Magana Ta Kare, INEC Ta Dora Sabon Tambarin Jam'iyyar Su Kwankwaso a Shafinta

Magana Ta Kare, INEC Ta Dora Sabon Tambarin Jam'iyyar Su Kwankwaso a Shafinta

  • Jagoran jam’iyyar NDC na ƙasa, Sanata Henry Seriake Dickson, ya tabbatar da cewa INEC ta dora sabon tambarin jam'iyya a shafinta
  • Sanata Dickson ya ce ɗora tambarin wani mataki ne na biyayya gaumarnin Babbar Kotun Tarayya da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyar NDC
  • Ya kuma yaba wa hukumar INEC da hukumar shari’a ta Najeriya bisa bin hukuncin kotu kan tambarin jam’iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jagoran NDC na ƙasa, Sanata Henry Seriake Dickson, ya taya shugabannin jam’iyyar da mambobinta murnar dora sabon tambarin jam’iyyar a zhafin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC).

Dickson ya ce wannan ci gaba ya yi daidai da umarnin Babbar Kotun, bayan amincewa da canza tambarin bisa kundin tsarin mulkin jam’iyyar NDC da kuma tabbatar da shi daga Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC).

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu bai ji daɗin abin da ya faru da mutane 32 a jirgin saman sojojin Najeriya ba

Dickson.
Jagorana NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

Sanatan na jihar Bayelsa ya bayyana haka ne a a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Talata, 6 ga watan Oktoba, 2026.

NDC ya yaba wa INEC da bangaren shari'a

Tsohon gwamnan Jihar Bayelsa ya yaba wa bangaren shari’a na Najeriya, da Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, da mambobin hukumar bisa bin hukuncin kotu.

Ya kuma yaba wa Shugaban NDC na ƙasa, Sanata Moses Cleopas, da mambobin NEC bisa ƙoƙarinsu, tare da gode wa ’yan takarar jam’iyyar da mambobinta saboda fahimtar da suka nuna yayin takaddamar da sabon tambarin.

A cewar Dickson, dora tambarin da aka amince da shi a shafin INEC zai bai wa ’yan takarar NDC tabbaci yayin da suke ƙara shirye-shiryen yaƙin neman zaɓe.

“Yanzu an dora tambarin da aka amince da shi, kuma ’yan takara za su iya buga kayan yaƙin neman zaɓe tare da ci gaba da tuntuɓar jama’a cikin kwanciyar hankali,” in ji shi.

Kara karanta wannan

2027: An samu gwamnan APC na farko da ya nuna bai adawa da tafiyar Wike

Dickson ya jaddada kudirin NDC

Dickson ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da jajircewa wajen cimma manufofinta na siyasa, yana mai cewa ƙoƙarin amfani da bangaren shari’a wajen raunana NDC ya gaza.

“Mu mayaƙa ne, kuma za mu yi yaƙi har ƙarshe. Mun ja daga da waɗanda suka nemi amfani da bangaren shari’a wajen yaƙar jam’iyyar, kuma sun gaza,” in ji shi.

Shugaban NDC ya buƙaci ’yan takarar jam’iyyar a faɗin ƙasar su yi aiki kafada da kafada da jam’iyyar a dukkan matakai yayin kafa ƙungiyoyin yaƙin neman zaɓensu.

Jam'iyyar NDC.
Jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson da tambarin jam'iyyarsu Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

Ya jaddada cewa ’yan takarar suna takara ne ƙarƙashin inuwar jam’iyyar, ba a matsayin ’yan takara masu zaman kansu ba.

Dickson ya gargaɗi ’yan takarar kan abin da ya kira yi wa kansu zagon ƙasa, yana mai buƙatarsu da su tabbatar da haɗin kai tare da daidaita ayyukan yaƙin neman zaɓensu da shugabannin jam’iyyar.

Babachir Lawal ya koma NDC

Kun ji cewa tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya koma jam’iyyar NDC watanni uku bayan ya yi murabus daga ADC.

Lawal ya sanar da komawarsa jam’iyyar NDC a Abuja, inda ya bayyana goyon bayansa ga tikitin shugaban ƙasa na Peter Obi da mataimakinsa Rabiu Kwankwaso gabanin zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262