An Sanya Sabuwar Doka kan Daliban da Suka Kammala Karatu a Jami'ar BUK da ke Kano

An Sanya Sabuwar Doka kan Daliban da Suka Kammala Karatu a Jami'ar BUK da ke Kano

  • Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta haramta wa ɗaliban da suka kammala karatu yin bikin bankwana a harabar makaranta
  • Jami’ar ta kuma hana amfani da rigunan yaye dalibai wajen ɗaukar hotuna ko gudanar da bukukuwan da ba ta amince da su ba
  • BUK ta yi gargaɗin cewa za ta hukunta duk ɗalibin da ya karya dokar, yayin da jami’an tsaro za su kama masu bijirewa umarnin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta haramta wa ɗalibai gudanar da bukukuwan bankwana na kammala karatunda kuma amfani da rigunan yaye dalibai ba tare da izini ba a harabar jami’ar.

Mai magana da yawun jami’ar, Lamara Garba, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Premium Times ta rahoto sanarwar na cewa:

Kara karanta wannan

Ciyaman a Kano ya ballo ruwa, ya yi barazana ga jama'a kan zaben APC a 2027

“Hukumar gudanarwa ta BUK ta lura cikin damuwa da yadda ake samun ƙaruwar ɗaliban da suka kammala karatu da ke gudanar da bukukuwan ‘signing-out’ a harabar makaranta.
“Saboda haka, an haramta duk wani nau’in bikin bankwana da ake gudanarwa a harabar jami’ar nan take.
“Wannan ya haɗa da sanya tufafin da aka lalata; amfani da fenti, tawada ko alkalaman rubutu a jiki ko kan kadarorin jami’ar; tayar da tarzoma a bainar jama’a; da duk wani abu makamancin haka da ake yi da sunan murnar kammala karatu.

Jami’ar ta kuma ce: ann haramta amfani da rigunan yaye dalibai ko wasu tufafi na musamman da ɗaliban da suka kammala karatu ke yi domin ɗaukar hotuna ko gudanar da bukukuwan da jami’a ba ta amince da su ba a harabar makaranta.

"Hukumar makaranta na tanadar da rigunan yaye dalibai ne kawai domin bukukuwan jami’a na yaye dalibai, wadanda aka amince da su," in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa za a hukunta duk ɗalibi ko ƙungiyar ɗalibai da aka samu suna gudanar da ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa bisa dokoki da ƙa’idojin jami’ar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kafa tarihi a Najeriya, ya kafa jami'a irinta ta farko a duniya

“An tunatar da ɗalibai cewa Jami’ar Bayero tana bayar da digiri ne ga waɗanda aka tabbatar sun cancanta ta fuskar ɗabi’a da ilimi. Saboda haka, ana sa ran duk ɗaliban da suka kammala karatu za su nuna halin da zai kare mutunci da martabar jami’ar.

“An umarci jami’an tsaro da su tabbatar da bin wannan umarni yadda ya kamata tare da kama duk wanda ya karya shi. Ta wannan sanarwa, ana shawartar dukkan ɗalibai da su kiyaye wannan umarni,” in ji shugabancin jami’ar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262