An Yi Ta Jifan Peter Obi da Magoya Bayansa yayin Ziyarar Ta'aziyya a Benue

An Yi Ta Jifan Peter Obi da Magoya Bayansa yayin Ziyarar Ta'aziyya a Benue

  • Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi ya ce wasu ’yan daba sun kai masu hari a Benue yayun ziyara a jihar
  • Obi ya zargi gwamnatin Benue da tura ’yan daba domin toshe hanyar, inda ya ce an jefe shi da tawagarsa da duwatsu yayin arangamar
  • Ziyarar Obi ta jawo cece-kuce saboda ta zo ne a lokacin da yakin neman zaben 2027 ke kara daukar zafi, lamarin da ya haifar da tambayoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Benue - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da zargi gwamnatin jihar Benue.

Magoya bayansa sun ce an hana su isa Yelwata a jihar Benue ranar Talata, 8 ga Satumbar shekarar 2026.

An kai wa Peter Obi hari a Benue
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Facebook

A wani faifan bidiyo da Nigerian Affairs Journal ta wallafa a shafinta na X, @NigAffars, an ji Obi yana cewa: “Suna jefa mana duwatsu.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya tafka kura kurai a gwamnati, ana ganin za su jawo ya sha kaye a zaben 2027

Yan daba sun kai wa Obi, masoyansa hari

Obi ya yi zargin cewa wasu ’yan daba dauke da makamai da gwamnatin Benue ta tura ne suka tare hanyar da ta nufi wuraren da wadanda kisan kiyashin Yelwata ya shafa suke.

Obi, wanda aka tabbatar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na NDC a ranar 29 ga Mayu, 2026, ya ce ’yan daban sun hana tawagarsa shiga yankin.

Tawagar tasa ta bayyana cewa an jefe su da duwatsu yayin arangamar, tana mai cewa hakan wani yunkuri ne na gangan domin hana su shiga yankin.

Ziyarar Peter Obi a Yelwata ta jawo maganganu

Yunkurin ziyarar ya zo ne yayin da yakin neman zaben babban zaben 2027 ke kara tsananta, lamarin da ya sa wasu masu lura suka fara tambayar dalilin lokacin ziyarar.

Wani mai amfani da X mai suna @Christbeloved00 ya tambayi dalilin da ya sa Obi ya jira lokacin yakin neman zabe kafin ya ziyarci wadanda harin ya shafa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya bada mamaki, ya halarci ƙaddamar kamfe na wani ɗan takarar shugaban kasa a 2027

Ya rubuta cewa:

“Amma me ya sa ya jira lokacin yakin neman zabe kafin ya ziyarci wadanda lamarin ya shafa? Idan damuwar da yake da ita ta gaskiya ce, me ya hana shi ziyartar su tun da dadewa?”

Ya kara da cewa mutanen da suka sha wahala sun cancanci tausayi, ba siyasa ba, yana mai cewa lokacin ziyarar na iya sa mutane su tambayi manufar tafiyar.

Yan daba sun kai wa Obi hari a Benue
Taswirar jihar Benue da wasu yan daba suka farmaki Peter Obi. Hoto: Legit.
Source: Original

Benue: Abin da ya faru a Yelwata

Kisan kiyashin Yelwata, wanda ya faru a Benue a bara, ya jefa al’ummomi cikin mawuyacin hali, kuma lamarin ya ci gaba da kasancewa mai matukar sarkakiya a siyasar Najeriya.

Da alama ziyarar Obi ta kasance wani yunkuri ne na jawo hankali kan halin da wadanda lamarin ya shafa ke ciki, sai dai hana shi shiga ya kara haifar da cece-kuce.

Peter Obi ya ce an hana shi ganawa da wadanda suka rasa matsugunansu a Benue yayin da yake zargin gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Yan daba sun farmaki ofishin jam'iyyar NDC, sun lalata kayan miliyoyi

Peter Obi, wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na Labour Party a zaben 2023, ya yi bayani kan abin da ya kai ga hana shi ganawa da mutanen da ke sansanonin ’yan gudun hijira a Benue.

Obi, wanda ya kasance gwamnan Anambra na wa’adi biyu, ya ce bai da tabbacin ko Gwamna Hyacinth Alia yana sane da abin da ya faru.

Dan takarar shugaban kasa na NDC a 2027 ya bayyana cewa ya shirya ziyartar gwamnan, Sarkin gargajiya na Tiv, sansanonin ’yan gudun hijira da kuma makarantar koyar da aikin jinya da ke jihar.

Obi ya ce Makinde yana da kwarewa

An ji cewa dan takarar shugaban kass na NDC, Peter Obi ya bayyana cewa dan takarar APM, Seyi Makinde, ya cancanci zama shugaban Najeriya.

Tsohon gwamnan Anambra ya ce siyasa bai kamata ta zama ta gaba da juna ko neman mulki ta kowane hali ba.

Obi ya ce zai goyi bayan duk wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2027 cikin adalci da gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.