Rashin Tsaro Ya Aika da ‘Yan Sandan Najeriya 98 Barzahu a Shekarar 2026
- An kashe jami'an 'yan sanda 98 a jihohi 21 na Najeriya cikin watanni 10, daga Janairu zuwa Oktoba
- Yobe ce kan gaba da jami'ai 17 da aka kashe, sai Zamfara da Kebbi da jami'ai 14 a shekarar nan ta 2026
- Hare-haren 'yan bindiga da ’yan ta’addan Boko Haram ne suka haddasa mafi yawan mace-macen nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Aƙalla jami'an 'yan sanda 98 ne suka rasa rayukansu a hare-hare da wasu ta’adi daban-daban a shekarar nan.
An tattaro wadannan mummunan alkaluma ne daga jihohi 21 na Najeriya tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba 2026.

Source: Getty Images
An rasa 'yan sanda 98 a jihohi 21

Kara karanta wannan
Kamfanin simintin Ashaka ya kulla yarjejeniyar cigaban al'umma na shekaru 5 da Funakaye
Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna yadda matsalar tsaro ta ke cin musamman jami’ai na ‘yan sanda.
Alkaluman da aka samu sun fito ne daga rahotannin labarai da hukumomin 'yan sanda suka tabbatar a cikin watanni 10.
Mutuwar jami'an ta faru ne sakamakon hare-haren 'yan bindiga, masu ɗauke da makamai da 'yan ta'adda da suka fitini jama’a.
Wasu sun mutu a dalilin haɗurra a kan tituna da kuma harbe-harben da jami'an 'yan sanda suka yi wa junansu duk shekarar nan.
Alkaluman asarar 'yan sanda a jihohi a 2026
Jihar Yobe ce ta fi kowace jiha asarar jami'an tsaro, an kashe 'yan sanda 17. Jihohin Zamfara da Kebbi sun biyo baya da jami'ai 14.
An kashe jami'ai biyar a Katsina, sai Borno da Taraba suka yi asarar jami'ai huɗu na ‘yan sandan daga farkon shekara zuwa yanzu.
Jihohin Rivers, Sokoto, Plateau, Enugu, Lagos da Imo sun rasa jami'ai uku zuwa yanzu.
Oyo, Anambra, Abia, Kaduna da Kogi sun rasa jami'ai biyu. Sannan an kashe ɗan sanda guda a duk jihohin nan: Adamawa, Kano da Neja.
Waɗanda suka fi kashe 'yan sandan
Binciken da aka yi ya nuna cewa a bana, 'yan bindiga ne suka fi kashe jami'an, su ne suka yi sanadin mutuwar jami’an tsaro har 35.
Miyagu masu ɗauke da makamai sun kashe 29, sai 'yan ta'addan Boko Haram da suka kashe jami'ai 22 a tsawon wannan lokaci.
Haka kuma, 'yan ta'addan Lakurawa sun kashe jami'ai biyu a watanni 10. Rahoton ya zo a jaridar 21st Century Chronicle.
Sauran mace-macen sun haɗa da jami'ai uku da abokan aikinsu suka harbe, huɗu da suka mutu a haɗurran ababen hawa.
Akwai ɗaya da masu garkuwa da mutane suka kashe, da wani da 'yan daba suka kashe, haka tsageru sun hallaka jami’i guda.
Hare-haren da suka fi muni a bana
Ɗaya daga cikin munanan hare-haren ya faru ne a jihar Kebbi, inda aka kashe 'yan sanda 10 yayin musayar wuta da 'yan bindiga.
A jihar Yobe kuma, an kashe jami'an tsaro 17 yayin harin da aka kai makarantar horas da dakarun sojoji a watan Mayu a Buni-Yadi.
Jihar Benue ma ta fuskanci munanan hare-hare, ciki har da kisan jami'an 'yan sanda huɗu yayin musayar wuta da 'yan bindiga.
'Yan sanda suna kashe abokan aikinsu
Binciken ya kuma gano wasu jami'an sun rasa rayukansu sakamakon harbin da abokan aikinsu suka yi musu da gan-gan ko akasinsa.
A watan Janairu, an zargi wani ɗan sanda da harbe abokin aikinsa, Sani Malumfashi har lahira a garin Onne da ke jihar Rivers.
A watan Oktoba kuma, wani kofur na ɗan sanda, Amos Yusuf, ya harbe abokin aikinsa, Kofur Grace Onimisi a garin Ajakouta.
Bayan wannan aika-aika a jihar Kogi, an rahoto cewa shi ma jami’in tsaron ya kashe kansa.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun sace 'yan mata a Neja
A wasu sababbin hare-haren ’yan bindiga, ana da labarin yadda aka sace ɗalibai mata 12 daga Islamiyya a kauyen jihar Neja.
An dauke yaran ne lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan yi wa malaminsu aiki a gonarsa a karamar hukumar Rafi.
A yanzu ‘yan bindiga sun hana manoma shiga gonakinsu bayan kwanaki an yi awon gaba da masallata har yau babu labarinsu.
Asali: Legit.ng


