Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Rutsa Shugaban Matasan APC da Matarsa a cikin Gida
- Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace shugaban matasan APC na mzabar Ogbabede, Kwamared Arome Adaji, da matarsa
- Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na daren Laraba a kan titin Ajegwuna da ke Abocho, ƙaramar hukumar Dekina
- Wani jagoran al’umma ya ce maharan sun sauya dabarunsu, inda yanzu suke kai hare-hare a gidaje da gonaki maimakon kan tituna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi, Nigeria - Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da shugaban matasan jam’iyyar APC na mazabar Ogbabede da ke yankin Abocho, a ƙaramar hukumar Dekina ta Jihar Kogi, Mista Arome Adaji.
Rahotanni sun nuna cewa yan bindiga sun hada da matarsa, Misis Justina Arome, sun tafi da su wani wuri da ba a sani ba.

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa maharan sun sace ma’auratan ne daga gidansu da ke kan titin Ajegwuna, a Abocho, da misalin ƙarfe 8:0 na daren Laraba.
Shaidun da aka samu daga mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan bindiga ɗauke da makamai sun mamaye titin, inda suka riƙa harbe-harbe yayin da suke shiga yankin, hakan ya tilasta wa mazauna wurin tserewa domin tsira da rayukansu.
Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Ndamodu, ya ce Adaji, wanda aka fi sani da Iron Gate, da matarsa suna zaune suna hutawa a gidansu ne lokacin da suka ji ƙarar harbe-harbe kwatsam a kusa da gidan.
Yadda aka sace ma’auratan
Ndamodu ya ce ƙarar harbe-harben ta tsorata mazauna yankin, inda kowa ya guji fitowa saboda fargabar fadawa cikin musayar wuta ko kuma harsasan da aka harba su same shi.
Ya ce mazauna yankin ba su fito ba sai bayan maharan sun bar wurin, inda suka taru domin gano inda harin ya faru.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali da sojojin Najeriya suka tare wasu matasa, suka harbe su har lahira
A cewarsa, a lokacin ne suka gano cewa maharan sun tafi da shugaban matasan APC da matarsa.
Masu garkuwa sun sauya dabaru
Wani jagoran al’umma, Surveyor Agono Eneogba, ya ce masu garkuwa da mutane da ke kai hare-hare a yankunan Kogi ta Gabas sun ƙara mayar da hankali kan gidaje da gonaki, maimakon kai hare-hare a kan tituna.
A cewarsa, jami’an tsaro, ’yan sa-kai da mafarauta na yankin sun ƙarfafa sintiri da sa ido a kan tituna a wasu al’ummomin Kogi ta Gabas.

Source: Original
Sai dai ya ce tun makonni da dama da suka gabata, masu garkuwa sun rage kai hare-hare a kan tituna, inda suka mayar da hankali kan gidaje da gonaki ko ƙauyukan da ke kusa da gonaki.
Yan bindiga sun sace mutane 75
Kun ji cewa an sace akalla mutane 75 a sababbin hare-haren da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a Bungudu da wasu kauyuka a Zamfara.
Kansilan Mazabar Bungudu a Karamar Hukumar Bungudu, Honarabul Anas Sulaiman, ya ce ’yan bindigar sun zo da yawa, inda suka sace kusan mutane 13 a kusa da gidan ciyaman.
Asali: Legit.ng
