Kano da Wasu Jihohi 19 Sun Fito a Wuraren da Bola Tinubu Zai Samu Nasara a Zaben 2027

Kano da Wasu Jihohi 19 Sun Fito a Wuraren da Bola Tinubu Zai Samu Nasara a Zaben 2027

  • Wani sabon hasashen ya nuna yadda Shugaba Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi za su iya samun kuri’u idan aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa yau
  • Ƙungiyar PIG ta bayyana Tinubu a matsayin ɗan takarar da ke kan gaba, yayin da hasashen samun nasara a Kano ya jawo hankalin masu sharhi kan siyasa
  • Ana hasashen Tinubu zai sake kwato Lagos a 2027, jihar da Peter Obi ya kayar da shi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wani sabon hasashen ya nuna cewa Shugaba Bola Tinubu zai lashe jihohi 20 a 2027, yayin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai ci jihohi tara, sannan ɗan takarar NDC, Peter Obi, zai lashe jihohi takwas.

Legit.ng ta ruwaito cewa hasashen ya fito ne daga kungiyar Political Intelligence Group (PIG), wadda ta tantance yanayin siyasa domin gano yadda manyan ’yan takara uku za su iya samun nasara idan aka gudanar da zaɓen bisa yanayin da ake ciki a yau.

Kara karanta wannan

Atiku ya ragargaji Tinubu kan tafiya hutu Turai 'Najeriya na ci da wuta'

Peter Obi, Tinubu da Atiku.
Manyan yan takarar shugaban kasa 3, Peter Obi, Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar Hoto: Peter Obi, Bayo Onanuga, Atiku Abubakar
Source: UGC

Tinubu zai mamaye Kudu maso Yamma

A cewar hasashen da Legit.ng ta gani ranar Talata, 1 ga Satumba, 2026, babbar nasarar Tinubu na zuwa ne daga Kudu maso Yamma, inda ake sa ran zai samu nasara a dukkan jihohi shida.

Tasirinsa da ya daɗe yana da shi a yankin ya sanya yankin ya zama tushen ƙuri’unsa mafi aminci. Ƙungiyar ta yi gargadin cewa yanayin siyasa na iya sauyawa sosai kafin ranar zaɓe.

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a hasashen shi ne nasarar da ake sa ran Tinubu zai samu a Kano, ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi yawan jama’a kuma muhimmiyar jiha a zaɓen shugaban ƙasa.

Nasara a Kano za ta bai wa shugaban ƙasar gagarumar dama a Arewacin Najeriya tare da ƙara masa damar haɗa babbar ƙawancen siyasa na ƙasa baki ɗaya, fiye da tushen ƙuri’unsa na Kudu maso Yamma.

Hasashen ya kuma nuna cewa Tinubu zai sake kwato jihar Lagos, wadda Peter Obi ya kayar da shi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Kara karanta wannan

Za a tura tawaga ga dattawan Igbo domin rokon Obi ya janye wa Tinubu a 2027

PIG ta ce hasashen 2027 zai iya sauyawa

Kungiyat PIG ta ce an yi hasashen ne bisa yanayin siyasar da ake ciki a yanzu, kuma ba hukunci na ƙarshe ba ne kan fafatawar zaɓen 2027. Abubuwa da dama na iya yin tasiri kan yadda masu zaɓe za su kaɗa ƙuri’a kafin a gudanar da ainihin zaɓen.

Hauhawar farashi, matakin samun ayyukan yi, tsaro, ababen more rayuwa da kuma tsadar rayuwa baki ɗaya na iya shafar yadda ’yan Najeriya za su tantance gwamnatin Tinubu zuwa 2027.

Jihohi 20 da Tinubu zai lashe a 2027

Jihohin da PIG ta yi hasashen Tinubu zai lashe su ne:

  1. Zamfara
  2. Kano
  3. Yobe
  4. Bauchi
  5. Plateau
  6. Kwara
  7. Oyo
  8. Ogun
  9. Lagos
  10. Osun
  11. Ekiti
  12. Ondo
  13. Kogi
  14. Benue
  15. Imo
  16. Cross River
  17. Bayelsa
  18. Rivers
  19. Akwa Ibom
  20. Anambra.
Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana magana a wani taro a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Yan adawa na shirin kayar da Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa shugabannin manyan jam’iyyun adawa shida sun gudanar da wani taro a Abuja domin ƙarfafa shirin haɗin gwiwa da nufin kayar da Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Daya daga cikin jagororin 'yan adawa, Salihu Lukman ya yi karin bayani game da abubuwan da suka sa a gaba da yadda suke son cimma su a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262