Hadarin Jirgin Sojoji: Za a Yi Kwana 3 ana Zaman Makoki a Fadin Najeriya

Hadarin Jirgin Sojoji: Za a Yi Kwana 3 ana Zaman Makoki a Fadin Najeriya

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki a Najeriya domin karrama jami'an da suka rasa rayukansu a hadarin jirgin saman sojoji
  • Shugaban kasar ya kuma bayar da umarnin sauke tutocin Najeriya zuwa kasa a fadin kasar yayin zaman makokin domin nuna girmamawa ga wadanda suka mutu
  • An bayyana cewa hadarin ya faru ne a yankin Igbokoda da ke jihar Ondo, yayin da jirgin ke gudanar da wata tafiya ta yau da kullum daga Benin zuwa Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki a fadin Najeriya domin tunawa da jami'an Sojojin Sama da suka rasa rayukansu a hadarin jirgin sama da ya faru a jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Shettima ya dura jihar Katsina, an raba miliyoyin Naira kyauta

Shugaban kasar ya kuma umarci a sauke tutocin Najeriya kasa a fadin kasar a matsayin girmamawa ga wadanda suka mutu.

Hadarin jirgin NAF
Wajen da jirgin Najeriya ya yi hadari. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a X ranar Litinin.

Tinubu ya jajanta wa sojoji

Tinubu ya bayyana alhininsa kan hadarin jirgin saman ATR-42 na Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya, wanda ya faru kusa da wani sansanin sojojin ruwa da ke yankin Igbokoda na jihar Ondo.

Jirgin na dauke da fasinjoji 25 da ma'aikatan jirgi bakwai a lokacin da yake kan wata tafiya ta yau da kullum daga Benin zuwa Legas kafin hadarin ya rutsa da shi.

Daily Trust ta wallafa cewa shugaban kasar ya ce:

"Wannan lokaci ne mai matukar radadi ga dakarunmu da kuma daukacin al'ummar Najeriya. Jami'an Sojojin Sama suna sadaukar da rayukansu a kullum domin kare Najeriya, kuma ba za a taba manta da sadaukarwarsu ba."

Ana binciken dalilin hadarin

Kara karanta wannan

Jirgin rundunar sojojin Najeriya ya yi hatsari, ana fargabar mutane da dama sun mutu

Tinubu ya ce Shugaban Rundunar Sojojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya yi masa bayani kan lamarin.

Ya umarci Rundunar Sojojin Sama da ta fara cikakken bincike kan musabbabin hadarin domin daukar matakan da za su taimaka wajen hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.

Shugaban kasar ya kuma yaba wa rundunar bisa fara aikin neman wadanda suka tsira da ceto nan take bayan hadarin.

A cewar sanarwar fadar shugaban kasa, Rundunar Sojojin Sama za ta fitar da sunayen jami'an da abin ya shafa bayan tuntubar iyalansu.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tinubu ya mika sakon ta'aziyyarsa ga Shugaban Rundunar Sojojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, da dukkan jami'ai da sauran ma'aikatan rundunar.

NAF ta tabbatar da hadarin

A wani labarin, mun ruwaito cewa Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya ta fara aikin neman wadanda suka tsira bayan hadarin jirgin ATR-42 da ya faru a yankin Igbokoda na jihar Ondo.

Daraktan Hulda da Jama'a da Yada Labarai na Rundunar Sojojin Sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce jirgin na kan wata tafiya ta yau da kullum ne daga Benin zuwa Legas lokacin da hadarin ya faru.

Ya ce aikin neman wadanda suka tsira na gudana ne tare da hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa da sauran hukumomin agajin gaggawa, yayin da rundunar ta ce za ta ci gaba da kokarin ganin an kammala aikin cikin nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng