Ayarin Shugaba Tinubu Ya Jefa Mutane cikin Babbar Matsala Ta Tsawon Lokaci a Abuja
- An samu cunkoson ababen hawa na tsawon sa’o’i a hanyar Lugbe zuwa Airport Road sakamakon ziyarar Shugaba Bola Tinubu a Jabi
- Wasu matafiya sun ce sun shafe kusan sa’o’i uku a hanyoyin da suka saba ɗaukar mintuna 20 zuwa 30, yayin da kuɗin mota ya ƙaru
- Mazauna Abuja sun buƙaci fadar shugaban ƙasa da jami’an tsaro su sauya tsarin tare da samar da tsaro ba tare da jefa dubban mutane cikin wahala ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Mazauna Abuja da ke zirga-zirga tsakanin tsakiyar birnin da sauran sassan birnin ta hanyar Lugbe da Airport Road sun shafe sa’o’i a cunkoson ababen hawa ranar Alhamis.
Lamarin ya faru ne bayan jami’an tsaro suka rufe wasu hanyoyi domin tabbatar da tsaro yayin wucewar ayarin Shugaba Bola Tinubu, wanda ya kai ziyara unguwar Jabi.

Kara karanta wannan
2027: Magoya bayan APC sun yi takansu da rigima ta ɓarke a wurin yakin neman zaben gwamna

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa zirga-zirgar ababen hawa a kan titin filin jirgi ta samu tsaiko yayin da Tinubu ya halarci taron ƙaddamar da wani littafin da Wole Olanipekun, SAN, ya rubuta a Jabi.
Ayarin Tinubu ya haddasa cunkoso
Matakin ya sa matafiya da dama suka makale a hanya, yayin da wasu fasinjoji suka biya kuɗin mota fiye da yadda suka saba saboda direbobi sun sha wahala wajen samun hanyoyin da za su bi.
An ce direbobi da matafiya da dama da suka makale a cunkoson jiya sun nuna fushi da takaici, inda suka bayyana matakin rufe hanyoyin a matsayin wanda ba dole ba kuma rashin adalci ga jama'a.
Adedoyin Ayinde, wanda ke tafiya daga Lugbe zuwa Jabi domin zuwa wurin aiki, ya ce ya shafe sama da sa’o’i uku a tafiyar da a al’adance ba ta wuce mintuna 30 ba.
Ya ce abin takaici ne yadda aka jefa daruruwan ’yan ƙasa cikin irin wannan wahala na tsawon sa’o’i saboda kawai shugaban ƙasa zai halarci bikin ƙaddamar da littafi.
Mutane sun nuna damuwa kan lamarin
Wani direba, Obinna Eze, ya kuma tambayi dalilin da zai sa a rufe babbar hanyar gwamnatin tarayya a Abuja na tsawon sa’o’i saboda zirga-zirgar shugaban ƙasa.
Mutane sun koka da cewa rufe hanyoyin da ake yi yayin wucewar shugaban ƙasa zuwa filin jirgin sama ko dawowa daga can ya zama ruwan dare, musamman ga matafiya da ke amfani da hanyar Airport Road.

Source: Facebook
Sun yi kira ga fadar shugaban ƙasa da hukumomin tsaro da su sake duba wannan tsari, suna mai cewa za a iya samar da isasshen tsaro ba tare da jefa dubban masu amfani da hanyoyi cikin wahala na tsawon lokaci ba.
Tinubu zai rage tsadar sufuri
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya bayyana shirin rage kuɗin sufuri da kusan kashi 40 cikin 100 sakamakon wahalhalun da ake fuskanta.
Ya bayyana cewa tsadar sufuri na ƙara wa iyalai matsin tattalin arziki, domin tana rage kuɗin da mutane ke iya adanawa ko amfani da shi wajen biyan buƙatun gida.
Asali: Legit.ng
