Sarkin Musulmi Ya Cika Shekara 20 a kan Karagar Mulki
- Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya taya Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, murnar cika shekaru 20 yana kan karagar mulkin masarautar Sakoto
- Bago ya bayyana Sarkin Musulmin a matsayin shugaba mai tawali'u, haƙuri da tausayi, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa addinin Musulunci da ci gaban al'umma
- Haka kuma, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya taya Sarkin Musulmin murna, inda ya yaba da gudummawar da yake bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto – Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, sun taya Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III, murnar cika shekaru 20 a kan karagar mulkin masarautar Sakoto.
Gwamna Bago ya bayyana hakan ne a cikin saƙon taya murna da ya fitar, inda ya yaba da irin jagorancin da Sarkin Musulmin ke bayarwa tun bayan hawansa karagar mulki.

Source: Facebook
A sakon da hadimin gwamna Bago, Balogi Ibrahim ya wallafa a Facebook ya ce mulkin Sarkin Musulmin ya kasance mai cike da sadaukarwa, haƙuri da tausayi, tare da fifita haɗin kan al'umma da zaman lafiya.
Bago ya yabi Sarkin Musulmi
Gwamna Bago ya bayyana Sarkin Musulmin a matsayin mutum mai tawali'u, jajircewa da ƙwazo, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yaɗa Musulunci da bunƙasa shi.
Ya ce Sarkin Musulmin ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban, tare da ƙarfafa zaman lafiya tsakanin Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba.
A cikin saƙon taya murnar, wanda babban sakataren yaɗa labaransa, Bologi Ibrahim, ya fitar a ranar 1 ga watan Nuwamba, Bago ya ce:
"Ina miƙa babbar taya murna ga Mai Martaba, shugabanmu, bisa cika shekaru 20 a matsayin Sarkin Musulmi.
"Kun bayar da gudummawa mai matuƙar muhimmanci ga Musulunci, masarautun gargajiya da ci gaban ƙasa, wadda ba za a iya yin watsi da ita ba."
Gwamnan ya roƙi Allah Ya ƙara wa Sarkin Musulmin lafiya, hikima da basira domin ci gaba da jagorantar al'ummar Musulmi.
Pantami ya taya sultan murna
A nasa saƙon, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya taya Sarkin Musulmin murnar cika shekaru 20 a kan karagar mulki, inda ya bayyana shekarun mulkinsa a matsayin na hikima, tawali'u da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya.
Pantami, wanda ke riƙe da sarautar Majidadin Daular Usmaniyya, ya wallafa a Facebook cewa Sarkin Musulmin ya bayar da gagarumar gudummawa wajen inganta ilimi, haɗin kan ƙasa da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai.

Source: Facebook
Ya kuma yaba da yadda Sarkin Musulmin ke jagorantar al'umma cikin tausayi, taimakon marasa galihu da kuma ƙarfafa fahimtar juna tsakanin mutane.
Sarkin ya yi naɗin sarauta
A wani labarin, mun ruwaito cewa Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar III, ya naɗa wasu mutane fitattu sarautun gargajiya a masarautar Sakoto, ciki har da 'ya'yansa biyu.
An naɗa Abubakar Sadiq Abubakar a matsayin Sarkin Dawaki Tsakar Gida, yayin da aka naɗa Shehu Usman Abubakar a matsayin Fagacin Sakkwato.
Sauran waɗanda aka naɗa sarautun sun haɗa da Alhaji Murtala Abdulkadir Dan'iya, wanda ya zama Dallatun Sakoto, da Farfesa Mansur Ibrahim a matsayin Danmasanin Sakkwato.
Asali: Legit.ng

