Abba Ya Shiga Ya Fita a Canza Kwamishina da Wasu Jami‘an ‘Yan Sanda kafin Zabe a Kano
- Gwamnan Kano ya nemi a sauya Kwamishinan ’Yan Sandan jihar tare da wasu DPO gabanin zaɓen shekarar 2027
- Rahoton ya nuna cewa matakin ya biyo bayan rashin jituwa tsakanin gwamnan da kwamishinan ’yan sandan jihar
- Lamarin ya haifar da zargin yiwuwar katsalandan ta siyasa daga Abba Kabir Yusuf cikin harkokin tsaro lokacin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nemi a sauya masa wasu manyan jami’an rundunar ‘yan sanda.
A dokar kasa, gwamna bai da iko da harkokin ‘yan sanda har da wadanda suke jihar shi, duk da kasuwancewar shi babban mai kula da tsaro.

Source: Facebook
Gwamnan Kano yana so a canza kwamishinan 'yan sanda
Rahoton da Daily Nigerian ta fitar ya ce Gwamnan Kano yana neman hanyar rabuwa da Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ibrahim Bakori.

Kara karanta wannan
Kare ya haddasa babbar matsala da ake zargin ta jawo kashe wani bawan Allah a Kano
Haka zalika yana neman sauya wuraren aikin jami’an ’yan sanda 18 masu kula da ofisoshin ’yan sanda (DPOs) a wasu muhimman sassan jihar.
Majiyoyi sun bayyana cewa matakin na iya kasancewa wani yunƙuri ne na samun iko da rundunar ’yan sandan jihar gabanin zaɓen Janairu, 2027.
Wa gwamna yake so ya zama kwamishinan 'yan sandan Kano?
Rahoton ya ce gwamnan ya zaɓi sabon Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Mohammed Yusuf Adamu, domin ya maye gurbin CP Ibrahim Bakori a Kano.
Kwanan nan aka ƙara wa Mohammed Yusuf Adamu zuwa matakin Kwamishina a gidan ‘yan sanda.
Sabani tsakanin Abba Kabir da CP Ibrahim Bakori
Majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne daga rashin jituwa tsakanin gwamnan da kwamishinan ’yan sandan kan sauye-sauyen da aka yi wa jami'ai.
An CP Bakori ya sauya wasu DPO a Kano, kuma ya maye gurbinsu da manyan jami’ai bisa la’akari da girman mukami da kyakkyawan tarihin aikinsu.

Kara karanta wannan
"Nan ba da daɗewa ba yan Najeriya za su fara murna da tsare tsaren Shugaba Tinubu"
Wata majiya ta ce akwai jami’an CSP da dama da ba a ba su muhimman ayyuka ba, yayin da na bayansu su ke shugabantar sassan rundunar tsaron.
Saboda haka ne kwamishinan ya maye gurbin wasu da manyan jami’ai da ba su yin aikin komai.
Sai dai hakan bai yi wa gwamnan daɗi ba, wanda ake zargin ya nemi manya daga Abuja su sauya wannan mataki da kwamishinan jihar ya dauka.
An dauke DPO 18 daga jihar Kano
Rahoton ya ƙara da cewa Sufeto-Janar na ’Yan Sanda ya tura DPO 18 daga Kano zuwa wasu jihohi, ciki har da Yobe, Gombe, Kebbi da Sokoto.
Wasu jami’an kuma za su kumo jihohin makwabta irinsu Zamfara da Katsina, su cigaba da aiki.
Daga bisani, hedikwatar ’yan sandan ta bayar da umarnin mayar da wasu jami’an da CP Bakori ya sauya, aka bukaci ya maida su wurin aikinsu.
Abin da ya bada mamaki shi ne ana zargin cewa manyan ‘yan sanda sun yi umarni a yi wasu nade-nade da suka yi daidai da abin da gwamna yake so.
Ita ma Leadership ta dauko labarin, ta ce sassan da abin ya shafa sun haɗa da Fagge, Gwale, Ungogo, Kumbotso, Sharada, Bompai da Bichi.
Fargabar katsalandan a harkokin tsaro
Wannan lamari ya haifar da fargabar cewa 'yan siyasa na iya yin katsalandan wajen naɗa jami’an ’yan sanda domin samun tasiri da su a zaɓen 2027.
A baya an zargi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da neman ganin an tura jami’an ’yan sanda masu biyayya gare shi zuwa jihar.
Martanin rundunar ’yan sanda da gwamnatin Kano
Jaridar ta tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan ƙasa, Anietie Iniedu, domin jin ta bakinsa, amma bai amsa kiran waya da saƙon da aka aika masa ba.
A nasa ɓangaren, mai magana da yawun gwamnan Kano, Mustapha Mohammed, ya ce bai san dabatun ba, don haka ba zai iya yin tsokaci a kai ba.
Legit hausa ta lura ‘dan takaran gwamna a NDC, Aminu Abdussalam ya fara maganganu game da wannan zargi da ba a kai ga tabbatarwa ba tukuna.

Source: Facebook
Abba Kabir ya ce Allah Yake bada mulki
A wajen Abba Kabir Yusuf, maganar tazarce ba abin a mutu ko a yi rai ba ne, komai yana wurin Allah SWT kamar yadda aka ji labari.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na fuskantar kalubale game da burinsa na komawa mulkin jihar Kano a 2027 bayan dawowar NDC takara.
Ana cigaba da tattaunawa kan makomar mulkinsa gabanin zabe mai zuwa inda zai gamu da fushin musamman wasu 'yan Kwankwasiyya.
Asali: Legit.ng

