Ministan Tinubu Bai Ji Dadin Abin da Ya Faru da Mutane 32 a Jirgin Saman Sojojin Najeriya ba
- Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana matuƙar jimami kan hatsarin jirgin NAF ATR 42 da ya yi sanadin mutuwar mutane 32
- Ya ce jami’an da suka rasu suna gudanar da aiki ne na yau da kullum daga birnin Benin zuwa Legas domin yi wa ƙasa hidima
- Musa ya miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shugabannin rundunonin sojin Najeriya da iyalan waɗanda suka rasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana matuƙar jimami kan hatsarin jirgin NAF ATR 42 da ya yi sanadin mutuwar jami’ai da sojojin sama.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Janar Musa ya miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shugabannin Rundunar Sojin Najeriya, iyalan waɗanda suka rasu, ’yan uwansu da abokan aikinsu.

Source: Twitter
Ya ce hatsarin jirgin mai lambar aiki ta NAF 931 ya jefa Ma’aikatar Tsaro da baki ɗaya Rundunar Sojin Najeriya cikin babban alhini, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ministan tsaro ya yi jimamin lamarin
“Cike da tsananin baƙin ciki da zuciya mai nauyi, ni a madadin Ma’aikatar Tsaro da baki ɗaya Rundunar Sojin Najeriya, ina bayyana matuƙar jimami kan hatsarin jirgin sojinmu mai lamba NAF 931, wanda ya shafi jajirtattun jami’an sojoji.
“Wannan lamari mai raɗaɗi ya yi sanadin mutuwar jajirtattun jami’ai da sojojin sama da ke gudanar da aikin yau da kullum, yayin da suke yi wa ƙasarmu hidima cikin ƙarfin hali, sadaukarwa da kishin ƙasa marar iyaka.
“Rashin waɗannan ’yan kishin ƙasa jarumai babban rashi ne da ba za a iya maye gurbinsa ba, ba ga manyan hafsoshin soji da abokan aikinsu kaɗai ba, har ma ga Najeriya baki ɗaya.
- Janar Musa.
Musa ya miƙa ta’aziyya ga iyalai
Janar Musa ya ce a madadin Ma’aikatar Tsaro, yana miƙa ta’aziyyarsa ga Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunonin Sojin Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Haka zalika ministan ya kuma mika ta'ziyya shugabannin rundunonin soji da kuma iyalai, ’yan uwa da abokan aikin waɗanda suka rasu.
“Muna tare da ku wajen wannan babban lokacin baƙin ciki kuma muna tare da ku kafada da kafada a wannan lokaci mai cike da tashin hankali.
“Har ila yau, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalan fararen hular da ke cikin jirgin da ya yi hatsarin. Muna tare da ku wajen jimamin wannan rashi," in ji shi.

Source: Facebook
Ministan ya ce an bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan abubuwan da suka haifar da hatsarin domin gano musabbabinsa, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Gwamna ya fadi dalilan faduwar jirgin soji
A baya, an ji cewa gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ce matsalar fasaha ko na’ura na iya zama sanadin faduwar jirgin sojin saman Najeriya a Igbokoda.
Gwamna Aiyedatiwa ya ce mai yiwuwa jirgin ya samu matsala yayin da yake cikin iska, lamarin da ya haddasa yanke sadarwa tsakaninsa da hasumiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama.
Asali: Legit.ng

