PDP Ta Kori Manyan Jam'iyyar da ke Adawa da Takarar Pantami a Gombe

PDP Ta Kori Manyan Jam'iyyar da ke Adawa da Takarar Pantami a Gombe

  • Jam'iyyar PDP ta kori manyan jiga-jiganta biyu a jihar Gombe, Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki da Hon. Usman Aliyu Garry
  • Jam'iyyar ta ɗauki matakin ne bisa zargin ayyukan cin amana da kuma rashin ɗa'a da ta ce sun saɓa wa dokokinta.
  • Matakin ya biyo bayan binciken kwamitin ladabtarwa na PDP, yayin da 'yan siyasar ke ƙalubalantar fitowar Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Jam'iyyar PDP ta kori wasu daga cikin manyan jiga-jiganta biyu a jihar Gombe bisa zargin aikata laifukan da suka saɓa wa dokokin jam'iyyar.

Waɗanda aka kora su ne Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki da Hon. Usman Aliyu Garry, waɗanda jam'iyyar ta zarga da ayyukan cin amana da kuma rashin ɗa'a.

Hon. Garry da Khamisu Mailantarki
Manyan PDP da aka kora a Gombe. Hoto: PDP Gombe State
Source: Facebook

PDP ta wallafa a Facebook cewa matakin na nufin mutanen biyu sun rasa kasancewarsu mambobin jam'iyyar, tare da dukkan haƙƙoƙi da gata da suke samu a matsayinsu na 'ya'yanta.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Tinubu ya fada kan zabe bayan shiga dakin Ka'aba a Saudi

Dalilin da ya sa PDP ta kore su

Vanguard ta wallafa cewa sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Hon. Jungudo Haruna Mohammed, ne ya sanar da korar a cikin wata sanarwa.

Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan sakamakon binciken kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar da kuma nazarin rahoton da hukumomin da abin ya shafa na jam'iyyar suka yi.

Sanarwar ta bayyana cewa laifukan da ake zargin mutanen biyu da aikatawa sun faɗa ƙarƙashin sashe na 58(1)(a), (b), (h) da (j) na kundin tsarin mulkin PDP na shekarar 2017 da aka yi wa kwaskwarima.

Waɗannan sassa sun shafi rashin ɗa'a da ayyukan da ka iya jawo wa jam'iyyar zubar da mutunci.

PDP ta kuma jaddada cewa ta bi ƙa'idojin sauraron ɓangarorin da abin ya shafa, kamar yadda sashe na 57(6) na kundin tsarin mulkinta da sashe na 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 suka tanada.

Haƙƙoƙin da suka rasa a PDP

Kara karanta wannan

Ana shirye shiryen zaben 2027, Atiku ya mika babbar bukata ga INEC

Jam'iyyar ta ce bisa sashe na 59(1)(j) na kundin tsarin mulkinta, Mailantarki da Garry sun daina kasancewa mambobinta.

Hakan na nufin ba za su ƙara cin gajiyar haƙƙoƙi, gata ko wata alaƙa da tsarin tafiyar da jam'iyyar ba.

PDP ta jaddada cewa babu wani mamba da matsayinsa zai ba shi kariya daga hukuncin ladabtarwa idan ya saɓa wa dokokin jam'iyyar.

A cikin sanarwar, jam'iyyar ta ce:

"Babu wani mamba, ko da kuwa matsayinsa, da ya fi ƙarfin dokokin jam'iyyar da tsarin ladabtarwarta."

Ta ƙara da cewa kundin tsarin mulkinta shi ne babban jagora da ya rataya a wuyan dukkan mambobinta, ba tare da la'akari da matsayinsu ba.

Sheikh Pantami a taron PDP
Sheikh Isa Ali Pantami a wajen taron PDP a Gombe. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Korarsu ta zo ne a daidai lokacin da Khamisu Ahmed Mailantarki da Usman Aliyu Garry ke cikin 'yan jam'iyyar da ke ƙalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar gwamnan Gombe na PDP.

PDP ta taya Pantami murna

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP a jihar Gombe ta yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) bisa sanya sunan Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a shafinta na yanar gizo.

Kara karanta wannan

Obasanjo da babbar ƴarsa sun yi wa juna habaici cikin dubban jama'a

Pantami, wanda ke riƙe da sarautar gargajiya ta Majidadin Daular Usmaniyya, ya samu amincewar hukumar bayan ta tantance cewa ya cika dukkan ƙa'idojin kundin tsarin mulkin Najeriya da dokar zaɓe.

Jam'iyyar ta bayyana cewa amincewar Pantami za ta ƙara faɗaɗa damar zaɓin al'umma, inganta gasa ta siyasa da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a jihar Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng