Jerin hatsarurrukan jiragen saman soji da aka yi a Najeriya a cikin 2021

Jerin hatsarurrukan jiragen saman soji da aka yi a Najeriya a cikin 2021

Shekarar 2021 ta kasance tattare da kalubale musamman ga Najeriya yayin da kasar ta fuskanci hadurran jiragen sama da dama wadanda suka yi sanadiyar rayukan mutane da dama.

Daga abin da ya faru a Abuja zuwa na baya-bayan nan a Zamfara, rundunar sojan Najeriya ta samu akalla hatsarin jirgin sama hudu a 2021.

Jerin hatsarurrukan jiragen saman soji da aka yi a Najeriya a cikin 2021
Wani jirgin saman sojojin saman Najeriya wanda aka dauki hotonsa yayin da sojojin Najeriya ke shirin barin Kaduna zuwa Mali a ranar 17 ga Janairun, 2013 Hoto: Victor Ulasi/AFP
Asali: Getty Images

1. Hadarin jirgin saman soja kusa da Abuja

A ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairu, jirgin sojojin sama na Najeriya (NAF) na King Air 350 ya yi hadari kusa da Abuja, inda jami’ai bakwai da ke jirgin suka rasa rayukansu.

A cewar Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, jirgin ya fado ne jim kadan bayan ya bayar da rahoton gazawar injin.

2. NAF475 ya sauka daga hanya

A ranar Laraba, 31 ga watan Maris, jirgin NAF475 na rundunar Sojan Sama ta Najeriya ya sauka daga kan hanya.

Jirgin wanda ke dauke da jami'ai biyu a ciki yana a hanyarsa ta zuwa jihar Borno ne don taimaka wa sojoji da ke yaki da 'yan ta'addan Boko Haram. Jami’an NAF biyu da ke cikin jirgin sun mutu.

Kara karanta wannan

Labari mai zafi: Hatsarin mota ya hallaka mutane da dama a hanyar zuwa Minna

3. Hadarin jirgin Kaduna

A ranar Juma’a, 21 ga watan Mayu, wani jirgin sojan Najeriya ya yi hadari a jihar Kaduna, inda ya kashe shugaban hafsan sojan kasar (COAS), Ibrahim Attahiru, da wasu hafsoshin soja 10.

Suna kan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja lokacin da mummunan lamarin ya faru.

4. Hadarin jirgin sama a Zamfara

Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) a ranar Litinin, 19 ga watan Yuli, ta tabbatar da cewa daya daga cikin jirginta ya fado a yayin da ya ke dawowa daga wani aiki mai cike da nasara a jihar Zamfara.

Air Commodore Edward Gabkwet, daraktan hulda da jama’a na NAF, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya aike wa Legit.ng.

A cewar kakakin, da misalin karfe 12.45 na ranar Lahadi, 18 ga watan Yuli, wani jirgin soji ya gamu da mummunar harin abokan gaba sakamakon aikin da ya yi tsakanin iyakar Zamfara da jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Manyan shugabannin PDP sun sauya sheka zuwa APC, an saki sunayensu

Abin farin ciki, matukin jirgin, Laftanar Abayomi Dairo, ya rayu bayan ya samu nasarar fitar da kansa daga jirgin.

A shekarar 2021 kadai, rundunar sojan Najeriya ta rasa hafsoshin soja 20, ciki har da tsohon babban hafsan sojan kasar sakamakon hatsarin jirgin sama.

Hatsarin jirgin soji: NAF ta bayyana dalilin da yasa aka kyale kananan matuka suna jigila da COAS da sauransu

A wani labarin, bayan hatsarin jirgin sama da ya kashe tsohon Shugaban Hafsun Sojoji (COAS), Ibrahim Attahiru da wasu hafsoshin soja 10 a ranar Juma’a, 21 ga Mayu, Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta mayar da martani game da takaddama da ta shafi shekarun matukin jirgin.

Jaridar The Punch ta rahoto cewa NAF ta ce bai kamata a tuhumi karfin matukan jirginta ba duk da hatsarin jirgin NAF din da ya gabata a kasar.

Legit.ng ta tattaro cewa wani jirgin NAF Beechcraft King Air 350i ya yi hadari a filin jirgin saman Kaduna, bayan matukin jirgin ya karkata daga filin jirgin soji saboda rashin kyawun yanayi.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji sun kama ‘Yan fasa-kauri za su tsallako da buhuna 160 na shinkafa

Asali: Legit.ng

Online view pixel