Boko Haram: Shekau ya musanta rade-raden zai mika wuya, ya bada sharuddan sulhu

Boko Haram: Shekau ya musanta rade-raden zai mika wuya, ya bada sharuddan sulhu

Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Jama’tu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad wacce aka fi sani da Boko Haram, ya musanta rade-radin mika wuya da aka ce zai yi.

Ya ce gaba da gaba da dakarun Najeriya ko na kasar Chadi ba zai sa ya mika kansa garesu ba, kamar yadda jaridar HumAngle ta wallafa.

Ya kara da musanta rahotannin da ke bayyana cewa mayakan sa duk sun kare kuma sauran duk sun nuna karaya.

A wani sautin murya mai tsayin minti takwas da dakika 22 da ya saki a ranar Alhamis, ya ce babu abinda ya faru da su kuma suna cikin koshin lafiya.

"Cewar da kuka yi kun ragargaza mu da 'yan uwanmu a Sambisa duk karya ne. Gwamnatin karya take yi wa jama'a don su so su," yace.

Shugaban 'yan ta'addan ya ce gwamnati ce ke kokarin janye hankalin mayakansa don su mika wuya a Chadi ko Najeriya.

Shekau ya ce in har za su tattauna da gwamnati don sulhu, dole ne a ba Musulmi fifiko a kan abokan gabarsu. Ya ce dole ne abokan gabar su gyara sannan su karba dukkan sharuddansa.

Boko Haram: Shekau ya musanta rade-raden zai mika wuya, ya bada sharuddan sulhu
Boko Haram: Shekau ya musanta rade-raden zai mika wuya, ya bada sharuddan sulhu. Hoto daga Google
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kwankwaso ya bukaci SSS da gwamnatin Kaduna su ceto Dadiyata

"Wadannan sharuddan kuwa ba na kafirai bane irinku. Damokaradiyya dokar jama'a ce, mu kuwa ta Allah muke bi," Shekau yace.

"Musulmai basu tattaunawa da kafirai har sai kafirai sun shirya mika wuya. Idan kuwa a yadda kuke tunani ne na cewa kun ci galaba har za mu mika wuya, ku sani cewa akwai babbar tazara tsakanin gabas da yamma," yace.

"Idris Derby, karya kake yi babu abinda ya faru da mu. Sharrinka zai kare maka," Shekau yace a yayin mayar da martani ga shugaban kasar Chadi.

Shugaban Boko Haram din ya soki salon nisantar juna da ake fadakarwa don gujewa cutar Korona. Ya ce 'yan kungiyarsa na yin sallah a jam'i kuma suna kasuwancinsu a maboyarsu.

A sautin muryar, an saki wata wakar Hausa wacce ke kira ga mayakan da suka kara hakuri tare da jajircewa.

Masu lura da lamurran 'yan ta;addan a yankin sun ce wannan duk nuni ne da irin jigatar da 'yan ta'addan suka yi a kan ruwan wutar da dakarun sojin ke musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel