Takarar Gwarzo: APC Ta Yi Zazzafan Martani ga Kwankwaso, Ta Cilla Zarge Zarge

Takarar Gwarzo: APC Ta Yi Zazzafan Martani ga Kwankwaso, Ta Cilla Zarge Zarge

  • Jam'iyyar APC ta zargi Rabiu Kwankwaso da ƙoƙarin ɗora mata laifin rikicin shari'ar da ya dabaibaye jam'iyyar NDC a Kano
  • APC ta ce wasu mambobin NDC ne suka shigar da ƙara kan jam'iyyarsu, ba ita ko Gwamna Abba Kabir Yusuf ba
  • Jam'iyyar ta buƙaci Kwankwaso ya gabatar da hujjoji masu ƙarfi da ke nuna hannun APC a shari'ar Aminu Abdussalam Gwarzo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano – Jam'iyyar APC a jihar Kano ta zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ƙoƙarin karkatar da hankali daga rikicin shari'ar cikin gida da ke addabar jam'iyyar NDC.

Jam'iyyar ta musanta hannu a yunƙurin hana ɗan takarar gwamnan NDC, Aminu Abdussalam Gwarzo, tsayawa takara a zaɓen shekarar 2027.

APC a Kano ta dura kan Kwankwaso
Gwamna Abba Kabir na jihar Kano da Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

APC ta ƙalubalanci Kwankwaso da ya gabatar da sahihan hujjoji da ke nuna alaƙar jam'iyyar ko ɗan takararta na gwamna, Abba Kabir Yusuf, da shari'ar, cewar PM News.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun sha kudi, Tinubu ya raba sama da Naira biliyan 100

APC ta musanta hannu a shari'ar Gwarzo

A cewar jam'iyyar, wasu mambobin NDC ne suka shigar da ƙara a kan jam'iyyarsu, ba APC, Gwamna Yusuf ko gwamnatin jihar Kano ba.

APC ta jaddada cewa ita da gwamnan ba su ɗauki nauyin shari'ar ba, kuma ba su yi tasiri ko taimakawa wajen shigar da ƙarar ba.

Jam'iyyar ta bayyana zargin Kwankwaso a matsayin ƙarya da rashin tushe, tana zarginsa da ƙoƙarin yi wa abokan hamayyarsa siyasa baƙar magana domin kawar da hankalin jama'a daga matsalolin cikin jam'iyyarsa.

Ta yi gargaɗin cewa zarge-zargen da ba su da hujja na iya yaudarar jama'a tare da ƙara tayar da hankalin siyasa.

Takarar Gwarzo ta jawo wa Kwankwaso magana
Mataimakin dan takarar shugaban kasa a NDC, Sanata Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

APC ta yi magana kan shari'ar siyasar Kano

Jam'iyyar ta ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa duk wani ɗan takara da ya cancanta damar shiga zaɓe bisa tanadin doka.

Ta kuma musanta cewa tana da niyyar amfani da ƙarfin ikon gwamnati wajen gallaza wa abokan hamayyarta siyasa, cewar Punch.

Kara karanta wannan

PDP ta kori manyan jam'iyyar da ke adawa da takarar Pantami a Gombe

APC ta ƙara da cewa ɓangaren shari'a yana cin gashin kansa, kuma ita ko Gwamna Yusuf ba su da ikon tsara yadda kotuna za su gudanar da shari'o'i ko yanke hukunci.

Jam'iyyar ta buƙaci Rabiu Kwankwaso da sauran 'yan siyasa su bar hukumomin da abin ya shafa su gudanar da ayyukansu ba tare da siyasantar da rikice-rikicen cikin gida na jam'iyyu ba.

Haka kuma, ta zargi 'yan adawa da neman hujjar da za su jingina wa yiwuwar shan kayen da za su yi a zaɓe.

APC ta buƙaci jama'a su yi watsi da zarge-zargen da ke danganta ta da matsalolin shari'a da Aminu Abdussalam Gwarzo ke fuskanta.

Kwankwaso ya ba Atiku shawara

An ji cewa dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya ce bai kamata Atiku Abubakar ya karya tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu ba.

Kwankwaso ya buƙaci Atiku ya mara wa Peter Obi baya domin Kudu ta kammala wa’adin mulkin da ya rage mata kafin shugabancin ya koma Arewa.

Tsohon gwamnan Kano ya ce ya taɓa yin watsi da burinsa na zama shugaban ƙasa domin ba wa Obi damar tsayawa takara, saboda sun yi imani da manufofi iri ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.