Bulama Bukarti Ya Yi Bayani kan Sakon da Ansaru Ta Fitar bayan Kashe Sheikh Yahaya Masussuka

Bulama Bukarti Ya Yi Bayani kan Sakon da Ansaru Ta Fitar bayan Kashe Sheikh Yahaya Masussuka

  • Audu Bulama Bukarti ya fito ya yi bayani kan zarge-zarge da tambayoyin da ake masa bayan ya fitar da sakon Ansaru kan kisan Sheikh Yahaya Masussuka
  • Lauyan ya musanta zargin cewa shi ne mutum na farko da ya fara fitar da sakon kungiyar Ansaru, wacce ta ce ita ta kashe malamin
  • Bulama ya kuma yi mamakin yadda wasu suka fara cewa shi dan kungiyar Izala ne shi yasa yake kokarin kare ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lauya mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Audu Bulama Bukarti ya yi karin haske kan zarge-zargen da suka biyo bayan sautin da ya wallafa kan kisan Sheikh Yahaya Ibrahim Masusduka.

Bulama na daya daga cikin mutanen da suka fitar da wani sautin murya da aka ji kungiyar ta'addanci ta Ansaru ta dauki nauyin kashe malamin a kofar gidansa da ke Dutsin-Ma a Katsina.

Kara karanta wannan

Ziyarar Hannatu Musawa ofishin uban ‘ya ‘yanta, Abdussamad ya dawo da batun aure

Bulama Bukarti.
Lauya mai sharhi kan harkokin tsaro a Najeriya, Audu Bulama Bukarti Hoto: Audu Bulama Bukarti
Source: Facebook

A wani faifan bidiyo da wallafa a shafinsa na Facebook, Bulama Bukarti ya nuna damuwarsa kan yadda wasu suka rika sukarsa bayan ya saki sautin muryar.

Bulama ne ya fara wallafa sakon Ansaru?

Sai dai ya bayyana cewa tambayoyi uku da aka rika yi ne suka ja hankalinsa ya fito ya yi bayani domin ba da amsa kan lamarin wanda ya shafi kisan Sheikh Masussuka.

Bulama Bukarti ya ce mutane sun rika tambayar a ina ya samo wannan sako na kungiyar Ansaru, wasu ma na cewa shi ne kadai a duniya ya fitar da sautin murya.

Lauyan ya musanta wannan zargi, yana mai cewa ba shi ya fara fitar da labarin cewa Ansaru ce ta kashe Sheikh Yahaya Masussuka ba.

Bulama ya ce:

"Ba ni na fara ganin wannan sako ba, ba nine na farko ba, kuma ba ni ne mutum na biyu ba, sai da aka wallafa wannan sako da sama da sa'o'i biyu sannan ni ma na wallafa shi.

Kara karanta wannan

An bayyana irin manyan makaman da Najeriya za ta fara kerawa

"Mutum na farko da ya fara wallafa sakon da Ansaru ta ce ita ta kashe Masussuka sunansa Vincent, masani ne a kan harkar Boko Haram, ya fitar da sakon karfe 10:42.
"Na san shi sama da tsawon shekara biyar, da naga ya wallafa na masa sako ta Twitter na nemi ya turo mini. Shi ba ma dan Najeriya ba ne, ina jin Bature ne amma mun dade tare, ya yi hira da tsofaffin yan Boko Haram sama da 200."

Bulama ya kara da cewa mutum na biyu da ya fitar da sakon kungiyar Ansaru shi ne Malik Samuel, wanda shi ma masani ne mai bincike kan harkokin kungiyar Boko Haram.

Bulama ya musanta zargin kare Izala

Ya ce sai bayan wadannan mutane sun fitar da wannan sako ne sannan ya nema, ya yi na shi binciken daga bisani ya wallafa a shafinsa.

Bukarti.
Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka a gefen hagu da lauya mai sharhi kan harkokin tsaro, Audu Bulama Bukarti a gefen dama Hoto: Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, Audu Bulama Bukarti
Source: Facebook

Lauyan ya kuma musanta cewa shi dan kungiyar Izala ne, yana mai tuna wa mutake yadda aka rika zaginsa bisa zargin cewa shi ya sa Dan Bello ya taba shugaban Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Kara karanta wannan

Bincike ya tono matsala a N37bn da aka ce gwamnatin Tinubu da Buhari sun raba wa talakawa

Ya kuma karyata zargin cewa yana da alaka da kungiyar Ansaru, inda wasu suka ce shi ne mai magana da yawunta.

Ansarau ta dauki nauyin kisan Masussuka

Kun ji cewa kungiyar Ansaru mai alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kashe Malam Yahaya Masussuka, wanda aka harbe har lahira a Dutsin-Ma ta jihar Katsina a ranar Litinin

A cikin wani saƙon murya, ƙungiyar ta zargi malamin da kafirci da adawa da Musulunci, amma ba ta bayyana wani takamaiman laifi da ya aikata ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262