Najeriya Ta Yi Rashi, Daya daga cikin Wadanda Suka Kafa NADECO Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa National Democratic Coalition (NADECO), Cif Ralph Obioha, ya rasu yana da shekara 80
- Iyalansa sun bayyana shi a matsayin uba, miji, ɗan’uwa, kaka da aboki mai matuƙar ƙauna, sun ce ya rasu ne ranar 3 ga Oktoba, 2026
- Bayani sun nuna cewa marigayin ya taka rawa sosai a harkokin siyasa da kasuwanci, tare da nuna jajircewa wajen ci gaban Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Enugu, Nigeria - Ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa National Democratic Coalition (NADECO), Cif Ralph Obioha, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 80.
A cikin wata sanarwa da ɗansa, Chima Obioha, ya fitar a madadin iyalan Obioha da ke Enugu, ya ce Ralph Obioha, wanda ake kira “Okpuruisizuruoha II na Arondizuogu”, ya rasu ranar 3 ga Oktoba, 2026.

Source: Facebook
An tabbatar da rasuwar Cif Obioha
Sanarwar ta ce marigayi Obioha ya kasance uba, miji, ɗan’uwa, kaka da aboki da iyalansa ke ƙauna sosai, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Ta ce za a ci gaba da tunawa da shi saboda alherinsa, ƙarfinsa, barkwancinsa, karamcinsa, imaninsa da kuma tsayuwar daka da ya yi wajen kula da iyalansa a lokacin rayuwarsa.
“Yawancin ’yan Najeriya sun san Cif Obioha a matsayin ɗan kishin ƙasa, dattijo mai kishin ƙasa, jagoran siyasa kuma ɗan kasuwa.
“Haƙiƙa, rayuwarsa mai cike da abubuwan tarihi ta shafi fannoni daban-daban na kasuwanci da kuma harkokin siyasa da zamantakewa da tattalin arziƙin Najeriya.
“Ya kasance mai matuƙar himma wajen ci gaban Najeriya da kuma manufofin hidima, shugabanci da gina ƙasa. Ya kasance murya da ake girmamawa a ƙasar nan, kuma ya yi imani sosai da dimbin damar da Najeriya ke da ita,” in ji sanarwar.
Iyalansa sun shiga matukar jimami
Iyalansa sun ce rasuwarsa ta bar babban gibi da ba za a iya auna shi ba a cikinsu. Sai dai sun ce suna samun sakon ta’aziyya daga cikar rayuwarsa, mutanen da ya taimaka musu da kuma gadon hidima da ya bari.
“Iyalin mu na matuƙar godiya ga addu’o’i, saƙonnin ta’aziyya da nuna ƙauna da aka riga aka aiko mana.
“Duk da haka, muna roƙon a mutunta sirrinmu a wannan lokaci yayin da muke jimamin rasuwar tare da ƙoƙarin fahimtar wannan babban rashi.
“Za a sanar da cikakkun bayanan taron tunawa da shi da kuma jana’izarsa a lokacin da ya dace. Ubangiji Ya jiƙansa da rahama, Ya ba shi cikakkiyar salama,” in ji sanarwar.

Source: Original
Jigon PDP a Gombe ya rasu
Kun ji cewa Mataimakin Sakataren Kudin PDP na jihar Gombe, Abdu Tefu Bambure, wanda ya taba rike kujerar kansila mai wakiltar mazabar Dadiya Hills ya rasu.
An bayyana Bambure a matsayin jajirtaccen mai tattara jama’a, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban siyasar al’umma a yankin karamar hukumar Gombe ta Kudu kafin rasuwarsa.
Sanata Bulus Kilawangs Amos, wanda ya wakilci Gombe ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya tabbatar da rasuwar jigon PDP a wata sanarwa da ya fitar.
Asali: Legit.ng

