Matakai 5 da za a Bi a Samu Rancen N100m na Tinubu domin Sayen Gida
- ’Yan Najeriya za su iya neman bashin sayen gida har Naira miliyan 100 karkashin shirin rancen kudi na MOFI Fund na gwamnatin tarayya
- An bayyana cewa shirin na bayar da bashin ne kan kudin ruwa na kashi 9.75 a shekara, tare da wa’adin biya har zuwa shekaru 20
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce masu neman bashin za su iya fara da biyan kashi 10 na kudin gidan da suke son saya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta samar da damar da ’yan Najeriya za su iya karbar bashin sayen gida har Naira miliyan 100 karkashin shirin MREIF.
Shugaba Bola Tinubu ne ya sanar da shirin a matsayin wani bangare na kokarin gwamnatinsa na saukaka wa ’yan Najeriya mallakar gidaje.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa shirin na bayar da bashin ne kan kudin ruwa na kashi 9.75 a duk shekara, tare da damar biyan bashin cikin shekaru 20.
Tinubu ya bayyana cewa mai neman bashin zai iya fara da kashi 10 na kudin gidan. Misali, idan mutum yana son sayen gida na Naira miliyan 10, zai biya Naira miliyan 1 a matsayin kudin farko, sannan ya rika biyan sauran a hankali.
Ga yadda za a nemi bashin:
1. Tabbatar da cewa ka cika sharuda
An bayyana cewa dole ne mai neman bashin ya kasance dan Najeriya, kuma shekarunsa ba su gaza 21 ba.
Haka kuma, dole ne ya kasance yana da karfin biyan bashin kafin ya kai shekara 60 ko shekarun ritayar da suka dace da shi.
Masu neman bashin za su kuma bukaci cika sharudan samun kudin shiga da tarihin bashi, tare da samun damar biyan kaso na farko da aka kayyade, wanda zai fara daga kashi 10% na kudin gidan.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Najeriya za ta fito da hatsin da aka adana saboda karya farashin kayan abinci
Masu sha’awar shirin za su iya amfani da na’urar lissafin kudin da za su iya biya da ke shafin MREIF domin tantance adadin bashin da ya dace da karfinsu.
2. Ziyartar shafin intanet na shirin
Masu sha’awar neman bashin za su iya fara rajista ta shafin intanet na shirin, wato www.mreif.com.ng, ko kuma shafin neman gidaje na housing.mreif.com.ng/pre-qualifier.
A shafin, za su iya amfani da na’urar tantance cancanta ta hanyar shigar da bayanai kamar shekarunsu, matsayin aikinsu, kudin shigarsu na wata-wata, kudin farko da za su iya biya da kuma tsawon lokacin da suke son dauka wajen biyan bashin.
Sai dai cike bayanan tantance cancanta ba yana nufin an amince da bayar da bashin ba, domin bankin da zai kula da neman bashin zai sake tantance karfin mai nema.
3. Za a zabi gidan da ake son
Bayan tantance cancantarsu, masu neman bashin za su iya duba gidajen da ake da su a shafin ko kuma su zabi gidan da suke son saya.
Dole ne gidan ya cika sharudan shirin, sannan ya kasance yana da takardun mallaka da hukumomin da abin ya shafa suka amince da su.
Takardun da ake bukata sun hada da:
- Ingantacciyar takardar shaida.
- Takardar daukar aiki ko tabbatar da aiki.
- Takardar albashi ta watanni shida ga ma’aikata.
- Kudin wutar lantarki ko ruwa na baya-bayan nan.
- Takardar haihuwa ko shaidar shekaru.
- Takardar biyan haraji ko katin haraji.
- Bayanin asusun ajiyar fansho ga wadanda abin ya shafa.
- Takardar tayin sayen gida da takardun mallakar gidan.
Bankuna na iya neman karin takardu, ciki har da bayanan asusun banki da rahoton tarihin bashi, gwargwadon yanayin mai neman bashin.
4. Mika takardun neman bashin
Bayan kammala tantance cancanta da zabar gidan da ake son saya, mai neman bashin zai mika bukatarsa tare da dukkan takardun da ake bukata ta hanyoyin da MREIF ta tanada.
Za a duba kudin shigarsa, tarihin bashi, karfin biyan bashin da kuma ingancin takardun mallakar gidan.

Source: Facebook
5. Za a nemi bashin ta bankuna
MREIF na aiki tare da bankunan kasuwanci da bankunan lamunin gidaje domin bayar da bashin.
Bankunan da ke cikin shirin sun hada da Access, FirstBank, FCMB, Globus, Providus, Stanbic IBTC, Union da Wema.
Haka kuma, akwai Abbey Mortgage Bank, AG Mortgage Bank,, Gateway Mortgage Bank, Homebase Mortgage Bank, Imperial Homes Mortgage Bank, Infinity Trust Mortgage Bank, LivingTrust Mortgage Bank, LBIC Mortgage Bankers da Nigeria Police Mortgage Bank.
Ana bukatar masu neman bashin su tabbatar da cewa bankin da suka zaba yana karbar bukatun neman bashin MREIF a halin yanzu.
Za a ba da tallafin N100,000
A wani labarin, mun rahoto cewa shirin tallafin NFSP na bayar da N100,000 ga iyalai matalauta da masu rauni domin rage musu nauyin tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki.
Gwamnati na amfani da tsarin NSSTS da lambar shaidar dan kasa ta NIN wajen tantance wadanda suka cancanci tallafin, tare da kauce wa maimaita sunayen wadanda suka riga suka amfana.
Masu sha’awar shiga shirin za su iya yin rajista ta shafin intanet da aka samar, amma cike fom ba ya tabbatar da cewa za su samu tallafin kai tsaye.
Asali: Legit.ng


