Halin da Ake Ciki da Yan Sanda Suka Tabbatar da Hari kan Ayarin Motocin Peter Obi

Halin da Ake Ciki da Yan Sanda Suka Tabbatar da Hari kan Ayarin Motocin Peter Obi

  • Rundunar ’yan sandan jihar Benue ta yi kan harin da aka kai kan ayarin Peter Obi yayin da yake kan hanyarsa zuwa Yelwata
  • ’Yan sanda sun ce har yanzu ba a gano dalilin matasan suka tare ayarin Obi ba, yayin da aka fara bincike domin gano cikakken bayani
  • Jam’iyyar NDC ta zargi APC da shirya matasan, yayin da ita kuma ta musanta zargin, tana cewa ba ta da hannu cikin lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Benue - Rundunar ’yan sandan Benue ta tabbatar da cewa an kai wa ayarin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, hari a hanyar Gboko-Makurdi.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata, yayin da Obi yake kan hanyarsa zuwa Yelwata da ke ƙaramar hukumar Guma domin ziyartar waɗanda harin ya shafa.

Kara karanta wannan

'Neman fitina yake yi': Gwamnatin Benue ta yi martani mai zafi bayan jifan Peter Obi

Matasa sun ai wa Obi hari a Benue
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Facebook

Peter Obi: Yan sanda sun yi martani

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Peter Orchia Aondongu, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa ’yan sanda sun samar da tsaro, cewar Leadership.

Sai dai rundunar ta ce ba a san dalilin da ya sa wasu matasa suka tare ayarin Obi ba, tana mai cewa an fara bincike.

Ya ce jami’an tsaro sun raka Obi yayin tafiyarsa zuwa Yelwata, amma har yanzu ba a gano dalilin da ya sa matasan suka tare ayarin ba.

Rundunar ta bayyana cewa za ta fitar da ƙarin bayani yayin da ake samun sabon ci gaba game da binciken lamarin.

A baya, an ruwaito cewa ɗimbin matasa sun tare ayarin Obi a hanyar Gboko-Makurdi, lamarin da ya hana shi ci gaba zuwa Yelwata.

Obi ya je Makurdi, babban birnin Benue, da safiyar Talata, inda yake shirin zuwa Yelwata domin jajanta wa waɗanda harin ta’addancin ya shafa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya dauki zafi bayan an yi wa Peter Obi ruwan duwatsu a Benue

Yan sanda sun magantu game da hari kan Obi
Taswirar jihar Benue da ke Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Zargin da NDC ke yi a Benue

Sakataren yaɗa labarai na NDC a Benue, Agile Bem Ordedoo, ya zargi APC da tattara matasan domin hana Obi shiga Yelwata.

Ordedoo ya ce dubban ’yan daba ne aka tattara suka tare ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, yayin da yake kokarin shiga Yelwata.

Ya bayyana cewa Obi ya shirya ziyartar waɗanda harin ya shafa tare da kai musu kayan agaji masu darajar biliyoyin naira.

Martanin APC kan zargin ta da ake yi

Sai dai APC ta musanta zargin, tana mai cewa ba ta da masaniya kan lamarin kuma ba za ta shiga harkar daba ba.

Sakataren yaɗa labarai na APC a Benue, Benedict Yaweh, ya ce ba su da masaniya kan harin idan da gaske an kai masa a Makurdi.

Ya ce idan har an kai wa Obi hari, akwai yiwuwar wasu magoya bayansa da ba su ji daɗi ne suka aikata hakan, ba ’yan APC ba.

Kara karanta wannan

An yi ta jifan Peter Obi da magoya bayansa yayin ziyarar ta'aziyya a Benue

Peter Obi: Gwamnatin Benue ta yi martani

An ji cewa Gwamnatin Benue ta zargi Peter Obi da neman tayar da hankali, bayan da aka toshe ayarin motocinsa yayin ziyararsa jihar a ranar Talata.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Solomon Iorpev, ya ce Obi bai sanar da gwamnatin jihar a hukumance kafin ziyarar ba, wanda ya saba ka’idojin aiki.

Iorpev ya ce ba a san mutanen da suka toshe ayarin ba, yana mai cewa ziyarar Obi ta zo daidai da taron matasan ƙananan hukumomi 23.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.