'Yan Najeriya Sun Sha kudi, Tinubu Ya Raba Sama da Naira Biliyan 100

'Yan Najeriya Sun Sha kudi, Tinubu Ya Raba Sama da Naira Biliyan 100

  • Gwamnatin tarayya ta kammala rabon Naira biliyan 75 ga masu masana'antu 104 domin ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida da bunƙasa tattalin arziki
  • Haka kuma, gwamnati ta raba Naira biliyan 65.8 ga ƙananan 'yan kasuwa 15,018 domin faɗaɗa harkokinsu da samar da ayyukan yi
  • Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Jumoke Oduwole, ce ta bayyana hakan, inda ta ce tallafin na daga cikin shirin gwamnati na bunƙasa kasuwanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta kammala fitar da Naira biliyan 75 ga masu masana'antu 104, yayin da ta raba Naira biliyan 65.8 ga ƙananan 'yan kasuwa 15,018 a faɗin Najeriya.

Gwamnati ta ɗauki matakin ne domin ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida, faɗaɗa harkokin kasuwanci da samar da guraben ayyukan yi ga 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Takarar Makinde ta fara tangal tangal, masu muƙamai 3 su yi murabus

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na jawabi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dr Jumoke Oduwole, ce ta bayyana hakan yayin wani jawabi mai taken 'Amfani da Damarmakin Tattalin Arzikin Najeriya Domin Samar da Ci Gaba'.

Yadda aka raba tallafin N200bn

Ministar ta bayyana cewa rabon kuɗin na daga cikin shirin tallafin Naira biliyan 200 da gwamnatin tarayya ta samar, wanda Bankin Masana'antu (BoI) ke kula da shi.

Shirin ya ƙunshi tallafin Naira biliyan 50 ga ƙananan sana'o'i, Naira biliyan 75 ga ƙananan da matsakaitan 'yan kasuwa, da kuma Naira biliyan 75 ga masu masana'antu.

Oduwole ta ce an kammala fitar da dukkan Naira biliyan 75 da aka ware wa masana'antu 104, yayin da aka fitar da Naira biliyan 65.8 ga 'yan kasuwa 15,018 ƙarƙashin shirin tallafawa ƙananan sana'o'i zuwa ƙarshen zangon farko na shekarar 2026.

Ta jaddada cewa bai kamata a auna nasarar tallafin gwamnati da yawan kuɗaɗen da aka raba kawai ba, sai dai da yadda ya taimaka wajen ƙarfafa kasuwanci, ƙara yawan kayayyakin da ake samarwa da inganta rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

PDP ta kori manyan jam'iyyar da ke adawa da takarar Pantami a Gombe

Matsalar masana'antun Najeriya

Ministar ta amince cewa samun jari na ci gaba da zama babban ƙalubale ga masu masana'antu, musamman wajen sayen injuna, samar da kayan aiki, faɗaɗa masana'antu da ɗaukar ma'aikata.

Ta ce sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya na buƙatar tsare-tsaren kashe kuɗi masu kyau, daidaiton tsarin kuɗi da kuma manufofin da za su tallafa wa samar da kayayyaki a cikin gida.

Taswirar Abuja
Taswirar Abuja a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Original

A cewarta, gwamnati na ƙoƙarin kawar da matsalolin da ke hana zuba jari, samar da kayayyaki da kasuwanci, domin samar da yanayin da zai ba kamfanoni damar bunƙasa.

Bola Tinubu ya gama Umrah

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kammala ziyarar ibada da ya kai ƙasar Saudiyya, inda ya yi addu'ar samun zaman lafiya da ci gaba a Najeriya.

A yayin ziyarar, Tinubu da tawagarsa sun samu damar shiga cikin Ka'aba mai alfarma da ke birnin Makka domin gudanar da addu'o'i da ibadar Umrah.

Shugaban ƙasar ya gode wa Sarkin Saudiyya da Yarima mai jiran gado bisa damar da suka ba shi da kuma kyakkyawar tarbar da suka yi masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng