Hatsarin jirgin soji: NAF ta bayyana dalilin da yasa aka kyale kananan matuka suna jigila da COAS da sauransu
- Rundunar Sojin sama ta Najeriya ta ce ana bincike game da hatsarin jirgin da ya kashe tsohon COAS, Ibrahim Attahiru da wasu mutane 10 a ranar Juma’a, 21 ga Mayu
- Daraktan hulda da jama'a da bayanai na NAF, Air Commodore, Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 28 ga watan Mayu
- Gabkwet, ya karyata rahoton cewa matasan matukan jirgin da suka tuka Attahiru da sauran jami'ai basu da cancanta da kwarewar da ake bukata
Kusan mako guda bayan hatsarin jirgin sama da ya kashe tsohon Shugaban Hafsun Sojoji (COAS), Ibrahim Attahiru da wasu hafsoshin soja 10 a ranar Juma’a, 21 ga Mayu, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta mayar da martani game da takaddama da ta shafi shekarun matukin jirgin.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa NAF ta ce bai kamata a tuhumi karfin matukan jirginta ba duk da hatsarin jirgin NAF din da ya gabata a kasar.
KU KARANTA KUMA: Waiwaye: Hoton Shugaba Buhari yana rawa da wata mace ya haifar da cece kuce
Legit.ng ta tattaro cewa wani jirgin NAF Beechcraft King Air 350i ya yi hadari a filin jirgin saman Kaduna, bayan matukin jirgin ya karkata daga filin jirgin soji saboda rashin kyawun yanayi.
Jaridar The Cable ta kuma rahoto cewa daraktan hulda da jama'a da bayanai na NAF, Air Commodore, Edward Gabkwet, ya ce kyaftin din jirgin wanda ya tuka jirgin sojin da yayi hatsarin, Taiwo Asaniyi, ya kasance Laftana wanda ya tashi jirgi na dubban sa’o’i.
Matasan matukan jirgin suna da cancantar tuka shugabannin sojoji ciki har da shugaban ƙasa
Ya ce marigayi matukin jirgin da wasu abokan aikinsa, ciki har da matukin jirgin da ke tuka shugaban, sun kasance suna tashi tun suna dalibai a makarantar horas da sojoji ta Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Jam'iyar APC ta dakatar da Hon. Muhammad Gudaji Kazaure
A cewarsa, cancantar matukan jirgin da kwarewar su bai kamata a dasa masu ayar tambaya ba, ya kara da cewa mafi yawansu sun tashi na tsawon sa’o’i fiye da wasu manya da yawa.
Gabkwet ya ce:
A kan mutanen da ke cewa wani babban jami’i ne ya kamata ya tuka Shugaban Hafsun Sojin da sauransu, mutane ba su san shi ba (kyaftin din jirgin da ya fadi). Shi da matukin jirgin da ke jigilar Shugaban kasar dukkansu Laftana ne na Jirgin Sama. Ya tashi tsawon awowi fiye da wasun mu. Ya kasance yana ta shawagi tun daga lokacin da yake makarantar horar da sojoji ta Najeriya. Ya fara tashi ne a matsayin cadet.
A matsayinsa na kaftin a jirgin Beechcraft, ya yi tafiyar awa 2,450, wanda ya kasance a cikin shekarar 2019. Don haka bai tuka kasa da awanni 5,000 ba tun lokacin da ya fara karatunsa. Ya kasance yana tuka COAS da sauran Manya a cikin wannan Beechcraft din. Yana da shekaru 29. Saboda yayi hatsari baya nufin bashi da kwarewa.
Ya ce matukin jirgin yana tafiya duk shekara don sake samun horo, ya kara da cewa horon ya kunshi na hadin gwiwa da masu kera jiragen.
Har ila yau, Gabkwet ya musanta jita-jitar cewa jiragen da ke NAF sun tsufa, yana mai lura da cewa jirgin da yayi hatsari na Beechcraft na daya daga cikin mafi kyau a duniya, yana mai cewa an sayi jiragen ne sabbu fil kimanin shekaru shida da suka gabata.
An fara bincike kan hatsarin jirgin
Ya kuma ce an fara gudanar da bincike kan hatsarin tare da hadin gwiwar Ofishin Binciken Hadarin, kuma za a dawo da bayanai daga bakin akwati.
A wani labarin, tawagar yan majalisar dokokin Najeriya sun kai ziyara kasar Amurka domin ganewa idanwansu sabbin jiragen yaki na A-29 Super Tucano da gwamnatin Najeriya tayi oda tun 2018.
A Febrairun 2018, shugaba Muhammadu Buhari ya bada kudi $469.4 million don sayan jirage Tucano guda 12 domin yaki da yan ta'adda.
Yan majalisar da wasu jami'an hukumar mayakan sama sun kai ziyara kamfanin ne domin ganin yadda ayyuka ke gudana kan odan da Najeriya tayi.
Asali: Legit.ng