Bayan Birne Masussuka, Dubban Mabiyansa Sun Yi Taron Zaman Lafiya

Bayan Birne Masussuka, Dubban Mabiyansa Sun Yi Taron Zaman Lafiya

  • Dubban mabiya marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka da malaman addinai sun halarci taron zaman lafiya na farko a Katsina
  • An shirya taron ne domin inganta zaman lafiya da hakuri tsakanin mabiya addinai daban-daban, duk da kashe Sheikh Masussuka a gidansa
  • Malaman addinai sun yi kira ga mabiyansa su kwantar da hankalinsu, tare da neman hukumomi su gano wadanda suka kashe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Katsina - Dubban mabiya marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka da malaman addinai daga sassan Najeriya da wasu kasashen Afirka sun halarci wani babban taro a Katsina.

An gudanar da taron zaman lafiya na addinai karo na farko a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina ranar Asabar.

Masoyan Masussuka sun yi taron zaman lafiya a Katsina
Manyan malamai da mutane daga ketare sun halarci taron zaman lafiya a Katsina. Hoto: Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka.
Source: Facebook

Wakilin Legit Hausa ya samu wannan bayani ne daga shafin marigayin wanda aka wallafa a Facebook a yau Asabar.

Kara karanta wannan

Jagora a Izala ya yi magana game da kashe Sheikh Masussuka

Shirin da Masussuka ya fara na taron

Marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka ne ya fara tunanin shirya taron, amma wasu 'yan bindiga sun harbe shi har lahira a gidansa.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Dutsin-Ma da ke jihar Katsina a ranar Litinin din makon da ya gabata.

Kungiyar Quranic Believers Harmony for Peace Initiative ce ta shirya taron domin cika burin marigayin.

A jawabin maraba, sakataren kungiyar, Dakta Mustapha Haruna, ya ce an shirya taron ne domin karfafa hakuri da juna tsakanin mabiya addinai.

Ya bayyana cewa manufar ita ce tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin kungiyoyin addinai daban-daban a Najeriya da Afirka baki daya.

Haruna ya ce rasuwar Sheikh Masussuka, wanda ya assasa wannan shiri, babban koma baya ne ga kokarin samar da zaman lafiya.

Sai dai ya ce kungiyar ta ga ya dace ta ci gaba da gudanar da taron domin cika burin marigayin.

Kara karanta wannan

Malamin Izala ya hango fitina a kashe Sheikh Yahaya Masussuka da aka yi

Ya kara da cewa yana da muhimmanci a girmama burin marigayin ta hanyar gudanar da wannan shiri da ya fara.

Shugaban Kiristoci a Katsina ya magantu

Shi ma shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a Katsina, Fasto Richard Sha'aibu Liti, ya bayyana taron a matsayin wani muhimmin tarihi.

Ya ce shirin zai taimaka wajen magance rashin hakuri tsakanin mabiya addinai da karfafa zaman lafiya domin samar da Najeriya mai inganci.

Fasto Liti ya bayyana cewa mutane daga addinai daban-daban za su ci gaba da tallafa wa wannan shiri a fadin kasar.

Ya jaddada cewa kokarin ba zai zama a banza ba, domin taron zai zama abin alfahari da za a ci gaba da tunawa da shi.

Sheikh Nuru Khalid ya halarci taron marigayi Masussuka
Babban malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Muhammad Nuru Khalid. Hoto: Sheikh Muhammad Nuru Khalid.
Source: Facebook

Martanin Sheikh Nuru Khalid

Haka kuma, Sheikh Muhammad Nuru Khalid daga Abuja, wanda aka fi sani da Digital Imam, ya ce kokarin marigayin zai kasance abin tunawa.

Ya ce ayyukan Sheikh Masussuka na inganta hakuri da juna da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai za su kasance gadon tarihinsa.

Sheikh Khalid ya bayyana cewa kashe malamin ba zai dakatar da wannan yunkuri na samar da zaman lafiya ba.

Kara karanta wannan

An farmaki yan APC yayin da Gwamna Radda ya kaddamar da kamfen a Katsina

Ya bukaci mabiyansa su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da addu'o'in zaman lafiyar Najeriya tare da yada manufofin da marigayin ya tsaya a kai.

Malamin addinin Musulunci ya kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar an gano wadanda suka kashe Sheikh Masussuka.

Ya bukaci a gurfanar da wadanda aka samu da hannu a kisan a gaban kotu domin su fuskanci hukunci.

Taron ya samu halartar fitattun malaman addinai da wasu manyan mutane daga sassa daban-daban na kasar nan.

Daga cikin wadanda suka halarta akwai tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Selcap Dalung, wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Masussuka: Malamin Izala ya magantu

A wani labarin, an ji cewa babban limamin JIBWIS a Abuja, Imam Ibrahim Aliyu Kaduna, ya ce suna adawa da akidar marigayi Sheikh Yahaya Masussuka saboda kin amincewa da Hadisi.

Limamin ya bayyana cewa Musulunci ba zai cika ba tare da bin Sunnar Annabi ba, domin ita ce ke karin bayani kan umarnin da ke cikin Alkur’ani.

Sai malamin ya yi Allah-wadai da kashe Masussuka, yana mai cewa bai kamata a kashe mutum saboda bambancin akida ko fahimtar addini ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.