Kamfanin Simintin Ashaka Ya Kulla Yarjejeniyar Cigaban Al'umma na Shekaru 5 da Funakaye

Kamfanin Simintin Ashaka Ya Kulla Yarjejeniyar Cigaban Al'umma na Shekaru 5 da Funakaye

Jihar Gombe - ​Kamfanin siminti na Ashaka (Ashaka Cement Limited), wanda reshen HBM Nigeria Plc ne, ya sanya hannu kan yarjejeniyoyin ci gaban al'umma na tsawon shekaru biyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kamfanin ya sanya hannu kan yarjeniyoyin ne wadanda za su fara daga shekarar 2026 zuwa 2030, da al'ummomin Funakaye da Maiganga da ke kananan hukumomin Funakaye da Akko a Jihar Gombe.

Kamfanin simintin Ashaka ya kulla yarjejeniya
Mutanen da suka halarci kulla yarjejeniya Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

An gudanar da bikin sanya hannun yarjejeniyar ne a Ma'aikatar Makamashi da Albarkatun Ma'adinai ta Jihar Gombe.

Abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa

Yarjejeniyar ta tanadi yadda kamfanin zai gudanar da ayyukan tallafa wa al'umma (CSR) a fannonin ilimi, kiwon lafiya, noma, hanyoyi, samar da ruwan sha, samar da ayyukan yi da tsaro.

Wannan na nuna aniyar kamfanin na inganta rayuwar al'ummar da ke makwabtaka da shi tare da bunkasa ababen more rayuwarsu.

Da yake jawabi a wajen bikin, Manajan Daraktan kamfanin siminti na Ashaka, Alhaji Ibrahim Aminu, ya tabbatar wa al'ummomin cewa kamfanin zai aiwatar da dukkan ayyukan da aka amince da su a cikin yarjejeniyar.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya

Ya bayyana cewa ‘ayyukan sun hada da tallafawa harkokin noma da kula da muhalli, tallafawa matasa da mata, bayar da tallafin karatu, hako rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana, gyaran hanyoyi, da kuma gina makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya a garuruwan Funakaye da Maiganga’

Za a fadada kamfanin

Haka kuma, ya sanar da cewa HBM Nigeria Plc, wanda ke karkashin kamfanin Huaxin Group, ya fara wani babban shirin fadada masana'anta domin kara karfin samar da siminti zuwa sama da ninki uku na yadda take samarwa a halin yanzu.

Ana sa ran kammala aikin tare da fara amfani da shi a zangon farko na shekarar 2027. Ya kuma bayyana cewa fadada masana'antar zai samar da karin guraben ayyukan yi ga 'yan asalin al'ummomin da ke makwabtaka da kamfanin.

Amfanin kulla yarjejeniyar

Kwamishinan Makamashi da Albarkatun Ma'adinai na Jihar Gombe, Injiniya Sanusi Ahmed Pindiga, ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta kara karfafa alakar kamfanin da al'ummomin da ke makwabtaka da shi, ta hanyar samar da ingantaccen tsari na warware sabani da korafe-korafe ta hanyar tattaunawa.

Pindiga ya bukaci bangarorin biyu da su cika alkawuran da suka dauka. Ya kuma bayyana cewa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya sanya hannu kan wata dokar zartarwa a ranar 4 ga watan Agusta domin karfafa sa ido kan ayyukan hakar ma'adinai wanda ya wajabta wa kamfanonin hakar ma'adinai da duwatsu su tabbatar da anyi riko da yarjejeniyoyin tsakanin su da al'ummomin da suke gudanar da ayyuka a yankunansu.

Kara karanta wannan

Majalisa ta tsawaita dakatarwar da ta yi wa shugabannin ƙananan hukumomi 3 a Kano

A nata jawabin, Madam Abimbola Adams, wadda ta wakilci Ministan Raya Albarkatun Ma'adinai na Kasa, Mista Dele Alake, ta bayyana yarjejeniyar a matsayin hadin gwiwa da aka gina bisa amana da daukar nauyin juna.

Ta bukaci kamfanin da ya sauke nauyin da ke kansa, sannan al'ummomin su tabbatar da zaman lafiya da samuwar kyakkyawar alaka.

An bayar da shawarwari

Dagacin gundumar Atiku, Injiniya Muhammad Ardo, ya yabawa bangarorin biyu bisa yadda suka shawo kan sabanin da ya faru a baya, inda ya bayyana fatansa cewa yarjejeniyar za ta samar da zaman lafiya mai dorewa.

A nasa jawabin, Shugaban al'ummar Maiganga, Mista David Daniel, ya yi kira da a rika warware matsaloli ta hanyar tattaunawa, mutunta doka da kuma gudanar da bincike mai kyau kan duk wani korafi. Ya kuma bukaci mazauna yankin da su guji daukar doka a hannunsu.

Manyan baki da suka halarci taron sun hada da jami'ai daga Ma'aikatar Raya Albarkatun Ma'adinai ta Tarayya, shugabannin al'umma, manyan jami'an gwamnatin jihar, wakilin shugaban karamar hukumar Akko, mambobin kwamitin hulda tsakanin kamfanin da al'ummomin Funakaye da Maiganga, shugabannin hukumomin tsaro, lauyoyi da kuma 'yan jarida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Legit.ng Branded Content avatar

Legit.ng Branded Content (marketing page) This account is used for publishing branded/sponsored content. For any enquiries please email: ads@corp.legit.ng or call: +234 810 304 48 99