INEC Ta Yi Wa 'Yan Siyasa Kudin Goro, Ta Gargade Su kan Zaben 2027
- Shugaban INEC, Joash Amupitan, ya ce hukumar za ta ɗauki matakin doka kan ’yan siyasa da za su yi amfani da tashin hankali ko daba a zaɓen 2027
- INEC ta ce ta kafa tsarin sa ido kan tashin hankalin siyasa, daba da kalaman da ka iya haddasa rikici yayin kamfen
- Hukumar ta kuma yi alƙawarin tsaurara matakan yaƙi da sayen ƙuri’a, tana mai cewa ƙuri’ar ɗan ƙasa ba kayan kasuwanci ba ce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gargadi ’yan siyasa cewa burin neman mulki bai kai darajar jinin ɗan Najeriya ba.
Hukumar ta kuma yi alƙawarin kama, hukunta da gurfanar da jam’iyyu, ’yan takara da wakilan jam’iyyu da suka koma amfani da tashin hankali, kalaman ƙiyayya ko sayen ƙuri’a a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Uba Sani ta fadi abu 2 da suka fi rashin tsaro barazana ga zaman lafiya

Source: Facebook
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya bayyana hakan ne a wani taron horaswa na musamman ga editoci da Ƙungiyar Editocin Najeriya (NGE) ta shirya tare da haɗin gwiwar INEC a Abuja.
INEC ta ce siyasa ba ta kamata ta koma tashin hankali ba
Amupitan ya ce yayin da harkokin kamfen ke ƙara kankama a faɗin ƙasar, ya zama dole a gargadi jam’iyyu, ’yan takara da masu kula da kamfen.
“INEC ba za ta tsaya tana kallon siyasa tana rikidewa zuwa tashin hankali, tsoratarwa ko kalaman da ke tayar da hankali ba."
“Dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne ta hanyar musayar ra’ayoyi, ba ta hanyar arangamar makamai ko yaɗuwar kalaman ƙiyayya ba.” In ji shi.
An kafa tsarin gano tashin hankalin siyasa
Shugaban INEC ya ce hukumar ta tanadi hanyoyin gano waɗanda suka karya doka, tare da ƙara cewa an fara aiwatar da tsarin gargadi da sa ido kan abubuwan da ke faruwa.

Kara karanta wannan
Amaechi ya hango barazanar da ke fuskantar 'yan adawa idan Tinubu ya zarce a 2027
Ya ce ta hannun Kwamitin Haɗin Gwiwa na Hukumomin Tsaro kan Zaɓe (ICCES), an samar da tsarin da zai tattara bayanai kan tashin hankalin siyasa, daba da kuma kalaman kamfen masu haɗari.
Amupitan ya ce duk jam’iyya ko ɗan takarar da aka samu yana tunzura tashin hankali, tarwatsa tarukan abokan hamayya ko amfani da ’yan daba masu ɗauke da makamai zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada da kuma gurfanarwa cikin gaggawa.
“Babu wani mukamin siyasa a wannan ƙasa da ya kai darajar jinin ko da ɗan Najeriya guda.” In ji shi.
Amupitan ya kawo misalin zargin nuna bindiga
Da yake kauce wa daga jawabin da aka shirya masa, shugaban INEC ya ce an nuna masa wani misali na irin halayen da yake gargadi a kansu.
Ya ce kafin a gayyace shi ya yi jawabin, an nuna masa wani rahoto kan wani ɗan takarar NDC a Kano da ake zargin ya yi kamfen ranar Lahadi yana riƙe da bindiga yana nuna ta.
Amupitan ya kuma ce an sanar da shi wani lamari inda wani mutum ya yi barazanar cewa za a kashe jami’an INEC da bindigogin AK-47.

Kara karanta wannan
Lambar su Pantami ta fito, INEC za ta dauki mataki kan 'yan takarar da suka karya dokar zabe
“Wannan shi ne abin da zaɓe ya koma a Najeriya a yau,” in ji shi cikin nuna damuwa.

Source: Facebook
INEC za ta dauki ma'aikata
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta buɗe shafin neman aikin ma'aikatan wucin gadi da za su taimaka wajen gudanar da babban zaɓen 2027.
Hukumar zaben ta bayyana cewa aikin neman ma'aikatan zai gudana ne ta tsarin daukar ma'aikata na INEC.
Asali: Legit.ng