Zaben 2027: Wike Ya Yi Hasashen Kuri'un da Atiku, Tinubu Za Su Samu a Arewa da Kudu
- Nyesom Wike ya ce babu jihar Arewa da Bola Tinubu ba zai samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u ba a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Wike ya yi hasashen cewa Atiku Abubakar ba zai kai kashi 10 cikin 100 na ƙuri’u a wasu jihohin Kudancin Najeriya ba
- Ya ce Tinubu zai lashe Plateau, Nasarawa, Kwara da Kogi, yana mai cewa hasashensa ya dogara ne kan yanayin siyasar da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT Abuja, Najeriya - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu akalla kashi 25 cikin 100 na ƙuri’u a kowace jiha ta Arewa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Wike ya kuma ce tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ba zai samu kashi 10 cikin 100 na ƙuri’u a wasu jihohin Kudancin Najeriya ba.

Source: Facebook
Wike ya yi magana kan Tinubu a Arewa
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Fatakwal, babban birnin Jihar Rivers, ranar Laraba, 2 ga watan Satumban 2026, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Wike ya yi watsi da ra’ayoyin da ke cewa tasirin siyasar Tinubu a Arewa na fuskantar barazana, yana mai cewa irin wannan hasashe ba shi da tushe.
Da aka tambaye shi kan damar Tinubu a Arewa a zaɓen 2027, Wike ya ce masu nazarin siyasa ya kamata su kuma duba irin damar da Atiku yake da ita a Kudancin ƙasar.
“Babu yadda za a yi a Arewa Shugaban ƙasa bai samu kashi 25 cikin 100 ba. Akwai wurare da dama a Kudu da ba za su samu kashi 10 cikin 100 ba.” In ji shi.
Wike ya lissafa jihohin da Tinubu zai ci
Wike ya ci gaba da bayyana wasu jihohin Arewa ta Tsakiya da yake ganin Tinubu zai samu nasara a cikinsu.

Kara karanta wannan
Kano da wasu jihohi 19 sun fito a wuraren da Bola Tinubu zai samu nasara a zaben 2027
Ya ce hasashensa bai dogara kan zato kawai ba, illa yanayin siyasar da yake gani a ƙasa, jaridar The Punch ta kawo labarin.
“Mu ɗauki Arewa ta Tsakiya. Wa zai ci Plateau? Shugaban ƙasa zai ci Plateau. Zai ci Nasarawa. Zai ci Kwara. Zai ci Kogi.” In ji shi.
Wike ya nuna cewa yana da kwarin gwiwar Tinubu zai samu gagarumar nasara a wasu jihohin Arewa ta Tsakiya yayin zaɓen 2027.
Wike ya yi magana kan yunwa da zaɓe
Ministan ya kuma yi watsi da hujjar cewa matsin tattalin arziƙi da wahalhalun rayuwa za su iya rage damar Tinubu ta sake lashe zaɓe.
A cewarsa, yunwa da matsin rayuwa ba su taɓa zama abin da ke kayyade sakamakon zaɓen Najeriya kai tsaye ba.
“Shin akwai wani zaɓe da aka taɓa yi a Najeriya ba tare da yunwa ba? Ku kawo zaɓe guda. Ko a lokacin zaɓen Buhari, mutane suna magana kan rashin tsaro da yunwa. Duk da haka, kowa ya jefa ƙuri’a.” In ji shi.
Ministan ya yi amfani da wannan misali wajen bayyana cewa matsalolin tattalin arziƙi da rashin tsaro kaɗai ba su isa su tabbatar da cewa ɗan takara zai rasa zaɓe ba.

Source: Facebook
Gwamnonin APC da ke takun saka da Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan Abuja Nyesom Wike, ya bayyana gwamnonin jam'iyyar APC biyu da yake zargin sun sa kafar wando daya sa shi.
Wike ya yi ikirarin gwamnonin jihohin Imo da Kwara, Hope Uzodinma da AbdulRahman AbdulRazaq, na daga cikin gwamnonin da ke adawa da shi a siyasance.
Asali: Legit.ng

