Tuna Baya: Abin da El Rufai Ya Fada da Aka Nada Janar Musa Ministan Tsaro

Tuna Baya: Abin da El Rufai Ya Fada da Aka Nada Janar Musa Ministan Tsaro

  • Nasir El-Rufai ya taya Christopher Gwabin Musa murna a lokacin da ya samu labarin zai zama Ministan tsaro
  • Tsohon gwamnan har ya fada wa na-kusa da shi wasu alheran tsohon hafsun tsaron da ya fito daga jihar Kaduna
  • Ba a dade ba sai aka ji Janar Musa mai ritaya yana maganganu marasa dadi game da El-Rufai da yanzu aka kama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - A karshen shekarar bara ta 2025 aka ji labari cewa Muhammad Badaru Abubakar ya sauka daga kujerar ministan Najeriya.

Bayan ya yi murabus ne sai Fadar shugaban kasa ta amince da nadin Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Minista na tsaro.

Nasir El-Rufai
Nasir El-Rufai lokacin yana mulkin Kaduna da Janar Christopher Musa (mai ritaya) a ofis Hoto: @AishaUmmi_Garba/@MODInfoNg (x)
Source: Twitter

Nasir El-Rufai ya taya CG Musa murna

Lokacin da aka ji sanarwar nadin Janar C.G Musa mai ritaya, Nasir El-Rufai yana cikin wadanda suka nuna farin cikinsu a shafin X.

Kara karanta wannan

Rigimar El Rufai da ministan tsaro: Jama'atu Nasril Islam da CAN sun tsoma baki

Tsohon gwamnan ya taya ‘dan jiharsa ta Kaduna murnar zama babban ministan tsaro, yana masa fatan ya magance matsalar tsaro.

Malam El-Rufai ya yi maganar ne bayan ya ji wata hira da BBC ta yi da tsohon hafsun tsaron da Hausa, tattaunawar ta kayatar da shi.

A gajeren jawabin da ya yi, har ya bada shawarar a fassara hirar tsohon sojan daga Hausa zuwa Turanci saboda muhimmancinsa.

Musa ya yi magana game da abubuwan da suka jawo aka gaza kawo zaman lafiya a kasar har yau.

Addu'ar da ya yi wa Musa murna

Nasir El-Rufai ya yi addu'a cewa:

"Ubangiji ya yi wa Chris Musa albarka wanda zai zo da sabon salo.
"Ubangiji ya taimake shi a yunkurinsa na gaskiya na samar da ainihin tsaro. Ya kamata a gaggauta fassara wannan hira zuwa harshen Inglishi a sake yada shi."

Sa’ilin da ya yi maganar a shafinsa, Malam El-Rufai ya tube rigar adawa duk da ya bar jam’iyyar APC a lokacin, ya shiga hadakar ADC.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An samu kungiyar da za ta ba Janar Musa hujjoji kan zarge zargen sa ya yi wa El Rufai

Makonni bayan wannan magana Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Janar Musa, shi kuma El-Rufai sai hukumar ICPC ta tsare shi.

Mutanen El-Rufai sun caccaki CG Musa

Yayin da El-Rufai yake hannun hukuma ne sai aka sake yin wata hira da Babban Ministan tsaron, a nan ne ya yi kaca-kaca da tsohon gwamnan.

Bayan jin wannan hira, na kusa da ‘dan siyasar sun fito sun yi Allah wadai da ministan tarayyar.

Daga cikinsu akwai Rukayya El-Rufai a X wanda diya ta ke wajen Malam El-Rufai, ta yi mamakin abin da ministan ya rika furtawa wannan karo.

"Ba tare da niyyar sa-in-sa da Mai Girma Ministan Tsaro ko tsoma baki cikin harkokin siyasa ba, dole ne in ce na yi matuƙar mamaki da na ga wannan bidiyon, domin @elrufai ya taɓa yin magana mai kyau sosai game da shi, har ma ya faɗa mini kyawawan abubuwa a kansa lokacin da aka naɗa shi.
"Allah Ya ci gaba da kare mu daga abubuwan da mu ka sani da waɗanda ba mu sani ba. Amin."

Kara karanta wannan

Magana ta girma: Iyalan El Rufai sun yi martani mai zafi ga Janar Christopher Musa

- Rukayya El-Rufai

A kafar X, Maryam Abubakar da ta yi aiki a matsayin hadima ta ce Christopher Musa ya soki mai gidansu ne saboda ya burge wasu a dalilin siyasa.

Ministan Buhari ya kalubalanci Ministan tsaro

An ji labari tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, ya kalubalanci Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa saboda zargin da ya yi wa Nasir El-Rufai.

Ya ce rikicin Kaduna yana dogon tarihi tun kafin mulkin El-Rufai, don haka yana da kyau a bambanta tsakanin gazawa da kuma kitsa sharri da gangan.

Dalung ya kuma jefa tambayoyi ga ministan ganin a baya har ya taba zama Hafsun tsaro na kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng