Jagora a Izala Ya Yi Magana game da Kashe Sheikh Masussuka
- Wani babban limamin JIBWIS a Abuja, Imam Ibrahim Aliyu Kaduna, ya ce suna adawa da akidar marigayi Sheikh Yahaya Masussuka saboda kin amincewa da Hadisi
- Limamin ya bayyana cewa Musulunci ba zai cika ba tare da bin Sunnar Annabi ba, domin ita ce ke karin bayani kan umarnin da ke cikin Alkur’ani
- Sai malamin ya yi Allah-wadai da kashe Masussuka, yana mai cewa bai kamata a kashe mutum saboda bambancin akida ko fahimtar addini ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Mataimakin sakataren majalisar malaman JIBWIS a Abuja, Imam Ibrahim Aliyu Kaduna, ya bayyana dalilan da suka sa suke adawa da akidar marigayi Sheikh Yahaya Masussuka, duk da cewa sun yi Allah-wadai da kashe shi.
Limamin, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin gudanarwa na JIBWIS a Abuja, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi, inda ya yi karin bayani kan bambancin fahimtarsa da koyarwar marigayin malamin.

Source: Facebook
A tattaunawa da Daily Trust, malamin ya ce babban abin da suke adawa da shi shi ne yadda Masussuka ya dogara da Alkur’ani kadai wajen fahimtar addini, ba tare da amincewa da Hadisan Annabi Muhammad (SAW) da SunnarSa ba.
Dalilin adawa da akidar Masussuka
Imam Ibrahim Aliyu Kaduna ya ce akidar Masussuka ta ginu ne kan cewa Alkur’ani shi kadai ne tushen koyarwar addini, ba tare da bukatar Hadisan Annabi ba.
Ya bayyana cewa wannan fahimta ta saba wa koyarwar Alkur’ani da kansa, domin Allah ya umurci Annabi Muhammad (SAW) da ya yi wa mutane bayanin abin da aka saukar masu.
Limamin ya kawo ayar da Allah ya ce:
“Mun saukar maka da Alkur’ani domin ka bayyana wa mutane abin da aka saukar masu.”
A cewarsa, wannan aya ta nuna cewa duk da cewa Alkur’ani shi ne littafin Allah, an damka wa Manzon Allah (SAW) aikin bayyana ma’anoni da yadda za a aiwatar da wasu umarnin da ke cikinsa.

Source: Facebook
Ya ce wadannan bayanai suna kunshe ne cikin Hadisai da Sunnar Annabi, don haka Musulmi na bukatar nazarin ilimin Hadisi domin fahimtar yadda za su gudanar da ibadunsu.
Ya kara da cewa ilimin Hadisi fanni ne na musamman a Musulunci, wanda ake bukatar zurfafa karatu a kansa domin fahimtar yadda ake tantancewa da amfani da Hadisan Annabi.
Maganar aiki da Hadisi a ibada
Limamin ya yi misali da dawafi a Ka’aba, inda ya ce Alkur’ani ya umurci Musulmi da yin dawafi, amma ba a fayyace adadin zagayen da za a yi ba.
Ya ce ta hanyar Hadisan Annabi ne aka fahimci cewa dawafi yana kunshe da zagaye bakwai, da kuma yadda mutum zai fara da inda zai kare.
Ya kuma yi misali da sallah, inda ya bayyana cewa wasu bayanai kamar adadin raka’o’in kowace sallah da yadda ake gudanar da ita suna bukatar komawa ga Sunnar Annabi (SAW).
Haka kuma, ya ce bayanai kan wankan gawa, likkafani, yadda ake shirya kabari da sauran abubuwan da suka shafi jana’iza suna cikin koyarwar Annabi da aka ruwaito ta hanyar Hadisai.
Dangane da zakka kuwa, limamin ya ce Alkur’ani ya yi umarni da bayar da hakkin amfanin gona a ranar girbinsa, amma Sunnah ce ta yi karin bayani kan adadin abin da za a bayar da kuma nau’in amfanin gonar da zakka ta wajaba a kansa.
Ya ce haka abin yake ga zakka a kan dabbobi, domin akwai bambanci tsakanin rakuma, shanu da tumaki, yayin da ake bukatar karin bayani kan sharudan da suka shafi kowanne.
Meye alakar Masussuka da Maitatsine?
Imam Ibrahim ya bayyana cewa yana ganin koyarwar Masussuka ta kunshi kuskure wajen fahimtar Musulunci, yana mai zargin cewa hakan na iya rikitar da mutanen da ba su da zurfin ilimin addini.
Ya yi ikirarin cewa akidar ta samo asali ne daga koyarwar Muhammadu Marwa Maitatsine, wanda ya yada irin wannan fahimta a wasu sassan Afirka a baya.
A cewarsa, Masussuka ya taba amincewa da cewa almajirin Maitatsine ne, yayin da ake cewa iyayensa ma sun kasance cikin mabiyansa.
Limamin ya ce wannan na nuna yadda irin wannan akida ta rika wucewa daga wani zamani zuwa wani, har ta kai ga mabiyanta na yanzu.
Ya kuma yi tambaya kan bukatar mabiyan Masussuka na tattara karatunsa a na’urorin zamani domin al’ummomi masu zuwa su amfana da su, alhali kuwa suna kin amincewa da tattara koyarwar Annabi Muhammad (SAW) ta hanyar Hadisai.
Ya ce akwai sabani a cikin wannan matsaya, domin idan ana ganin ya dace a adana karatun Masussuka, ya kamata a ba wa koyarwar Annabi muhimmanci fiye da haka.

Source: Facebook
JIBWIS ta yi tir da kashe Masussuka
Duk da bambancin akida da fahimtar addini, Imam Ibrahim ya ce kashe Masussuka abin bakin ciki ne, kuma babu wani mai wa’azin Musulunci da zai ji dadin kashe wani mutum saboda bambancin fahimtar addini.
Ya bayyana cewa manufar Ahlus Sunnah wal Jama’ah ita ce kira zuwa ga gaskiya, da kokarin shawo kan wadanda ake ganin sun karkata daga koyarwar addini domin su dawo kan hanya madaidaiciya.
Ya ce nasarar mai wa’azi ita ce ya samu wanda yake da ra’ayi daban ya fahimci gaskiya, ya bar abin da ba daidai ba, ba wai a kawar da shi ta hanyar kashe shi ba.
Limamin ya jaddada cewa su a matsayin mambobin JIBWIS da Ahlus Sunnah wal Jama’ah sun yi Allah-wadai da kisan, yana mai cewa ba sa goyon bayan kashe kowa, Musulmi ko wanda ba Musulmi ba, saboda bambancin akida.
Ya ce hanyar da kungiyar Izala ke bi ita ce tattaunawa da jan hankali cikin hikima domin tabbatar da gaskiya, ba amfani da tashin hankali wajen kawar da wadanda suke da fahimta daban ba.
Bayanin Bulama kan Masussuka
A wani labarin, kun ji cewa mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Audu Bulama Bukarti, ya yi karin bayani kan zarge-zargen da tambayoyin da suka biyo bayan wallafa wani sako game da kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka.
Bukarti na cikin mutanen da suka fitar da wani sautin murya da aka danganta wa kungiyar Ansaru, inda kungiyar ta yi ikirarin cewa ita ce ta kashe malamin a kofar gidansa da ke Dutsin-Ma, jihar Katsina.
Lauyan ya musanta zargin cewa shi ne mutum na farko da ya fara fitar da sakon kungiyar, sannan ya nuna mamakinsa kan yadda wasu suka fara alakanta shi da kungiyar Izala.
Asali: Legit.ng




