuka da dukiyoyin Kanawa.

Kara karanta wannan

“Ko zai shafi Tinubu a 2027?” Yadda al’ummar Legas suka tarbi Kwankwaso ya ja hankali

Dauke shugaban jam'iyyar APC a Kebbi

A kwanakin baya aka ji labari an sace tsohon shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Koko/Besse da ke jihar Kebbi tare da wani abokinsa.

An saki wani bidiyo a kafafen sadarwa inda mutanen biyun ke rokon a taimaka masu ganin cewa ba su da lafiya, lamarin da ya jefa al'umma cikin bacin rai.

Ganin wannan bidiyo ya kara tayar da hankali kan matsalar tsaro musamman da daga baya aka ji labarin rasuwar Muhammadu Mai Barga Besse a jeji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng