Gwamna Ya Tausaya wa Malamai Mata, Zai Saya Masu Hannun Jarin Matatar Dangote

Gwamna Ya Tausaya wa Malamai Mata, Zai Saya Masu Hannun Jarin Matatar Dangote

  • Gwamnatin Kwara ta shirya sayen hannun jarin matatar Dangote ga mata malamai, domin karfafa musu guiwa
  • Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce za a bai wa mata malamai hannun jari 10,000, tare da shirin fadada tsarin
  • Gwamnatin ta kuma ware N120m ga fitattun malamai, shugabannin makarantu da jami’an ilimi domin yaba kokarinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Gwamnatin Jihar Kwara ta sanar da shirin sayen hannun jarin matatar Dangote ga mata malamai a jihar domin karfafa zuba jari.

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Ilorin yayin wani taro na bikin Ranar Malamai ta Duniya ta 2026.

Gwamnan Kwara taimakawa malamai mata
Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na jihar Kwara. Hoto: Kwara State Government.
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito gwamnan na cewa shirin wani sabon tsari ne da aka kirkiro domin karfafa zuba jari da kuma bunkasa damar samun kudi ga malamai.

Kara karanta wannan

Shettima ya dura jihar Katsina, an raba miliyoyin Naira kyauta

Gwamna ya ware N120m ga fitattun malamai

Gwamnan ya kuma bayar da kyaututtukan kudi kusan N120m ga fitattun malamai, shugabannin makarantu da cibiyoyin ilimi a jihar.

AbdulRazaq ya ce jihar za ta sayi hannun jari 10,000 ga mata malamai 10 a kowace makarantar gwamnati da ta yi fice.

Ya kara da cewa shirin zai kuma shafi fitattun mata malamai da suka yi ritaya daga aikin koyarwa a jihar.

Gwamnan ya ce an kirkiro shirin ne tare da hadin gwiwar Gidauniyar Dangote domin karfafa mata su daina dogaro da samun kudin shiga kawai.

Ya ce ana son mata malamai su fara mallakar kadarori ta hanyar zuba jari da mallakar hannun jari a kamfanoni.

AbdulRazaq ya ce Gidauniyar Dangote za ta bayar da karin hannun jari daidai da adadin da gwamnati ta saya.

Ya bayyana cewa idan gwamnati ta sayi hannun jari 10, za a ba da karin hannun jari 10 a matsayin tallafi, wanda zai zama 20 gaba daya.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai za ta binciki NNPCL da INEC kan zargin karkatar da N802bn

Malamai sun ga gata a Kwara kan jajircewa
Taswirar jihar Kwara da aka ba hazikan malamai kyautar miliyoyi. Hoto: Legit.
Source: Original

Shirin ba malamai mata kyautar hannun jarin Dangote

Gwamnan ya ce malamai mata masu aiki karkashin TESCOM da SUBEB za su samu hannun jari goma-goma a karkashin shirin.

Ya kuma ce za a fadada tsarin zuwa ga mata malamai da suka yi ritaya domin su ma su amfana da shirin.

Gwamna AbdulRazaq ya umarci Shugabar Ma’aikatan Jihar, Dr Olufunke Mercy Shittu, da ta tsara yadda za a tantance malaman mata da suka yi ritaya.

Ya ce shirin zuba jari wani bangare ne na kokarin inganta walwala da damar samun ci gaban tattalin arziki ga malamai.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa malamai muhimmanci saboda muhimmiyar rawar da suke takawa wajen ilimin yara.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da inganta walwala da yanayin aikin malamai cikin tsari mai dorewa domin kara musu kwarin gwiwa, cewar Punch.

Gwamnan ya kuma bayar da kyaututtukan kudi da suka kai kusan N120m ga fitattun masu ruwa da tsaki a fannin ilimi.

Kara karanta wannan

An zo wajen: An fara shirin daina kai shanu daga Arewa zuwa Kudu

Malamai 29 da shugabannin makarantu sun samu N29m, yayin da malamai 119 suka karbi kyautar kudi N59.5m saboda bajintarsu.

Gwamnan Kwara ya ba malamai motoci

A baya, an ji cewa Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bai wa Babban Limamin Ilorin da Majalisar Malaman Ilorin motoci hudu.

Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya yabawa gwamnan bisa cika alƙawari da kuma ci gaba da tallafa wa harkokin addini.

Babban Limamin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Dasuki Imam Fulani, ya ce tallafin zai sauƙaƙa zirga-zirgar malaman addini da ayyukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.