Hadarin Jirgin Ruwan da aka yi a Najeriya Ya Shafi Kamfen Din APC na 2027

Hadarin Jirgin Ruwan da aka yi a Najeriya Ya Shafi Kamfen Din APC na 2027

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa kan mutanen da suka mutu bayan wani kwale-kwale dauke da fasinjoji da dama ya kife a jihar Bayelsa
  • Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Ukubie, kusa da Oweikorogha, da ke karamar hukumar Ijaw ta Kudu
  • Tinubu ya umurci hukumomin agajin gaggawa na tarayya da su hada kai domin tabbatar da nasarar aikin ceto da kuma gano wadanda suka bata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jimamin mutanen da suka rasa rayukansu bayan wani kwale-kwale dauke da fasinjoji da dama ya kife a jihar Bayelsa.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Ukubie, kusa da al’ummar Oweikorogha, da ke karamar hukumar Southern Ijaw ta jihar.

Kara karanta wannan

An gwabza rikici tsakanin sojoji da jama'a a Lawanti da ke Gombe

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A cewar sanarwar fadar shugaban kasa da mai ba Tinubu shawara kan yada labarai, Sunda Dare, ya fitar a X a ranar 21 ga Nuwamba, 2026, wadanda suka mutu na cikin masu makoki da ke tafiya domin halartar jana’iza a yankin.

Tinubu a ceto mutanen

Shugaban kasar ya bayyana bakin cikinsa kan wannan mummunan lamari, yana mai cewa mutanen da suka rasa rayukansu ba su cancanci mutuwa ta irin wannan hanya ba.

Tinubu ya ce ya bayar da umarnin dukkan hukumomin agajin gaggawa na tarayya da abin ya shafa su hada kai domin tabbatar da gudanar da aikin ceto da gano wadanda suka bata cikin nasara.

Shugaban kasar ya kuma yi addu’ar Allah ya ji kan wadanda suka mutu, ya ba iyalansu hakurin jure wannan babban rashi.

Lamarin ya shafi taron APC

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa ya bayar da umarnin a gudanar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a Ibadan, jihar Oyo, ranar Asabar, 21 ga Nuwamba, 2026, ba tare da shagali mai yawa ba.

Kara karanta wannan

Muhimmin tarihi da Tinubu ya kafa game da yaki da ta'addanci a Najeriya

Ya ce an dauki matakin ne domin girmama wadanda suka mutu da kuma nuna tausayawa ga iyalansu da sauran wadanda lamarin ya shafa.

Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, gwamnatin jihar Bayelsa da daukacin al’ummar jihar.

Tinubu ya jajanta wa Gwamna Diri

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa yana tare da Gwamna Douye Diri na Bayelsa a wannan lokaci na bakin ciki.

A cikin sakon ta’aziyyar, Tinubu ya ce a madadin daukacin ’yan Najeriya, yana jimamin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin.

Gwamna Douye Diri
Gwamnan Bayelsa, Douye Diri. Hoto: Bayelsa State Government
Source: Twitter

Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikansu, ya kuma kwantar wa iyalansu da sauran wadanda suka shiga cikin wannan mummunan lamari hankali.

An zargi dan Bello da tallata Tinubu

A wani labarin, mun rahoto cewa tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya yi tsokaci kan zargin cewa Dan Bello da Sharafadeen Bature sun taka rawa wajen tallata Shugaba Bola Tinubu.

Dalung ya nuna damuwa kan yadda wasu masu sukar gwamnatin Tinubu a kafafen sada zumunta ke da alaka da mutanen da suke goyon bayan gwamnatin.

Tsohon ministan ya bukaci Dan Bello da Sharafadeen Bature su yi wa mabiyansu karin bayani kan irin alakar siyasar da suke da ita da APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng