'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban APC a Kano bayan kai Kazamin Hari
- ’Yan bindiga sun sake kai hari a wasu al’ummomi a Jihar Kano, inda suka kashe mutum guda tare da yin garkuwa da shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Rogo
- Wannan shi ne karo na uku a jere da ake samun hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar Kano, inda sabon harin ya faru a ƙauyen Beli da ke Rogo a ranar Talata
- Wata majiya ta tabbatar da harin, inda ta ce ’yan bindigar sun kutsa cikin ƙauyen da misalin ƙarfe 1:00 na dare, suka buɗe wuta tare da yin garkuwa da Alhaji Audu Fanka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – ’Yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Beli da ke ƙaramar hukumar Rogo ta Jihar Kano, inda suka kashe wani matashi tare da yin garkuwa da shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar.
Wata majiya da ta yi magana da manema labarai ba tare da bayyana sunanta ba ta ce maharan sun shiga garin da misalin ƙarfe 1:00 na dare ranar Talata, inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi.

Source: Facebook
Rahoton Premier Radio ya nuna cewa a yayin harin, ’yan bindigar sun harbe wani mazaunin garin tare da yin awon gaba da shugaban APC na Rogo, Alhaji Audu Fanka.
Barnar da aka yi a Kano
Rahotanni sun ce wani matashi ya rasa ransa sakamakon harin, yayin da wasu mazauna garin suka samu raunukan harbin bindiga.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu ƙarin bayani kan halin da mutanen da suka samu raunuka ke ciki ba ko wani mataki da aka dauka..
Haka zalika ba a samu cikakken bayani daga rundunar 'yan sandan jihar Kano ko gwamnati ba game da wanda aka sace ko kokarin ceto rayuwar shi.
Alakar Yahaya da Falgore
Rahoton da Daily Post ta wallafa ya nuna cewa shugaban APC na karamar hukumar Rogo da aka sace na da kusanci da Kakakin Majalisar jihar Kano.
Jaridar ta bayyana Yahaya a matsayin makusancin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Jibril Ismail Falgore.
Falgore ɗan asalin ƙaramar hukumar Rogo ne, inda lamarin sace shugaban jam’iyyar a yankin ya ƙara jefa mazauna yankin cikin fargaba.

Source: Original
Jihar Kano dai na cigaba da fama da hare-haren 'yan bindiga masu garkuwa da mutane duk da cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf na cewa tana daukar matakan da suka dace.
An kashe shugaban APC a Bebeji
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban APC na Rantan a ƙaramar hukumar Bebeji ta Jihar Kano, Alhaji Garba Buba, da wani mutum guda, Sulaiman Zunduma, sun mutu bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun harbe su.
Rahotanni daga mazauna karamar hukumar sun ce maharan sun shiga garin Rantan ne a daren Lahadi, inda suka buɗe wuta kan mazauna garin.
Wani mazaunin yankin ya ce Buba ya samu harbin bindiga a yayin harin, daga bisani ya rasu a asibiti yayin da ake ƙoƙarin ceto rayuwarsa.
Asali: Legit.ng

