Lauya Ya Shiga Neman Beli da Aka Maka Shugabannin Jam’iyyar ADC a Kotu
- Dr. Bamidele Ekundayo da Ilesanmi Omolayo sun yi rigima saboda neman shugabancin ADC a Ekiti
- Wannan rigima ta jawo ‘yan sanda suka yi karar su a wani kotun majistare mai zama a babban birnin jihar
- Lauya ya yi nasarar samo masu beli kafin a cigaba da sauraron shari’ar a karshen watan Oktoban 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Ekiti - Wasu jagorori biyu na jam’iyyar ADC sun samu kan su a kotu a dalilin rikicin neman shugabanci da suka yi.
An yi karar Dr. Bamidele Ekundayo da wani matashi, Ilesanmi Omolayo a kotun majistare da ke garin Ado Ekiti a jihar Ekiti.

Source: Getty Images
An yi rigima saboda shugabancin ADC a Ekiti
Rahoton Daily Trust ya ce ana zarginsu da yin fada da juna saboda neman kujerar shugaban jam'iyyar ADC na reshen Ekiti.

Kara karanta wannan
Maganar zargin Dickson na shirya wa Obi da Kwankwaso makarkashiya ta yi nisa a NDC
Wanda ya shiga da karar, ASP Akinwale Oriyomi ya fada wa kotu cewa wadannan mutane sun kawo hatsaniya a garin Ado Ekiti.
ASP Oriyomi ya ce Bamidele Ekundayo mai shekaru 71 da Ilesanmi Omolayo sun tada rikicin ne a ranar 2 ga watan Oktoba 2026.
Baya ga su, akwai wasu wadanda ake tuhuma sai dai ba a san ina suka shiga ba zuwa yanzu.
Ya yi wa kotu bayani cewa abin da suka aikata laifi ne a karkashin sassa na 181(1)(d), 69, da 421 na dokokin jihar Ekiti.
Jami’in tsaron ya bukaci alkalin kotun, Abayomi Adeosun ya hukunta su kamar yadda dokokin jihar suka tadana.
Lauya ya samo belin jagororin ADC a kotu
Da ya mike a kotu, lauyan da aka yi haya ya kare ‘yan siyasar, Oluwasola Fapohunda ya roki mai shari’a ya bada belinsu.
Barista Fapohunda ya fada wa alkali cewa wadanda yake ba kariya a gaban kotun ba za su tsere idan sun samu beli ba.

Kara karanta wannan
Rikicin APC a jihar Kano ya fara fitowa, an aika saƙo mara daɗi ga Shugaba Tinubu
Tashar rediyon Trust wanda ita ma ta kawo labarin a ranar Laraba, ta ce an ba da belin Ekundayo da kuma Mista Omolayo.
Sai karshen wata za a koma kotu
Abayomi Adeosun ya bada belin kowanensu ne a kan N100, 000 tare da kawo wani wanda zai tsaya masu a kotu.
A doka, idan har aka samu matsala ko aka neme su aka rasa yayin da ake shari’ar, wanda ya tsaya masu shi zai fito da su.
Daga nan alkalin kotun majistaren ya daga shari’ar har sai zuwa ranar 30 ga watan Oktoba 2026 domin cigaba da sauraron su.
Ba mu da labarin yadda za a yi da sauran wadanda 'yan sanda suke zargin da hannunsa a rikicin siyasar da aka tada a garin.

Source: Getty Images
Alhassan Doguwa ya yi kira a zabi APC
An ji labari Alhassan Ado Doguwa ya roki mutanen Kano su yafe wa gwamnan Kano da shugaban kasa, su zabi APC a 2027.
‘Dan siyasar da ya dade a majalisa ya kawo hujjojin da za su sa a zabi Bola Tinubu a Kano da sauran jihohin Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan
Doguwa ya fito da abubuwa 2 da za su ceci APC daga shan kaye a jihar Kano a zaben 2027
Hon. Doguwa ya fada mabiyansa cewa shugaba Tinubu bai manta da yankin Arewa ba bayan ya gaji Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng