'Yan Ta'adda Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Lahani a Kebbi, an Kashe Fararen Hula
- ’Yan sanda sun tabbatar da kashe sufeto guda da fararen hula 11 a hare-haren da aka kai ƙauyukan Waiwayi da Kystu da ke ƙaramar hukumar Koko/Besse a Kebbi
- Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ya ce sufeton ya rasu ne yayin musayar wuta da maharan
- Maharan sun ƙona wasu gidaje tare da satar kayan abinci a shaguna, lamarin da ya tilasta wa mazauna ƙauyukan tserewa domin neman mafaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Mamudawa/Lakurawa ne sun kashe sufeton ’yan sanda da fararen hula 11 a hare-haren da suka kai ƙauyukan Waiwayi da Kystu, da ke ƙaramar hukumar Koko/Besse a jihar Kebbi.
Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da mutuwar mutanen, inda ta bayyana cewa sufeton ya rasu ne yayin musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da maharan.

Source: Facebook
’Yan sanda sun tabbatar da kisan sufeta
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar Vanguard.
Bashir Usman ya ce har yanzu ba a bayyana sunan sufeton da aka kashe ba, saboda ana ci gaba da bincike kan lamarin.
"Eh, an kai hari ƙauyukan Waiwayi da Kystu daga wasu da ake zargin Mamudawa ne. Abin takaici, yayin musayar wuta, sun kashe sufeto ɗaya na ’yan sanda. Ba zan iya bayyana sunansa ba sai mun kammala bincike.” In ji shi.
Baya ga kashe-kashen, an kuma ruwaito cewa maharan sun ƙona wasu gidaje tare da kwashe kayan abinci daga shagunan da ke yankunan da aka kai wa harin.
Mazauna kauyukan sun tsere daga gidajensu
Hare-haren sun tilasta wa mazauna ƙauyukan da suka tsira tserewa daga gidajensu domin neman wuraren da za su samu tsaro.
Lamarin ya ƙara jefa al’ummomin yankin cikin fargaba, musamman saboda yadda hare-haren da ake kai wa ƙauyuka ke barazana ga rayukan jama’a da dukiyoyinsu.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: 'Yan bindiga sun nuna wa mata kusan 30 da karamin yaro rashin imani
An kaddamar da farautar maharan
Bashir Usman ya bayyana cewa jami’an ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun kewaye wuraren da aka kai harin domin hana sake kai wasu hare-hare.
Ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun fara farautar waɗanda ake zargi da kai harin domin kamo su tare da gurfanar da su a gaban doka.
Wannan hari ya ƙara nuna matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan jihar Kebbi, inda hare-haren da ake kai wa al’ummomin karkara ke jefa rayuka, sana’o’i da dukiyoyin jama’a cikin haɗari.

Source: Original
'Yan bindiga sun sace mata a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa Wasu ’yan bindiga sun kai hari ƙauyuka huɗu a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja a yankin Arewa ta Tsakiya.
Majiyoyi sun nuna cewa yan ta'addan sun tattara mata 29 da wani karamin yaro, sun yi awon gaba da su.
Maharan sun kai hare-haren ne a ƙauyukan Kwimo, Kalgo, Kakaki da Mabona duk a karkashin karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.
Asali: Legit.ng
