Mutumin Katsina Ya Burma Matsala kan Zargin Lalata Allunan Tallar Tinubu
- An tsare Aminu Sanda, wanda aka fi sani da Nesta, sannan aka gurfanar da shi bisa zargin aikata laifin cin amanar ƙasa
- Sanda ya musanta zargin lalata allunan tallan Shugaba Bola Tinubu da kuma kutsawa ofishin APC a Katsina domin satar Naira miliyan 35
- Wasu lauyoyi sun nuna mamaki kan tuhumar cin amanar ƙasa, suna cewa lalata allon tallan siyasa bai cika ma’anar irin wannan babban laifi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - An tsare wani mazaunin Jihar Katsina, Aminu Sanda, wanda aka fi sani da Nesta, sannan aka tuhume shi da laifin cin amanar ƙasa bisa zargin lalata allunan tallan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan
Kano da wasu jihohi 19 sun fito a wuraren da Bola Tinubu zai samu nasara a zaben 2027
Da farko, ’yan sanda sun gayyaci Sanda a Katsina, daga bisani aka tsare shi bisa zargin cewa ya cire wasu allunan tallan shugaban ƙasa.

Source: Original
Haka kuma, ana zargin Sanda da kutsawa sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta Jihar Katsina, inda ake zargin ya kwashe Naira miliyan 35, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Sanda ya musanta zarge-zargen
Sanda ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa, ciki har da cewa ya lalata allunan tallan Tinubu ko kuma ya shiga sakatariyar APC domin satar kuɗin.
Ya bayyana zarge-zargen da ake yi masa a matsayin marasa tushe, yana mai cewa bai aikata abubuwan da ake danganta masa ba.
Daga baya an tura Sanda zuwa hedikwatar rundunar ’yan sanda da ke Abuja, inda wata Kotun Majistare da ke Jiwa, a babban birnin, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare shi bisa tuhume-tuhumen da suka haɗa da cin amanar ƙasa.
’Yan sanda sun nemi ƙarin makonni biyu
’Yan sanda sun je kotun ne ta hanyar wata buƙata ta musamman, inda suka nemi izinin ci gaba da tsare Sanda na tsawon makonni biyu domin su kammala bincikensu kan zarge-zargen.
Sai dai a ranar Talata, lauyoyin Sanda sun bayyana a gaban kotun domin neman a bayar da belinsa.
A wannan lokaci kuma, ’yan sanda sun shigar da wata sabuwar buƙata suna neman ƙarin makonni biyu domin kammala binciken.
Alƙalin Majistare, Huzaifa Macchudo, ya ajiye hukunci kan buƙatar belin da lauyoyin Sanda suka shigar.
A cewar lauyoyin Sanda, ajiye hukuncin na iya bai wa ’yan sanda damar neman ƙarin lokacin tsare shi, yayin da yake ci gaba da kasancewa a hannunsu.
Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta tabbatar cewa an gurfanar da Sanda a gaban kotu ranar Talata.
Majiyar ta ce an ɗage shari’ar zuwa ranar 15 ga Satumban 2026 domin yanke hukunci kan buƙatar belin da lauyan Aminu Sanda ya shigar.
Lauyoyi sun soki tuhumar cin amanar ƙasa
Wasu ƙwararrun lauyoyi sun nuna damuwa kan tuhumar cin amanar ƙasa da aka yi wa Sanda.
Lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Hameed Ajibola Jimoh, ya bayyana mamakinsa kan yadda cire allon talla zai iya zama laifin cin amanar ƙasa.
“Abin mamaki ne cewa cire allon talla zai zama cin amanar ƙasa. Laifi yana da ma’anarsa. Cin amanar ƙasa ma yana da ma’anarsa. Cire allon talla al’amari ne na siyasa.” In ji shi
Lauya ya bayyana tuhumar a matsayin abin mamaki
Shi ma wani lauya mai aiki a Abuja, Barrister Abdurrahman Salis, ya bayyana tuhumar cin amanar ƙasa da aka yi wa Sanda a matsayin “abin mamaki”.

Kara karanta wannan
Fin karfi: Ana zargin Kwamishina ya raba aure, ya lallaba ya auri matar a Zamfara
Abdulrahman Salis ya ce ko lauya ko ɗalibin shari’a zai yi mamakin ganin irin wannan tuhuma a kan mutumin da ake zargi da cire allon tallan Shugaban Ƙasa a Katsina.
Ya bayyana cewa cin amanar ƙasa da kuma laifin da ake kira treasonable felony laifuka ne daban-daban a ƙarƙashin dokokin Najeriya, kuma suna da yanayi masu tsanani fiye da zargin lalata allon talla.

Source: Facebook
Wike ya yi hasashe kan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, y.a yi hasashen kuri'un da Shugaba Bola Tinubu zai samu a Arewa.
Wike ya yi hasashen cewa Shugaba Tinubu zai samu kaso 25 cikin 100 na kuri'u a jihohin Arewacin Najeriya.
Asali: Legit.ng

