Boko Haram da ISWAP sun yi sulhu, sun amince da sabon Shugaba bayan mutuwar Shekau
- Rahotanni sun ce kan ‘Yan ta’addan ISWAP da na Boko Haram ya hadu
- Sojojin kungiyoyin sun yi wa Ibrahim Al-Hashimiyil Khuraishi mubaya’a
- An tabbatar da hadin-kan bangarorin biyu a wani bidiyo da aka fitar yau
Makonni da mutuwar tsohon shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ‘yan ta’addan Islamic State of West Africa Province sun samu sabon jagora.
Jaridar PR Nigeria ta ce kungiyar ta ISWAP ta yi sulhu da bangaren Boko Haram da su ka yi wa marigayi Abubakar Shekau mubaya’a, sun zabi wani shugaban.
Bidiyon mintuna 13 ya fito
A wani faifen bidiyo mai tsawon mintuna 13 da PR Nigeria ta samu a ranar Asabar, an fahimci sojojin ‘yan ta’addan sun hakura da sabanin da ke a tsakaninsu.
KU KARANTA: Shekau: Boko Haram ta naɗa sabon shugaba
Daily Nigerian ta tabbatar da rahoton, ta ce Sojojin ‘yan ta’addan sun daura hannuwansu a kan na juna, su na yin wasu kalamai da ke nuna cewa sun hada-kansu.
Bayan nan an ji ‘yan ta’addan suna cewa su na tare da Abu Ibrahim Al-Hashimiyil AlKhuraishi, wanda su ka hadu a kan shi ne ya zama sabon ‘Khalifan Muslimai’
An ga wasu ‘yan ta’adda hudu daga cikin tsofaffin ‘yan kungiyar Boko Haram da ISWAP a bidiyon.
Wadanda su ka fito a bidiyon sun yi mubaya’a ga Abu Ibrahim Al-Hashimiyil AlKhuraishi, su na magana a cikin harshen larabci, hausa, ingilishi da kuma fulfilde.
KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun shiga Abuja, sun dauke baki suna kwance a otel
“Makiya (jami’an tsaro) sun yi nasarar raba kanmu, amma yanzu mun dawo.” Inji wani daga cikin sojojin ‘yan ta’addan da yake bayani a wannan bidiyon da ya fito.
Kan 'yan ta'adda ya hadu
Mai jawabin ya yi wa Al-Hashimiyil Khuraishi godiya na hada kan bangarorin, ya ce ya kamata kowane ‘dan Boko Haram da ISWAP ya yi murna da hadin-kan.
Wani wanda ya yi magana da Hausa, ya tabbatar wa Al-Hashimiyil Khuraishi cewa su na tare da shi, ya ce shi da abokan aikinsa za su bi umarninsa sau da kafa.
A makon da ya gabata kun ji cewa rundunar sojojin sama da kasa sun yi taron-dangi, sun hallaka Mayakan Boko Haram rututu su na shirin kai hari a jihar Borno.
Kamar yadda mu ka ji, an yi amfani da jiragen yaki an bindige wasu motocin ‘Yan ta’addan. Sojojin kasa sun ba dakarun sama gudumuwa wajen wannan hari.
Asali: Legit.ng