Yadda Buhari da Sojojinsa Suka Ki Yin Azumin Watan Ramadan saboda Yaki

Yadda Buhari da Sojojinsa Suka Ki Yin Azumin Watan Ramadan saboda Yaki

  • Marigayi Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi da dakarunsa sun daina azumin Ramadan a lokacin yakin basasar Najeriya
  • Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan a cikin littafin tarihinsa mai mujalladi uku, inda ya yi bayani kan rawar da ya taka a yakin
  • Buhari ya kuma bayyana yadda ya taimaka wa 'yan kabilar Igbo da suka rasa matsugunansu, tare da hukunta sojojin da e da hannu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bayyana dalilin da ya sa shi da dakarunsa suka ki yin azumin Ramadan.

Marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya ya sun ki yin azumin watan Ramadan a lokacin yakin basasar Najeriya, inda ya ce yakin na bukatar karfin jiki.

Yadda Buhari ya kaucewa azumi saboda yaki
Tsohon shugaban kasa a Najeriya, Muhammadu Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Instagram

Buhari ya bayyana hakan ne a cikin babi na bakwai zuwa na tara na littafin tarihinsa mai mujalladi uku mai suna Muhammadu Buhari: The Authorised Biography, wanda Dakta Yakubu Udu ya rubuta, cewar ThisDay.

Kara karanta wannan

Bangare 1 da Bola Tinubu ya yi wa Atiku da Peter Obi fintinkau a siyasa

Bayanin Buhari kan yakin basasa

A cikin littafin, tsohon shugaban kasar ya yi cikakken bayani kan yadda yakin basasar Najeriya ya samo asali, rikicin siyasa da soja da ya biyo bayan juyin mulkin 1966, da kuma rawar da ya taka a yakin.

Ya bayyana cewa juyin mulkin da aka yi a watan Yulin 1966, wanda ya hambarar da gwamnatin soja ta Janar Johnson Aguiyi-Ironsi, an dauke shi a Arewa a matsayin martani.

Buhari ya ambato Malam Liman Ciroma yana cewa juyin mulkin Janairun 1966 ya yi sanadin cire shugabannin Arewa na siyasa da soja daga gwamnati.

Ya ce bayan juyin mulkin na ramuwar gayya, Najeriya ta shafe kwanaki uku ba tare da cikakken jagoranci ba, saboda Birgediya Babafemi Ogundipe, shugaban ma'aikatan Ironsi, ya kasa shawo kan sojojin da suka yi tawaye.

Buhari ya bayyana cewa manyan hafsoshin Arewa sun goyi bayan Laftanar Kanal Yakubu Gowon, wanda yake da shekaru 31 a lokacin, inda suka nada shi shugaban kasa kuma babban kwamandan rundunar sojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya ayyana kan shi a matsayin cikakken dan APC

Ya ce Gowon ya saki fursunonin siyasa, ciki har da Cif Obafemi Awolowo, tare da soke dokar soja mai lamba 34 wadda gwamnatin Ironsi ta kafa, domin dawo da tsarin tarayya.

Yadda Buhari ya sha taba
Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammau Buhari. Hoto: Garba Shehu.
Source: Twitter

Yadda Buhari ya fara shan taba

Tsohon shugaban kasar ya kuma bayyana cewa a wani lokaci ya yi tattaki daga Makurdi zuwa gadar kan iyakar Kamaru, yana mai cewa kamar tafiya ce zuwa karshen Najeriya.

Buhari ya ce a lokacin yakin ya fara shan taba saboda matsin lamba, amma bai taba shan barasa ba saboda alkawarin da ya yi wa mahaifiyarsa, ya kara da cewa daga baya ya daina shan taba.

Ya bayyana cewa cututtuka irin su typhoid, zazzabin cizon sauro da hepatitis sun addabi sansanonin sojoji a lokacin yakin, lamarin da ya kara wahalar da rayuwar dakarun.

Dangane da azumin Ramadan, Buhari ya ce shi da sojojinsa ba su yin azumi a lokacin yakin saboda bukatar samun karfin jiki domin tunkarar kalubalen fagen daga, cewar Tribune.

Yadda Emefiele ya take umarnin Buhari

An ji cewa wani jami’in ’yan sanda ya shaida wa kotu cewa Godwin Emefiele ya sauya launin takardun naira maimakon sake tsara su kamar yadda Muhammadu Buhari ya amince.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya hada Kwankwaso da Obi ya yi masu rubdugu kan 2027

Shaidan ya ce bincike bai gano wata hujja da ke nuna cewa kwamitin gudanarwar CBN ya amince da sauyin launin ba.

EFCC na zargin Emefiele da sake fasalin takardun N200, N500 da N1,000 ba bisa ƙa’ida ba, da kuma buga kuɗin N684.5bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.