Ana Zargin Gwamnatin Najeriya Ta Shiga Yarjejeniyar Sulhu da Boko Haram a Asirce
- Wasu rahotanni sun yi zargin an sasanta da Boko Haram har an biya kudin fansar saki wasu mutane a Borno
- Lamarin ya ta taimaka wajen kubutar da mutane sama da 300 da aka yi garkuwa da su a Ngoshe a kwanaki
- Yarjejeniyar tsagaita wutar ba ta shafi bangaren ISWAP ba, domin su suna ci gaba da kai hare-hare har gobe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ana zargin cewa Gwamnatin Najeriya ta shiga yarjejeniyar tsagaita wuta a boye da wani tsagin Boko Haram.
Idan zancen ya tabbata, Gwamnatin tarayya ta sasanta da tsagin ‘yan kungiyar ta’addan da yake karkashin Bakura Doro.

Source: Getty Images
Boko Haram da Gwamnatin Najeriya sun yi sulhu?
Rahoton da ya fito daga The New Humanitarian ya ce sulhun ya sa an shafe watanni kusan uku babu harin tsagin na Boko Haram.

Kara karanta wannan
Halin da ake ciki da yan sanda suka tabbatar da hari kan ayarin motocin Peter Obi
Yanzu haka Jama’atu Ahlis-Sunna Lidda’awati wal-Jihad (JAS) da aka fi sani da 'yan Boko Haram tana da tsagi akalla uku.
Tsagin kungiyar Boko Haram da ake da su
Bangaren da ke tare da Bakura Doro sun yi karfi a Arewa maso gabas har sun shiga wasu wurare cikin Arewa ta tsakiya.
Bakura Doro shi ya gaji Abubakar Shekau, fitaccen shugaban kungiyar wanda ya mutu wajen fada da ‘yan ISWAP a 2021.
Premium Times ta ce ragowar bangarorin su ne na Ali Ngulde da Alhai Kale sai ‘yan ta’addan da ke bayan Mallam Sadiku.
Shi Doro da mutanensa suna yankin tafkin Chadi ne, sun yi karfi a dalilin rashin karfin jami’an tsaro da ake fama da shi.
Sulhun da aka yi da mayakan Bakura Doro
Wasu majiyoyi sun shaida wa jaridar cewa an sasanta da tsagin Doro tun a watan Yuni, kuma ana sa ran tsawaita sulhun.
Ana ganin sulhun da aka yi a boye ne ya yi sanadiyyar ceto mutane sama da 300 da aka sace a Ngoshe a yankin Gwoza.
An ce Gwamnatin Najeriya ta sasanta da ‘yan ta’addan har ta biya fansar N5bn, sai dai hukumomi sun karyata wannan batu.
Wani jagoran matasa a Borno, Samaila Kaigama yana cikin wadanda suka fara fito wa suna cewa kudi aka biya Boko Haram.
Tuni jami’an DSS suka kama shugaban na kungiyar BOSYA kuma aka gurfanar da shi a gaban kotu.
'Sulhun' zai shafi sauran bangarorin Boko Haram?
Kafin yanzu, an ji rade-radin yadda gwamnati mai-ci ta ke yin sulhu da ‘yan ta’adda, tana biyan kudi domin a kubutar da mutane.
Duk da sasantawar da aka yi da yaran Doro, wannan yarjejeniya ba ta shafi sauran ‘yan ta’addan da ba su karkashinsa ba.
Har gobe sojojin ISWAP suna barna a yankin tafkin chadi idan sun samu dama musamman a yankin Arewa maso gabas.
Sojoji sun yi gum kan zargin sulhu da 'yan ta'adda
Hedikwatar tsaro ta ki yarda ta ce uffan da aka yi mata wannan magana a cewar wani rahoto daga The Guardian.
Birgediya Janar Mike Onoja ya gagara cewa komai da aka bukaci jin matsayar sojoji game da zargin sulhu da miyagun.
An tuntubi babban jami’in ne a matsayin na Darektan labarai na ayyukan sojojin Najeriya.

Source: Getty Images
Wasu sun nemi jin ta bakin Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga, domin tabbatar da gaskiyar zancen amma ba a dace ba.
Sakonnin da aka tura zuwa ofishin Malam Nuhu Ribadu ba su samu amsa ba, haka zalika da aka tuntubi Kakakin sojojin kasa.
Babban ma'aikaci a Aso Rock ya mutu
Bola Ahmed Tinubu ya fitar da ta’aziyyar ma’aikacin Aso Rock da ya mutu a Kano kamar yadda labari ya gabata a farkon makon nan.
Shugaban kasar yana kasar waje, ya nuna alhinin mutuwar kwararren ma’ikacin da ya yi aiki da shugabanni uku a fadar Aso Rock.
Bola Tinubu ya yi maganar rasuwar Peter Onwubuariri ne ta bakin Bayo Onanuga ranar Talata.
Asali: Legit.ng

