Kotu Ta Raba Gardama kan Tikitin Takarar Mawakin Kwankwasiyya a Kano

Kotu Ta Raba Gardama kan Tikitin Takarar Mawakin Kwankwasiyya a Kano

  • Kotu ta yi watsi da ƙarar Aminu Isyaku Yusuf, wanda ya ƙalubalanci zaɓen Tijjani Gandu a matsayin ɗan takarar NDC
  • Gandu, wanda ya shahara a matsayin mawaƙin siyasar Kwankwasiyya, ya samu damar ci gaba da takararsa ta kujerar majalisar dokokin jihar Kano
  • Har yanzu ba a san ko Aminu Yusuf zai ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara cikin wa'adin da doka ta tanada ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta tabbatar da zaɓen Tijjani Hussaini Gandu, fitaccen mawaƙin siyasar Kwankwasiyya, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar NDC na mazaɓar Kano Municipal a zaɓen majalisar dokokin jihar Kano na 2027.

Mai shari’a Simon Amobeda ne ya yanke hukuncin ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban 2026 a shari'ar wadda mai kalubalantar Tijjani Gandu ya shigar.

Kara karanta wannan

Tsugunne ba ta kare ba; kotu ta dauki mataki kan matsalar auren Gwamna Abba

Tijjani Gandu ya yi nasara a kotu
Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso tare da Tijjani Gandu Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Alkalin kotun ya yi watsi da ƙarar da Aminu Isyaku Yusuf ya shigar domin ƙalubalantar tsayar da Gandu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Dalilin da ya sa aka kai ƙarar kotu

Aminu Isyaku Yusuf ya shigar da ƙarar ne bayan jam’iyyar NDC ta aika sunan Tijjani Gandu ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), wadda daga bisani ta wallafa sunansa a matsayin ɗan takarar mazaɓar Kano Municipal.

A cikin ƙarar, Aminu Yusuf ya haɗa jam’iyyar NDC da INEC a matsayin waɗanda ake ƙara na biyu da na uku.

Ya bayyana cewa shi ma ya sayi fom ɗin takarar jam’iyyar domin neman kujerar, amma maimakon aika sunansa ga INEC, jam’iyyar ta aika da sunan Gandu.

Mai ƙarar ya kuma yi zargin cewa an samu kura-kurai a matakan da aka bi wajen zaɓen Gandu a matsayin ɗan takara.

Saboda haka, ya roƙi kotu ta umarci jam’iyyar da ta aika sunansa ga INEC a matsayin halastaccen ɗan takarar NDC na mazaɓar Kano Municipal a zaɓen majalisar dokokin jihar mai zuwa.

Kara karanta wannan

Tsohon na kusa da Atiku ya zayyano matsalolin dan takarar na ADC a 2027

Kotun ta yi watsi da ƙarar

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Amobeda ya amince da hujjojin lauyan da ya wakilci mawaƙin siyasar Kwankwasiyya, Badamasi Suleiman Gandu, Esq.

Bayan nazarin batun, alkalin ya yi watsi da ƙarar, tare da barin tsayawar Tijjani Gandu a matsayin ɗan takarar NDC ta ci gaba da kasancewa yadda take.

Wannan hukunci ya ba Gandu damar tsallake ƙalubalen shari’a na farko da ya taso kan takararsa ta kujerar majalisar dokokin jihar Kano a 2027.

Sai dai har yanzu ba a san ko Aminu Isyaku Yusuf zai ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara cikin wa’adin da doka ta tanada ba.

Tijjani Gandu ya yi nasara a kotu
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kotu ta soke takarar sanatan APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na APC na kujerar Sanatan Benue ta Arewa maso Gabas.

Tsohon gwamnan ya shigar da ƙarar ne domin ƙalubalantar matakin APC na cire sunansa tare da maye gurbinsa da na Emmanuel Udende, duk da cewa shi ne ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng